Abin da ya kamata ku sani kan taron Jam'iyyar ADC na ƙasa

Asalin hoton, Peter Obi/Facebook
Jam'iyyar ADC ta haɗakar masu hamayya a Najeriya ta ce ta kammala shirinta tsaf, domin gudanar da babban taronta na ƙasa a Abuja, babban birnin ƙasar.
A ƙarshen mako ne jam'iyyar - tsagin David Mark - ta gudanar da tarukanta na jihohi, inda ta zaɓi shugabanninta na rassa jihohin.
Tuni dai jam'iyyar ta fitar da jerin kwamitocin babban taron nata.
Taron jam'iyyar na zuwa ne a daidai lokacin da take tsaka da rikicin shugabanci.
Sai dai jam'iyyar ta koka kan ƙalubalen da take fuskanta game da samun wurin da za ta gudanar da taron nata, ko da yake daga baya ta ce za ta yi taron a babban ɗakin taro na Rainbow Event Center da ke Abuja.
'Gwamnatin APC ta hana mu wurin taro'
Tun da farko jam'iyyar ta zargi gwamnatin APC mai mulkin Najeriya ta Shugaba Tinubu da hana ta wurin da za ta gudanar da babban taron nata na Abuja.
Ɗaya daga cikin masu magana da yawun jam'iyyar, Faisal Kabir ya shaida wa BBC cewa sun rubuta buƙata a hukumance ta neman babban filin taro na Eagle Square da ke tsakiyar birnin, amma aka hana su tare da ƙin ba su dama.
''Bayan Eagle Square mun kuma nemi babban filin wasan ƙwallon ƙafa na ƙasa, nan ma aka hana mu, duk wani wuri da zai iya ɗaukar mutanenmu don wannan taro amma sun hana,'' in ji shi.
Ya kuma ce sun koma wurin ƴan kasuwa waɗanda suka mallaki manyan filaye, nan ma ya ce ''gwamnati ta riƙa bi ta na yi musu barazanar kada su ba mu wurin taron'', kamar yadda ya yi ƙarin haske.
Sai a yammacin ranar Litinin ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike ya ce ba su samu wata buƙata daga ADC ba ta gudanar da babban taro a dandalin Eagle Square.
"Babu wanda ya rubuto wasiƙa. Ban san wane wuri suke magana a kai ba. Idan ma ana magana a kan dandalin Eagle Square ne, babu wanda ya rubuto takardar neman yin amfani da dandalin. Babu yadda za a yi mu hana su saboda ai za mu karɓi kuɗi ne," a cewar Wike.
Sai dai daga baya jam'iyyar ADCn ta tabbatar da samun wurin taron nata.
'Za mu yi taronmu a Abuja ko da a kan titi ne'

Asalin hoton, ADC/BBC

Asalin hoton, ADC
Kakakin na ADC ya ce tun da farko ma lokacin da suke shirin ƙaddamar da jam'iyyar hana su wurin taro aka yi a Abuja, sai daga ƙarshe suka samu ɗakin taro na Shehu Musa Yar'Adua suka yi taron.
''Bayan taron ƙaddamar da jam'iyyar tamu, mun yi ƙoƙarin samun ofishi, amma duk inda muka je sai mun biya kuɗi sai gwamnati ta yi wa mai wurin barazana ya hana mu'', kamar yadda ya bayyana.
Faisal Kabir ya ce a yanzu kam sun shirya gudanar da taron nasu babu gudu ba ja da baya.
''A yanzu za mu gabatar da babban taronmu a babban ɗakin taro na Rainbow Event Center da ke Area 8 a yankin Garki da ke Abuja'', in ji wata sanarwa da jam'iyyar ta wallafa a shafinta na X.
Mene ne taron zai ƙunsa?
Kamar dai sauran jam'iyyun siyasar ƙasar, babban taron ADC zai mayar da hankali ne wajen zaɓen shugabannin da za su jagoranci jam'iyyar zuwa zaɓukan 2027.
A shekarar da ta gabata ne jam'iyyar ta zaɓi shugannin nata a matsayin na riƙo ƙarƙashin jagorancin Sanata David Mark, a lokacin ƙaddamar da jam'iyyar.
Don haka ana sa ran babban taron nata zai tabbatar da shugabannin ne a matsayin masu cikakken iko; ba na riƙo ba.
Tuni dai jam'iyyar ta saka ranar 12 ga watan Mayun 2026 a matsayin ranar rantsar da duka shugabannin da ta zaɓa, ciki har da na jihohi.
Gargaɗin da INEC ta yi wa ADC kan taron

