'Yan wasan Najeriya da za su haska a gasar Premier League ta 2026/27

Wasa

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 6

A gasar Premier League ta 2026/27, za a ganin wasu matasan ’yan wasan Najeriya, inda kusan ’yan Super Eagles tara ke wakiltar kungiyoyi biyar daban-daban.

Cikin jerin akwai fitattun ’yan wasa irin su Alex Iwobi, Calvin Bassey da Ola Aina, yayin da matasan ’yan wasa Benjamin Fredrick da Zadok Yohanna da ke wakiktar kungiyoyinsu a babbar gasar ta kwallon kafa a Ingila.

Haka kuma, akwai wadanda suka koma sababbin kungiyoyins kamar Taiwo Awoniyi da Frank Onyeka, wadanda yanzu suke taka leda a Coventry City, yayin da Semi Ajayi da David Akintola ke cikin tawagar Hull City, wadda ta dawo gasar Premier League.

Ga bayanan kowane dan wasa da kulob din da yake bugawa:

Benjamin Fredrick — Brentford

Benjamin Fredrick na daga cikin matasan ’yan wasan Najeriya da za su buga Premier League, kuma yana cikin wadanda ake sa ran za su ja hankali.

An haifi Fredrick a Kaduna, inda ya fara taka leda a kungiyar Simoiben Football Academy da ke Kaduna, kafin ya koma buga wa ABS, sannan Nasarawa United wasa a Najeriya.

Ya koma Ingila a 2023, inda ya fara taka leda a kungiyar matasan Brentford, Brentford B, a matsayin aro.

Kokarinsa ya sa Brentford ta dauke shi na dindindin a 2024. Daga bisani ya zama muhimmin dan wasa a kungiyar matasan kulob din, inda ya lashe kyautar gwarzon dan wasan Brentford B a 2025. Ya kuma taimaka wa kungiyar ta lashe gasar Under-21 Professional Development League.

Bayan ya koma Belgium a matsayin aro domin buga wa FCV Dender wasa, rauni ya katse zamansa, inda ya koma Brentford.

A kakar 2026/27, an daga shi zuwa tawagar farko ta Brentford, inda ya kuma sanya hannu kan sabon kwantiragi na shekaru hudu.

Fredrick ya fara bugawa Najeriya wasa a matakin manya a 2025, kuma yanzu yana fatan nuna kansa a matsayin fitaccen dan wasan Premier League.

Zadok Yohanna — Brighton & Hove Albion

Tafiyar Zadok Yohanna zuwa matakin Premier League ta kasance cikin sauri sosai.

Matashin ya fara harkar kwallon kafa ne a Ikon Allah Football Academy da ke Kaduna a Najeriya, kafin ya koma Sweden a 2025 domin komawa kungiyar AIK.

A AIK, Yohanna ya yi saurin dagawa daga matakin matasa zuwa tawagar farko. Ya buga wasa 18 a gasar lig da sauran kofuna a lokacin da ya fara samun damar taka leda, inda ya ci kwallo biyar sannan ya taimaka aka ci wasu hudu.

Hakan ya ja hankalin Brighton, wadda ta dauke shi kan kwantiragin shekara biyar da zai ci gaba har zuwa 2031.

Wannan komawa Brighton babbar dama ce ga matashin dan wasan, wanda zai iya taka leda a matsayin lamba 10 ko kuma dan wasan gefe mai shigowa tsakiyar fili.

Brighton na kallon sa a matsayin dan wasa mai kuzari, saurin gudu da iya fuskantar abokan hamayya kai tsaye.

Yohanna na daga cikin sabbin ’yan wasan Najeriya da ya kamata a sa ido sosai a kansu a wannan kakar.

Ola Aina — Nottingham Forest

Ola Aina na daga cikin ’yan wasan Najeriya mafi kwarewa a wannan jerin.

An haife shi a Landan, inda ya fara Amin horo a makarantar koyon kwallon kafa ta Chelsea. Ya samu nasarori da dama a matakin matasa kafin ya fara bugawa babbar tawagar Chelsea wasa.

