Yadda za ku kare yaranku daga kamuwa daga cutar mashaƙo

Asalin hoton, Getty Images
Kimanin yara 50 ne suka mutu sakamakon ɓarkewar cutar diphtheria a jihar Kano.
Ɗan majalisar dokokin jihar Kano mai wakiltar mazaɓar Rano, Ibrahim Muhammad ne ya bayyana haka lokacin zaman majalisar a wannan mako, yana mai cewa akwai wasu da dama da ke kwance a asibitoci suna karɓar magani sakamakon wannan cuta, kamar yadda Jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Hon Muhammad ya shaida wa Majalisar cewa ɓarkewar cutar ta fi ƙamari a ƙauyukan Ridin da Sabuwar Kaura, inda mafi yawan waɗanda suka kamu suka rasa rayukansu.
Ya ce duk da cewa an fara ɗaukar matakan gaggawa, ciki har da samar da magunguna da tura ma'aikatan lafiya zuwa yankunan, har yanzu akwai buƙatar ƙarin tallafi cikin gaggawa domin dakile yaɗuwar cutar.
Ɗanmajalisar ya yi kira ga Gwamna Abba Kabir Yusuf da kwamishinan lafiyar jihar su samar da ƙarin tallafin gaggawa ga al'ummomin da lamarin ya shafa.

Asalin hoton, Getty Images
Mece ce cutar mashaƙo?

Asalin hoton, Getty Images
Dakta Usman Bashir, likitan kula da lafiyar al’umma ne a asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano da ke jihar Kano, ya ce cutar mashako dai wata cuta ce da ke kama yara waɗanda suka kai shekara biyar da kuma manya da suka haura shekara 60.
Dr Usman ya ce cutar tana an fi samunta a wuraren da ba a fiya yin alluran rigakafi ba. Kama garkuwar jikin ɗan adam take kamawa ta yi mata mummunar illa.
Likitan ya ce cutar tana saurin kisa saboda ba a gane ta da wuri idan an kamu, kuma a mafi yawan lokuta sai ta kai ga yaro ya fara numfashi cikin wahala, ko kumaya gaza cin abinci ko ya kamu da zazzabi mai tsanani ko kuma yawan tari.
Ya ce cutar na yaɗuwa ne ta hanyar zama cikin cunkoso a ɗaki ɗaya, musamman wanda aka rufe tagoginsa babu wajen shan iska da kuma waɗanda ba a yi wa allurar rigakafi ba wadda ke bayar da garkuwa ga kwayoyin halittar ɗan adam da ke yaƙar kwayoyin cutar.
Ya kuma ce tana ɗaya daga cikin cutukan yara da ke saurin kisa, sannan tafi tashi a lokacin sanyi.
Yadda cutar ke kama mutum
Tsohon shugaban hukumar yaki da cutuka masu yaɗuwa ta Najeriyar Farfesa Abdussalam Nasidi, ya shaida wa BBC cewa cutar mashaƙo, na kama maƙogoro ne, tare da hana mutum sakat.
Ya ce: ''Idan ta kama mutum za ta riƙe masa wuya kamar an shaƙe ka, idan ta kama yaro idan ba Allah ne ya kiyaye ba a gaban iyayensa za a rasa shi, don haka babbar barazana ce''.
Wasu alamomin cutar
Alamomin cutar na fara bayyana a jiki ne cikin kwanaki biyu zuwa biyar.
- Tari
- Zazzabi mai zafi
- Rashin cin abinci
- Kumburin cikin baki
- Numfashi sama-sama
- Yoyon hanci
- Gajiya
Hanyoyin kauce wa kamuwa da cutar mashaƙo
Likitoci sun ce hanya ɗaya ta kauce wa kamuwa da cutar mashaƙo ga manya da ƙananan yara ita ce yin allura, saboda za ta kashe ƙwayoyin cutar da ke jikin mutum.
Yana da muhimmanci a wayar da kan al’umma wajen yi wa yara allurar riga-kafi, domin hakan zai iya magance ba wai mashaƙo kaɗai ba har da cutar sarƙewar haƙora da ƙyanda da sauransu.