Asalin hoton, INEC
Tuni dai hukumar zaɓen ƙasar, INEC ta gargaɗi jagororin jam'iyyar da kada su gudanar da taron nasu, saboda rikicin jam'iyyar da ke gaban kotu.
Cikin wata hira da gidan talabijin na Arise a makon da ya gabata, shugaban hukumar zaɓen ƙasar, Farfesa Joash Amupitan ya ce yin taron nasu ka iya jefa jam'iyyar cikin haɗarin rashin shiga zaɓen 2027.
''Amma in suna ganin za su yi taronsu su suka sani, koda ya saɓa wa hukuncin kotu, amma dai INEC ba ta yanke hukunci, ba haka kawai muke hukunci da kanmu ba, muna yi da umarnin kotu, shi ke yi mana jagora'', kamar yadda ya bayyana cikin hirar.
Rikicin shugabancin jam'iyyar ya samo asali ne tun lokacin da shugabannin jam'iyyar suka yi murabus, kuma David Mark ya zamo sabon shugaba na riƙon ƙwarya, inda aka zaɓi sauran ƴan kwamitin zartarwa babu hamayya.
Za a saurari shari'un jam'iyyar biyu
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Taron Jam'iyyar na zuwa ne a daidai ranar da Kotun Ƙolin ƙasar ke shirin sauraron ƙarar da tsagin David Mark ya shigar gabanta yana ƙalubalantar hukuncin kotun ɗaukaka ƙara da ta kori ƙarar da tsagin na David Mark ya shigar gabanta yana ƙalubalantar hurumin babbar kotun tarayyar na sauraron shari'arta.
Tun da farko tsohon mataimakin shugaban jam'iyyar na ƙasa mai kula da yankin arewacin ƙasar, Nafi'u Bala Gombe ne ya shigar da tsagin David Mark ƙara a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, yana zargin su da ƙwace shugabancin jam'iyyar.
Lamarin da ya sa tsagin na David Mark - ya garzaya gaban kotun ɗaukaka ƙara, inda ya buƙaci kotun ta hana babbar kotun tarayya sauraron batun rikicin shugabancin nata.
Ɓangaren na David Mark ya ce babbar kotun tarayya ba ta hurumin sauraron ƙarar da ta shafi rikicin shugabancin jam'iyya.
To sai dai a hukuncin ta yi, kotun ɗaukaka ƙarar ta tabbatar da hurumin kotun tarayyar na sauraron ƙarar.
Kotun ɗaukaka ƙarar ta kuma bayar da hukuncin a tsaya matsayin da ake gabanin shigar da ƙarar, har zuwa lokacin da kotun za ta yanke hukunci.
Sannan kuma kotun ɗaukaka ƙarar ta buƙaci hukumar zaɓen ƙasar ta janye sunayen tsagin David Mark daga shafinta a matsayin shugabannin jam'iyyar, matakin da hukumar INEC ta zartar ba tare da ɓata lokaci ba.
Haka kuma babbar kotun tarayyar za ta yi zama kan shari'ar dambarwar jam'iyyar da ke gabanta, wanda Leke Abejide ɗan majalisar wakilai na tarayya mai wakiltar Yagba ta Kudu da Yagba ta Gabas a majalisar wakilan ƙasar daga jihar Kogi ya shigar gaban kotun yana ƙalubalantar shugabancin tsagin na David Mark.











