Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Mene ne aikin gidauniyar yaƙi da matsalar tsaro a Arewa?
Ƙungiyar Gwamnonin jihohin Arewacin Najeriya ta ƙaddamar shugabancin kwamitin amintattu na gidauniyar yaƙi da matsalar tsaro ta yankin da aka samar.
Gwamnonin yankin sun ce an kafa gidauniyar ne a yunƙurin da suke yi na daƙile matsalar tsaron da ke ci gaba da addabar yankin.
Ƙungiyar gwmnonin ta amince da matakin kafa kwamitin ne a taron da ta gudanar a jihar Kaduna cikin wanna mako.
Gwamnonin sun kuma buƙaci duka jihohin yankin da masu riƙe da sarautun gargajiya da ƙungiyoyin fararen hula da kafafen yaɗa labarai su mutunta kwamitin tare da ba shi haɗin kan da ya dace domin aikinsa na lalubo hanyoyin inganta tsaro a yankin.
Tuni dai ƙungiyar gwamnonin suka sanar da shugabannin kwamitin da za su jagoranci ragamar aikin.
Arewacin Najeriya na fama da matsaloli na tsaro, inda ake da yawaitar mutanen da rikici ya tarwatsa, wani abu da ya ƙara jefa yankin cikin mummunan hali.
Baya ga ƙungiyar Boko Haram da ta daɗe tana addabar yankin, ƙungiyoyin ƴan bindiga da suka ɓulla a jihohin arewa maso yammacin ƙasar sun ƙara jefa yankin cikin mawuyacin hali.
Su wane ne mambobin kwamitin?
Ƙungiyar gwamnonin ta sanar da mambobin kwamitin waɗanda suka ƙunshi ƙwararru a fannoni da dama daga jihohin ƙasar.
Ƙwamitin na ƙarƙashin jagorancin Alhaji Mahmoud Yayale Ahmed, CFR daga jihar Bauchi da kuma Janar Martin Luther Agwai, CFR mai ritaya, tsohon babban hafsan tsaron Najeriya, daga jihar Kaduna.
Sauran mambobin kwmaitin sun haɗa da:
1. Lt Gen. Umar Farouk Yahaya (rtd) - Sokoto
2. DIG Hafiz Mohd Inuwa (rtd) – Jigawa
3. AVM Kabiru Aliyu (rtd) – Taraba
4. Prof. Usman Tar – Borno
5. AVM Napoleon Bali (rtd)
6. Maj. General A. M. Dikko (rtd) – Niger
7. AIG Sunday Babaji (rtd) – Gombe
8. AVM Farouk Omeiza Umar (rtd) – Kogi
9. Maj. Gen. Muhammad Sani (rtd) – Kano
10. Muhammad Mujtaba Isa – Zamfara
11. Alh. Adamu Tanko Umar – Nasarawa
12. Malam Abubakar Mustafa – Kaduna
13. DIG Sani Usman Mohammed (rtd) – Bauchi
14. Maj-Gen. Bello Sarkin Yaki (rtd) – Kebbi
15. Barr. Boss Mustafa, CFR – Adamawa
16. Alhaji Falalu Bawale – Katsina
17. Brig. Gen. Ibrahim Bolakala Agbab (rtd) – Kwara
18. Maj. Gen John Seyina Malu (rtd) – Benue
19. IGP Usman Alkali Baba (rtd) – Yobe
Mene ne aikin kwamitin?
Ƙungiyar gwamnonin arewar ta ɗora wa kwamitin alhakin gudanar da ayyuka kamar haka.
- Kula da kuɗaɗen asusun Gidauniyar Tsaron
Gwamnonin sun amince su riƙa bayar da naira biliyan ɗaya a kowane wata ga gidauniyar tsaron, don haka mambobin kwamitin za su riƙa kula da kuɗaɗe tare da aiwatar da yadda aka tsara kashe su.
- Sayen kayan aikin da jami'an tsaro ke buƙata
Kwamitin ne zai riƙa kula da sayen kayan aikin leƙen asiri da kayan yaƙi da jami'an tsaron da ke aiki a yankin ke buƙata.
- Haɗin kan tsaro tsakanin jihohin Arewa
Ɗaya daga cikin manyan ayyukan kwamitin shi ne ƙoƙarin aiki tare don magance matsalar tsaro tsakanin jihohin arewacin ƙasar, musamman kula da kan iyakokinsu.
