Nau'o'in wayoyi 5 da NCC ta ce za su daina aiki a Najeriya

Wayoyin da za su daina aiki a Najeriya
    • Marubuci, Bashir Zubairu Ahmad
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Multimedia Journalist
    • Aiko rahoto daga, Abuja
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 4

A kwanan nan ne Hukumar Sadarwa ta Najeriyar dai (NCC) ta sanar da fara aiwatar da wani sabon tsarin tantance wayoyin hannu da sauran na'urorin sadarwa da ake amfani da su a Najeriya, inda ta ce za a kulle wasu wayoyin da ba su da rijistar yin aiki a ƙasar.

NCC ta bayyana wa BBC cewa sabon tsarin na cikin shirin inganta ka'idojin tantance na'urorin sadarwa, wanda ya fara aiki daga ranar 7 ga Oktoba, 2026, domin daƙile yawaitar jabun wayoyi da kuma kare lafiyar hanyoyin sadarwa a ƙasar.

Hukumar ta ce manufar ita ce tabbatar da cewa dukkan na'urorin da ake sayarwa ko amfani da su a Najeriya sun cika ka'idojin da kare masu amfani da sabis.

Malam Usman Mamman shi ne daraktan sashen bayar da lasisi na hukumar Sadarwa ta Najeriya, (NCC), ya shaidawa BBC cewa, "ba wani sabon abu ba ne dama akwai dokar da NCC take da".

Abin da NCC ta ce

Hukumar ta shawarci jama'a musamman masu sayen wayoyin hannu da aka taɓa amfani da su wato sakan han, da su tabbatar sun tantance wayar kafin biyan kuɗi, domin gujewa sayen wayoyin da ba su da sahalewar amfani a Najeriya.

"Dam duk harkar waya na ƙarƙashin hukumarmu, mu ke bada lasisi kuma duk wayoyin da ke shiga ƙasar nan sai mun tantance, ba sabuwar doka ba ce," in ji Malam Usman

Daraktan da ke lura da samar da lasisin ya ƙara da cewa ana tura wa jama'a wasu lambobi da za su shigar don tantance wayoyinsu idan sun cika ƙa'idojin yin amfani a Najeriya.

Ya ce ta hakan ne mutum zai gane idan NCC ta tantance wayar, saɓanin haka kuma dole sai mutum ya nemi yadda za a tantance ta", in ji shi.

Hukumar ta ce duk wayoyin da suka riga suka kasance a kan cibiyoyin sadarwar Najeriya kafin fara aiwatar da tsarin a ranar 7 ga Oktoba, 2026, an riga an tantance su kai tsaye, don haka mafi yawan masu amfani ba za su ɗauki wani ƙarin mataki ba.

Waɗanne nau'ukan wayoyi da na'urori ne NCC za ta dakatar?

Tsallake Whatsapp
BBC News Hausa WhatsApp latsa nan domin shiga tasharmu
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

NCC ta ce sabon tsarin tantance na'urorin sadarwa na da nufin hana na'urorin da ba su cika ƙa'idojin da aka gindaya ba shiga cibiyoyin sadarwar wayar salula a ƙasar.

Daraktan bayar da lasisi na hukumar, Usman Mamman, ya ce wasu na'urorin da ake shigowa da su Najeriya na da lahani, ciki har da waɗanda ba sa iya kiran waya ko karɓar kira yadda ya kamata.

Ya kuma yi gargaɗin cewa wasu na'urorin na iya jefa lafiyar jama'a da tsaron ƙasa cikin haɗari.

Ga nau'ukan wayoyi da na'urorin da sabon tsarin NCC ya shafa:

1. Wayoyin zamani (Smartphones): Wayoyin zamani da ba su cika ƙa'idojin amfanin hukumar ba na iya rasa damar shiga wasu manhajojin sadarwar wayar salula a Najeriya.

2. Ƙananan wayoyin hannu: Ƙananan wayoyin da ake amfani da su wajen kira da saƙonnin waya kawai, su ma suna cikin na'urorin da tsarin ya shafa idan ba su cika ƙa'idojin da aka gindaya ba.

3. Kwamfutocin hannu masu amfani da layin waya: Kwamfutocin hannu da laptop, ciki har da iPad da sauran na'urori masu amfani da layin kira na SIM na iya fuskantar barazanar kullewa idan ba su cika ƙa'idojin ba.

4. Na'urorin sadarwar Intanet na (IoT): Waɗannan na'urori ne da ke amfani da intanet wajen sadarwa ko gudanar da wasu ayyuka a intanet kamar router

5. Na'urorin POS masu amfani da katin SIM: Na'urorin POS da ake amfani da su wajen karɓar kuɗin ciniki ta hanyar katin banki ko wasu hanyoyin biyan kuɗi na cikin na'urorin da tsarin ya shafa idan har ba a yi musu rijista ba.

Sai dai NCC ta kuma wallafa a shafinta na intanet a ranar 2 ga watan Oktoban 2026 cewa akwai jerin wayoyi sama da 2,000 da aka amince da amfani da su a Najeriya.

Wane mataki mutum zai ɗauka idan wayarsa ba ta da rijista?

NCC ta jaddada cewa wannan sabon tsari ba yana nufin masu amfani da wayoyi a halin yanzu su canza wayoyinsu ba.

Hukumar ta ce akwai hanyoyin da aka tsara ga duk wanda ke son tantance wayarsa ya kamata ya yi amfani da su, a cewar Usman Mamman.

Ga hanyoyin da ya ce mutum zai bi domin gane ko wayarsa na da rijistar:

  • Na ɗaya a kira waɗannan lambobin na *315# kyauta ba sai an biya ba
  • Idan an tantance wayar ko akasin hakan za nuna wa mutum hanyoyin da zai bi
  • Za kuma a iya ziyartar shafin intanet na hukumar a ncc.gov.ng
  • Akwai bayanai kan yadda mutum zai bi ya gane wayarsa na da rijista
  • Ana kuma iya kiran 622 a faɗa wa mutum yadda zai tantance waya ko na'urarsa, kamar yadda daraktan hukumar NCC ya bayyana

Yaushe matakin zai fara aiki?

Hukumar ta NCC ta ce tsawon lokacin da aka ba masu amfani da wayoyin hannu a Najeriya domin su tantance wayoyinsu, ya kai kwana talatin, inda daga bayan wannan lokaci duk wata waya maras inganci ko mai ɗauke da wani lahani ba za ta yi aiki ba a Najeriya.

Haka kuma hukumar ta ce alhakin samun amincewar na'urori ba ya kan masu saye kai tsaye, domin masana'antu, masu shigo da kaya da masu sayarwa ne ke da alhakin tabbatar da cewa na'urorin sun cika dukkan ka'idojin da aka shimfiɗa kafin su kai ga kasuwa.

Akan haka duk waɗanda suka samu wayar da suka saya ba ta da inganci ko kuma ya shigar da lambobin da aka bayyana amma ya ga ba tantance wayar ba, to suna da damar mayar da ita ga wanda ya sayar musu a biya su kuɗinsu.