Abin da mazauna ƙauyukan da aka sace mutane 500 a jihar Niger suka shaida wa BBC

Asalin hoton, Presidency/Getty Images
Mutanen da suka kuɓuta daga mummunan harin ƴanbindiga a jihar Niger da ke tsakiyar Najeriya sun shaidawa BBC yadda maharan suka kashe gomman masu ibada sannan suka yi garkuwa da wasu da dama daga ƙauyuka huɗu.
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya umarci jami'an tsaron ƙasar su gaggauta bin sahun maharan omin ceto waɗanda aka sata a ranar Juma'a 21 ga watan Ogusta, a yankin Borgu na jihar Niger.
Rahotanni sun ce ƴanbindigar sanye da kayan soji sun afkawa ƙauyukan Dekara da Gidan Zana da Sabon Gida da kuma Masaka.
Kakakin rundunar ƴansandan jihar Niger Wasiu Abiodun ya shaidawa BBC cewa naharan sun kashe mutane fiye da 40. Amma mahukunta sun ce ba za su iya tabbatar da haƙiƙanin adadin mutanen da aka kashe da kuma waɗanda aka yi garkuwa da su ba.
"a ranar 21/08/2026 da ƙarfe 4 na yamma rahoto ya zo mana cewa da misalin ƙarfe 2 na rana wasu da ake zargin ƴan ta'adda ne sun afkawa ƙauyukan Gidan-Zana da Kpenya kuma sun shiga ne ta yankin Dekara na gundumar Borgu kuam sun kai hari masallacin Kpenya inda suka yi garkuwa da mutanen da ba a tabbatar da yawan su ba, yayin da wasu suka gudu zuwa cikin daji,'' in ji Abiodun.
Abiodun ya ƙara da cewa daga bayanan da suka tattara babu wanda aka kashe kuma sun tura tawagar jami'ansu zuwa yankin domin tantance abinda ya faru da kuma ceto waɗanda aka sace.

Asalin hoton, AFP via Getty Image
Mazauna yankin sun bayyana damuwar cewa yawan mutanen da aka sace na iya zarce yadda mahukunta suka sanar.
Wani jagoran matasa da aka ɓoye sunansa saboda dalilan tsaro ya shaidawa BBC cewa mutanen da aka sace sun kai 500.
Ƙiyasin nashi ya biyo bayan wani bidiyo da ƴanbindigar suka fitar a kafafen sada zumunta wanda ya nuna mata da ƙananan yara a zaune cikin daji, a hannun maharan.
Jagoran matasan ya ce ya gane mutanen ƙauyen su da dama daga cikin bindiyon.
"Na iya gane mutane da yawa. Daga cikin su akwai wanda kamar kaka ne a gare mu, kuma mazaunin ƙauyen Gidan Zana ne.''
Ya ce iyalan da suka ga ƴan uwansu a cikin bidiyon sun samu kwanciyar hankali cewa ƴan uwan nasu suna raye.
Ya ƙara da cewa: "Aƙalla sun samu tabbacin ƴan uwansu suna raye kuma suna fatan a ceto su, b kamar waɗanda ba su da wani labari game da nasu ƴan uwan da aka sace ba.''
Jagoran matasan ya ce a ranar Litinin suka yi janaizar mutane aƙalla 30 da maharan suka kash, kuma ya ce har yanzu ƴanbindigar ba su kira domin bayyana abin da suke buƙata ba.
A cikin bindiyon an ga wani daga cikin ƴanbindigar yana aikewa da saƙo ga iyalan mutanen da ke hannun su.
Ya ce su sanya ido su gano ƴan uwansu a cikin mutanen da ke hannun su.
"Ga mutanen ku nan. Muna nuna wannan bidiyo ne domin ku gane ƴan uwanku, da iyayen ku da ƴaƴa da kuma makusanta,'' in ji danbindigar.
Rundunar ƴansandan jihar Niger ta ce tana cigaba da ƙoƙarin tantance bindiyon kuma batun yana da sarƙaƙƙiya sosai.
BBC ba ta tantance ingancin bidiyon ba amma jama'ar ƙauyen sun iya gano wasu daga cikin ƴan uwansu da aka sace a cikin mutanen da aka nuna a bidiyon.
Ibrahim Abubakar ya shaidawa kamfanin dillacin labarai na Reuters cewa ''Na gane mutane 13 ƴan Dekina a cikin bidiyon.''
Wani fitacce a shafukan sada zumunta da ke yankin ya shaidawa BBC cewa mutane da dama sun gudu daga gidajen su, inda suka nemi mafaka a jihohin da ke maƙwabtaka da su, yayin da wasu kuma suka tsallake zuwa jamhuriyar Benin.
Wasu daga cikin mutanen da suka tsira suna kwance a asibiti, ciki harda masu munanan raunuka.
Wani jami'i ya shaidawa BBC cewa maharan sun dasa wasu abubuwan fashewa a sassan ƙauyukan da suka kai hari, yayin da suka yi awon gaba da mutane zuwa cikin daji.
Ya ce akwai wani saurayi da ya mutu bayan tashin ɗaya daga cikin nakiyar da maharan suka dasa.
Wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban Najeriya Bayo Onanuga ya fitar ta ce shugaba Tinubu ya yi Allah wadai da kisan mutanen da kuma garkuwa da wasu, kuma ta yi alƙawarin hukunta duk masu hannu a lamarin.
"Waɗanda suka aikata wannnan mummunan aiki kan ƴan Najeriya da basu ji ba, ba su gani ba, maƙiyan ƙasa ne kuma za mu tabbata sun girbi abin da suka shuka,'' in ji sanarwar.
Shugaban ya kuma yi ta'aziyya ga iyalan mutanen da aka kashe.
Harin yana daga jerin matsalolin tsaro na baya-bayan nan a yankin Borgu, wanda ke da iyaka da jihohin Kebbi da Kwara da kuma jamhuriyar Benin.
A farkon watan nan ƴansanda sun ce sun ceto mutane 145 da aka sace a ƙauyukan yankin.
Mahukunta a yankin sun daɗe suna bayyana damuwa kan matsalar tsaro da ta addabe su.
Matsalar garkuwa da mutane ta zamo babban ƙalubalen tsaro a Najeriya, ta yadda da wuya a wuce wata biyu ba a samu rahoton sace mutane ba.
Ba da dadewa ba jami'an tsaron ƙasar suka ceto ƴan makaranta da malamansu da aka sace a garin Orire.
An gurfanar da mutane uku da ake zargi da hannu a garkuwa da mutanen, yayin da gwamnati ta nemi kotu ta zartar masu da hukunci. Dukkan su kuma sun amsa laifin da ake zargn su da aikatawa.
A lokacin aikin ceto mutanen Orire, wani hafsan sojin Najeriya ya rasa ransa.
Wannan ɗaya ne kacal daga cikin sace mutane da ake fama da su a sassan ƙasar.
Shugaba Bola Tinubu ya sauya manyan jami'an tsaron ƙasar, amma da alama har yanzu akwai sauran aiki a gaban su.
A watan Mayu, ƴanbindiga sun sace mutane 50 daga jihar Borno. Kuma yanzu
babbar tambayar ƴan Najeriya ba ta wuce yaushe za a kawo ƙarshen garkuwa da mutane a ƙasar ba.