- Taimaka wa gwamnatin tarayya da ƙarfafa ƴan sa-kai
Gwamnonin arewacin Najeriyar sun kuma ce kwamitin zai riƙa aiki tare da gwamnatin tarayya, tare da ƙarfafa ayyukan jami'an sa-kai da wasu jihohin yankin ke da su.
- Magance abubuwan da suka haddasa matsalolin tsaron arewa
Gwamnonin sun kuma ɗora wa sabon kwamitin alhakin haɗa kai da sarakunan gargajiya da shugabannin al'umma da masu ruwa da tsaki domin magance abubuwan da ke janyo tashin hankali.
Haka nan an buƙaci kwamitin ya lalubo hanyoyin zamanantar da kiwon dabbobi da magance matsalolin jin-kai, musamman waɗanda suka shafi gudun hijira.
Daga ina za a samu kudin da ake buƙata?
Ƙungiyar gwamnonin ta alƙawarta tara naira biliyan ɗaya a kowane wata tsakaninsu domin inganta ayyukan tafiyar da Gidauniyar.
To sai dai kawo yanzu babu tabbaci kan abin da kowace jiha za ta bayar.
Haka kuma babu tabbaci kan har zuwa wane lokaci jihohin za su riƙa tara kuɗin.
Jihohin arewacin ƙasar dai dama na fuskantar matsalar tsaro, wadda masana ke cewa na haifar da koma-baya ga yankin.
Waɗanne ƙalubale kwamitin zai fuskanta?
Sai dai duk da wannan yunƙuri da gwamnonin arewacin Najeriyar suka yi, masana al'amuran tsaro na ganin yunƙurin nasu zai iya cin karo da ƙalubale.
Dr Kabiru Adamu, shugaban kamfanin Beacon Security Limited, da ke nazarin al'amuran tsaro a yankin Sahel ya bayyana wasu daga cikin ƙalubalen da yake ganin kwamitin zai iya fuskanta da suka haɗa da:
- Rashin saka ƙungiyoyin fararen hula cikin kwamitin
Dr Kabiru Adamu ya ce duk da kwamitin cike yake da tsoffin jami'an tsaro da suka san harkar ayyukan jami'an tsaro, amma akwai buƙatar saka wakilan fannoni daban-daban da suka haɗa da ƙungiyoyin fararen hula da mata da matasa da malaman jami'a.
''Mambobin da aka saka babu shakka suna da ƙwarewa ta aiki a fagen yaƙi da ilimin nazarin haɗari da tantance kasada da tsarin kariya da tattara bayanai da samar da hanyoyin zamani da suka dace da yanayin Najeriya, amma duk da haka suna buƙatar aiki tare da ƙwararru daga waje'', in ji shi.
Galibi dai mambobin kwamitin tsofaffin manyan jami'an tsaro ne da tsofaffin ma'aikatan gwamnati.
- Rashin ƙwararrun masu bincike
Shugaban kamfanin na Beacon Security ya kuma ce kodayake akwai murya ɗaya ta ilimi (Prof. Usman Tar) a ciki, kwamitin ba shi da isassun masana bincike masu zaman kansu da masu bincike, waɗanda ke da zurfin ilimi game da yanayin yankin.
''Ƙarfin bincike na gaskiya da fahimtar tushen rikici da yanayin tashe-tashen hankula zai janyo koma-baya ga aikin kwamitin'', in ji shi.
- Rashin zuba jari don inganta rayuwar al'umma
Kabiru Adamu ya ce ya kamata a ce ɗaya daga cikin ayyukan kwamitin shi ne zuba jari a fannoni daban-daban domin inganta rayuwar al'ummar yankin.
''Ba ko yaushe ne amfani da ƙarfin tuwo ke aiki ba, akwai wasu matsalolin da in da an magance su za a samu sauƙin wannan matsala,'' in ji shi.
Ya ce in dai har za a iya samar da naira biliyan ɗaya a kowane wata domin magance matsalar tsaro, to da za a samar da wata biliyan ɗin a zuba jari da ita domin samar da ayyukan yi ga matasa, to za a samu sauƙin matsalar tsaro sosai a arewa.