Iraniyawa na cikin fargaba bayan gaza cimma yarjejeniya

...

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Har yanzu ba a saka sabon ranar gudanar da tattaunawar zaman lafiya ba, yayin da Iraniyawa ke fuskantar rashin tabbas game da makomarsu.
    • Marubuci, Ghoncheh Habibiazad
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Senior reporter, BBC News Persian
  • Lokacin karatu: Minti 2

Tsagaita wutar da ke tsakanin Amurka da Iran wadda take sama take kasa ta ƙara jefa mutane cikin zaman dar-dar bayan tattaunawar zaman lafiya da aka yi tsakanin bangarorin biyu a Pakistan ta ƙare ba tare da cimma wata matsaya ba.

Bayan haka, sojojin Amurka sun ce za su hana jiragen ruwa fita daga tashoshin Iran. Iran kuma ta yi barazanar ramawa ta hanyar kai hari ga tashoshin jiragen ruwa na ƙasashen yankin Gulf.

Jama'a a Iran na bin lamarin cikin tsoro, suna fargabar yiwuwar sake barkewar yaki.

Wani matashi da ke da shekara 20 a Karaj kusa da Tehran ya ce yana ganin yakin na iya dawowa nan ba da jimawa ba, ko gobe ko cikin makonni masu zuwa.

A cikin Iran, gwamnati ta katse intanet fiye da makonni shida, abin da ya sa yana da wahala a tuntuɓi mutane. Gwamnati na cewa hakan na kare ƙasar daga hare-hare ta intanet

BBC ta ce ta tattauna da wasu Iraniyawa masu adawa da gwamnati, amma ra'ayoyinsu ba sa wakiltar dukkan jama'ar ƙasar.

,,

To request:

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Complete the translations here: https://tinyurl.com/3jxuwu4n

Fill-in the commissioning form https://bit.ly/ws_design_form with this title in English: Iran ports - map - 2026041302

Wani matashi a Tehran ya ce "Ba na fatan yaƙin zai sake barkewa amma ina fargabar hakan."

Ya ce yana ƙoƙarin shagaltar da kansa domin kada damuwa ta rinjaye shi.

Wata budurwa kuma ta ce tana ƙoƙarin kasancewa da fata, tana fatan abubuwa za su ƙara lafawa kuma yba ta son yakin ya ci gaba. Ta kuma nuna damuwa kan katsewar intanet, inda ta ce "ina fatan ya dawo domin mutane su samu bayanai da kuma kasuwanci ya dawo daidai. Ta ce idan yaki ya ci gaba, hakan zai cutar da jama'ar Iran sosai.

Yawancin Iraniyawa da suka tattauna da BBC a lokacin rikicin sun bayyana damuwa mai tsanani kan rashin intanet. Sun ce katsewar intanet ya hana su samun bayanai masu inganci kuma ya janyo babbar matsala ga harkokin kasuwanci da rayuwa.

Wani mai aikin kirkirar abubuwa yana saka wa a shafukan sada zumunta ya ce "babu wanda ke cin riba." Ya ƙara da cewa ajiyarsa ta kuɗi ba za ta ɗauke shi fiye da watanni biyu ba kafin ya ƙare.

Wani mutum kuma ya ce yana jin dama-dama tun lokacin da aka cimma yarjejeniyar tsagaita wuta ba kamar lokacin da ake ta kai musu hare-hare ba "amma har yanzu ina cikin damuwa". Ya ce ko da an cimma yarjejeniya, tattalin arzikin da ya lalace zai sa rayuwa ta ci gaba da wahala.

Wani mutum a Karaj ya ce yana ganin shugaban Amurka Donald Trump ba zai yi sassauci ba wajen cimma yarjejeniya saboda siyasar zaɓe da ke tafe a ƙasarsa.

Wani mutum kuma ya fusata saboda kashe masu zanga-zangar adawa da gwamnati, ya ce tattaunawa da gwamnatin Iran ba ta da amfani, yana mai kiran ta masu aikata zalunci. Ya ce ba zai taɓa manta lokacin da aka yi harbi a tituna a gabansa ba.

An kashe dubban masu zanga-zanga a Iran tare da kama dubban mutane da dama, a cewar ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta HRANA.

Har yanzu ba a saka sabon ranar gudanar da tattaunawar zaman lafiya ba, yayin da Iraniyawa ke fuskantar rashin tabbas game da makomarsu.