Arsenal da Madrid, Man Utd da Munich PSG da Villa duk a Champions Lig

,

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 3

Zakaran Turai Paris Saint-Germain (PSG) za ta kara da manyan kungiyoyi irin su Manchester City, Aston Villa da Barcelona a matakin league phase na Champions League na wannan kakar.

PSG za ta karbi bakuncin Barcelona a Parc des Princes, sannan kuma ta yi tafiye-tafiye zuwa Villa Park da Manchester domin fuskantar Aston Villa da Manchester City.

Arsenal za ta fuskanci Real Madrid da Bayern Munich, Zakarun Premier League Arsenal za su karbi bakuncin Real Madrid a Emirates Stadium, sannan su yi tafiya zuwa Jamus domin karawa da Bayern Munich.

Kungiyar Mikel Arteta za ta kuma kara da Borussia Dortmund, Real Betis, Lille, Napoli, Sabah da Slavia Prague.

Manchester City za ta sake haduwa da Rodri da De Bruyne, za ta karbi bakuncin PSG a Etihad Stadium sannan ta yi tafiya zuwa Barcelona, inda za ta kara da tsohon dan wasanta Rodri, wanda ya koma Barcelona a wannan bazarar.

City kuma za ta fuskanci Napoli, inda za ta sake haduwa da tsohon tauraronta Kevin De Bruyne.

Sauran abokan karawarta sun hada da Sporting CP, Porto, RB Leipzig, AEK Athens da Lens.

Aston Villa ta dawo Champions League za ta karbi bakuncin PSG da Borussia Dortmund, sannan ta yi wasannin waje da Barcelona da Galatasaray.

Sauran kungiyoyin da za ta kara da su su ne Club Brugge, Fenerbahce, Viking da Slavia Prague.

Manchester United ta dawo gasar bayan shekaru biyu za ta kara da Bayern Munich,

Atletico Madrid, Roma, Sporting CP, RB Leipzig, Villarreal, Sabah, Como.

Liverpool za ta kara da Atletico Madrid da Inter Milan za ta karbi bakuncin, Atletico Madrid, Porto, Villarreal, Lens

Sannan za ta yi wasannin waje da Inter Milan, Club Brugge, Fenerbahce,LASK.

Za a fara wasannin rukunin matakin farko ne a ranar 8 ga Satumba, yayin da zagayen karshe zai gudana ranar 27 ga Janairu, 2027.

Za a fitar da cikakken jadawalin wasannin ranar Asabar.

Wasan karshe

Za a buga wasan karshe na Champions League na kakar bana a Estadio Metropolitano da ke Madrid ranar 5 ga Yuni, 2027.

Waɗanne ƙungiyoyi ne za su fuskanci na Premier

Arsenal: Real Madrid (a gida) Bayern Munich (a waje) Borussia Dortmund (a gida) Real Betis (a waje) Lille (a gida) Napoli (a waje) Sabah (a gida) Slavia Prague (a waje).

Aston Villa: PSG (a gida) Barcelona (a waje) Borussia Dortmund (a gida) Club Brugge (a waje) Fenerbahce (a gida) Galatasaray (a waje) Viking (a gida) Slavia Prague (a waje).

Liverpool: Atletico Madrid (a gida) Inter Milan (a waje) Porto (a gida) Club Brugge (a waje) Villarreal (a gida) Fenerbahce (a waje) Lens (a gida) LASK (a waje)

Manchester City: PSG (a gida) Barcelona (a waje) Sporting CP (a gida) Porto (a waje) Napoli (a gida) RB Leipzig (a waje) AEK Athens (a gida) Lens (a waje)

Manchester United: Bayern Munich (a gida) Atletico Madrid (a waje) Roma (a gida) Sporting CP (a waje) RB Leipzig (a gida) Villarreal (a waje) Sabah (a gida) Como (a waje).

Ya ya tsarin matakin farko na Champions zai kasance?

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

A sabon tsarin Champions League, kowace ƙungiya daga cikin ƙungiyoyi 36 za ta buga wasanni takwas da ƙungiyoyi takwas daban-daban a matakin league phase, inda za ta buga wasanni huɗu a gida da huɗu a waje.

Ƙungiyoyin da suka kammala a cikin manyan takwas na teburin gasar za su tsallaka kai tsaye zuwa zagayen 'yan 16. Waɗanda suka zo daga matsayi na tara zuwa na 24 kuwa za su buga wasannin neman gurbi gida da waje domin samun damar shiga zagayen 'yan 16.

Ƙungiyoyin da suka kammala daga matsayi na 25 zuwa ƙasa za su fita daga gasar gaba ɗaya, kuma ba za su sauka zuwa gasar Europa League ba.

A kakar wasan da ta gabata, Arsenal wadda ta kai wasan ƙarshe ita ce ta zo ta ɗaya a teburin league phase da maki 24 bayan ta yi nasara a dukkan wasanninta takwas.

Liverpool ta zo matsayi na uku da maki 18, bayan Bayern Munich da ta zo ta biyu, yayin da Tottenham ta kammala a matsayi na huɗu da maki 17.

Chelsea da Manchester City su ma sun tsallaka kai tsaye zuwa zagayen 'yan 16 bayan sun kammala a matsayi na shida da na takwas bi da bi, yayin da Newcastle ta zo ta 12.

Sai dai Chelsea, Manchester City, Newcastle da Tottenham duk sun fita daga gasar tun a zagayen 'yan 16 a kakar da ta gabata. Liverpool kuwa PSG ta fitar da ita a wasan kwata-fainal.

Daga baya PSG ta kai wasan ƙarshe inda ta sake doke Arsenal, ta kuma lashe kofin Champions League karo na biyu a jere.

Za a iya kallon fitattun lokutan dukkan wasannin Champions League daga ƙarfe 10:00 na dare ranar Laraba a BBC iPlayer da kuma shafin BBC Sport da manhajarsa.

Haka kuma za a gabatar da shirin Champions League Match of the Day a tashar BBC One ranar Laraba daga ƙarfe 10:40 na dare zuwa tsakar dare.