Daga baya ya koma Torino ta Italiya, inda ya fara taka leda a matsayin aro kafin daga bisani kungiyar ta dauke shi na dindindin.

Aina ya koma Ingila tare da Fulham a kakar 2020/21 a matsayin aro, inda ya buga wasa 31 na Premier League.

Bayan wasanninsa a Italiya da Ingila, ya koma Nottingham Forest a 2023. Tun daga lokacin ya zama muhimmin dan wasa a kungiyar.

A kakar 2024/25, ya buga wasa 35 na Premier League, sannan ya tsawaita kwantiraginsa da Forest har zuwa 2028.

Aina ya shiga sabuwar kakar a matsayin daya daga cikin ’yan wasan baya mafi kwarewa na Najeriya.

Calvin Bassey — Fulham

Calvin Bassey ya bi wata hanya mai ban sha'awa kafin ya kai ga Premier League.

An haife shi a Italiya ga iyayen Najeriya, amma ya girma a Landan. Ya taso ne a makarantar koyon kwallon kafa ta Leicester City, ko da yake bai samu damar buga wa babbar tawagar kungiyar wasa ba.

A 2020 ya koma Rangers ta Scotland, inda ya yi suna cikin kankanin lokaci.

Ya lashe gasar Scotland da Scottish Cup, sannan ya taka muhimmiyar rawa a lokacin da Rangers ta kai wasan karshe na Europa League a 2022.

A wannan shekarar ne Ajax ta Netherlands ta dauke shi, kafin Fulham ta saye shi a 2023.

A Fulham, Bassey ya zama daya daga cikin ’yan wasan baya na kungiyar, kuma yana iya taka leda a matsayin mai tsaron baya na tsakiya ko kuma na gefen hagu.

Ya kuma zama daya daga cikin fitattun ’yan wasan Super Eagles.

Alex Iwobi - Fulham

Alex Iwobi na daga cikin ’yan wasan da suka fi kwarewa a Premier League a wannan jerin.

Shi ne dan uwan shahararren tsohon dan wasan Najeriya Jay-Jay Okocha. Iwobi ya taso ne a makarantar koyon kwallon kafa ta Arsenal, inda ya samu damar shiga babbar tawagar kungiyar kafin ya koma Everton a 2019.

Ya koma Fulham a 2023, inda ya zama muhimmin dan wasas tsakiya da kuma wajen kai hari.

A watan Yunin 2026, Iwobi ya cimma wani babban tarihi bayan ya buga wasansa na 100 da Super Eagles, inda ya shiga cikin rukunin ’yan Najeriya kalilan da suka kai wannan adadi.

Ya buga daruruwan wasanni a Premier League kuma har yanzu yana daga cikin ’yan wasan Najeriya da suka fi iya kirkirar damar cin kwallo.

A Fulham, iya taka leda a wurare daban-daban ya sa yake da matukar amfani ga kungiyar.

Taiwo Awoniyi — Coventry City

A watan Agustan 2026, ya koma Coventry City daga Nottingham Forest, a yarjejeniyar da aka ruwaito ta kai kusan fam miliyan tara.

Tafiyarsa zuwa Premier League ta fara ne daga Imperial Soccer Academy a Najeriya, kafin Liverpool ta dauke shi tun yana matashi.

Saboda matsalolin samun izinin aiki a Ingila, ya shafe shekaru yana zuwa kungiyoyi daban-daban a matsayin aro, ciki har da kungiyoyi a Jamus, Belgium, Netherlands da Ingila.

Lokacin da ya fi yin fice shi ne a Union Berlin ta Jamus, inda ya zama dan wasan gaba mai yawan cin kwallaye.

Forest ta dauke shi a 2022, kuma ya yi tasiri sosai a kakarsa ta farko a Premier League, inda ya ci kwallaye 10 a gasar a kakar 2022/23.

Yanzu da yake Coventry, Awoniyi zai yi fatan dawo da mafi kyawun salon wasansa tare da taimaka wa kungiyar da kwallaye yayin da take dawowa Premier League bayan shafe shekara 25.

