EFCC za ta wanda ya fallasa kuɗin sata da aka ɓoye a ƙasar waje kashi 5

Asalin hoton, EFCC/FACEBOOK
Hukumar EFCC ta ce mutanen da suka bayar da sahihan bayanai da za su taimaka wajen gano dukiyar da aka wawure daga Najeriya tare da ɓoyewa a ƙasashen waje, na iya samun lada har zuwa kashi 5 cikin 100 na asalin dukiyar da aka ƙwato.
Shugaban EFCC, Ola Olukoyede, ya yi kira ga mutanen da ke da sahihan bayanai kan inda aka boye kuɗaɗe da kadarorin Najeriya a ƙasashen waje da su fito su bayar da bayanan.
Ya yi wannan kiran ne yayin wani taro kan laifukan tattalin arziki da aka gudanar a Cambridge, Ingila, ina ya ce a ƙarƙashin tsarin ladar, mai fallasa bayanai (whistleblower) wanda bayanansa suka kai ga samun nasarar ƙwato dukiya, na iya samun lada tsakanin kashi 2.5 zuwa 5 cikin 100 na ƙimar dukiyar da aka ƙwato.
Da yake magana a taron, Olukoyede ya ce ya kamata a ƙara matakan kariya ga mutanen da ke bayar da bayanan da ke taimakawa wajen tona asirin laifukan kuɗi, inda ya nanata cewa kariyar na da muhimmanci, musamman a ƙasar da wasu masu bayar da bayanai ke fargabar ramuwar gayya bayan fallasa mutanen da ke da alaƙa da siyasa ko kuma masu tasiri a ƙasar.
Najeriya ta ƙaddamar da manufar kare masu fallasa bayanai ta gwamnatin tarayya a shekarar 2016, wadda ta tanadi lada ga mutanen da suka taimaka wajen fallasa almundahana, ɓoye ko karkatar da kuɗaɗen gwamnati da kadarorinta. Sai dai, duk da alkawarin bayar da lada, an taɓa nuna damuwa cewa wasu masu fallasa bayanai sun shafe lokaci suna jiran biyan kuɗaɗen da aka yi musu alkawari. Haka kuma, babu wata takamaiman doka da ke ba su cikakkiyar kariya.
Sai dai sabuwar sanarwar EFCC kan ladar ta haifar da tambayoyi kan ko hukumomi za su iya tabbatar da sirri, kariya da kuma biyan ladan kamar yadda aka yi alƙawari.




