David Akintola — Hull City

David Akintola ya bi kungiyoyi da dama a kasashe daban-daban kafin ya kai ga Premier League.

Dan wasan dan asalin Oyo ya fara sana'ar kwallon kafa a FC Ebedei, kafin ya koma kungiyar Midtjylland ta Denmark.

Daga nan ya yi zaman aro a kungiyoyi da dama ciki har da Thisted, Jerv, Haugesund, Rosenborg, Omonia da Hatayspor.

Daga bisani ya buga wa Adana Demirspor da Çaykur Rizespor wasa a Turkiyya.

Hull City ta dauke shi a watan Agustan 2025 kan kwantiragin shekaru biyu.

A kakar 2025/26, ya buga wasanni 20 na Championship da Hull, inda ya ci kwallo daya sannan ya taimaka aka ci wasa biyu.

Yanzu da Hull ta koma Premier League, dan wasan mai shekaru 30 ya samu damar gwada kansa a matakin mafi girma na kwallon kafa a Ingila.

Semi Ajayi — Hull City

Semi Ajayi ya zo Hull da kwarewar Premier League sosai.

An haife shi a Landan, inda ya taso a makarantar koyon kwallon kafa ta Charlton Athletic, kafin ya yi wasa a kungiyoyi kamar Cardiff City da Rotherham United.

Ya kafa kansa sosai a West Bromwich Albion, inda ya shafe shekaru shida tare da kungiyar kuma ya buga wasanni sama da 200 a dukkan gasa.

Hull City ta dauke shi a 2025.

Komawarsa Premier League ta samu kyakkyawan farawa.

A wasan farko na Hull a kakar 2026/27, Ajayi ya ci kwallon farko ta Hull a wasan da ta doke Manchester United da ci 2-0.

Ga dan wasan baya, wannan wata babbar hanya ce ta sanar da dawowarsa gasar Premier League.

Ajayi ya kuma kasance cikin tawagar Super Eagles na tsawon lokaci, inda ya buga wasanni sama da 50 wa Najeriya.

Frank Onyeka — Coventry City

Frank Onyeka shi ne na karshe cikin ’yan wasan Najeriya tara.

Onyeka ya fara sana'ar kwallon kafa ne da FC Midtjylland ta Denmark bayan ya taso daga FC Ebedei a Najeriya.

Ya zama muhimmin dan wasa a Denmark, inda ya lashe gasar lig da kofuna, sannan ya samu damar buga gasar Champions League.

Brentford ta dauke shi a 2021, inda ya zama dan wasan farko da kungiyar ta saye tun bayan da ta shiga Premier League.

Bayan shekara hudu a Brentford, ciki har da zaman aro a kungiyar Augsburg ta Bundesliga, Onyeka ya koma Coventry City na dindindin a watan Yunin 2026.

Ya taimaka wa Coventry wajen lashe Championship da samun gurbin zuwa Premier League.

Yanzu zai sake haduwa da dan uwansa na Super Eagles, Taiwo Awoniyi, a Coventry.

Kuzarinsa, karfinsa da iya taka rawar tsaron tsakiyar fili na iya zama muhimmin abu yayin da Coventry ke kokarin kafa sansani a Premier League.

Sabuwar kakar, sabon kalubale ga 'yan Najeriya

Daga gogaggun ’yan wasan kasa irin su Iwobi, Aina, Bassey, Ajayi da Onyeka, zuwa matasa masu tasowa kamar Fredrick da Yohanna, Najeriya na da dimbin wakilci a Premier League ta 2026/27.

Abin da ya kara sanya kakar ta bana ta zama ta musamman shi ne kasancewar Coventry City da Hull City sun dawo Premier League, wanda ke nufin ’yan Najeriya hudu daga cikin tara suna buga wa kungiyoyin da suka samu karin girma daga Championship wasa.

Ga Super Eagles, wannan kakar za ta kasance wata dama ta bibiyar haduwar kwarewar tsofaffin ’yan wasa, wadanda suka riga suka kafa kansu a Premier League, da kuma sabbin ’yan wasa masu tasowa wadanda ke neman kafa tarihi a nan gaba.