Zarge-zargen da ake yi wa shugaban INEC - Ko za su shafi zaɓen Najeriya na 2027?

Shugaban Inec Amupitan

Asalin hoton, @inecnigeria/X

Lokacin karatu: Minti 7

Yayin da zaɓen Najeriya na 2027 ke ƙara matsowa, haka nan wasu al'umma a ƙasar ke ƙara nuna damuwa game da shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta na ƙasar Joash Amupitan

A cikin ƴan makonnin nan muhawarar da ta kaure a fili da kuma shafukan sada zumunta na ƙasar bisa zargin Amupitan da cewa "ya taɓa nuna goyon baya ga jam'iyyar APC mai mulki", zargin da hukumar ta musanta.

A makon da ya gabata ƴaƴan jam'iyyar ADC ta ƴan adawar da suka yi haɗaka ta miƙa wa hukumar zaɓen takardar neman Amupitan ya sauka daga muƙaminsa, bisa zargin cewa "ba zai iya gudanar da sahihin zaɓe cikin adalci ba".

Wannan matsi da sabon shugaban na Inec ke fuskanta abu ne da ba a saba gani a baya-bayan nan, kasancewar akasarin ƴan Najeriya na yi wa shugabannin hukumar da suka shuɗe kallon masu mutunci da kuma tsayawa a tsakiya.

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya naɗa Farfesa Joash Amupitan a matsayin shugaban hukumar zaɓen Najeriya INEC a watan Oktoban 2025, bayan ƙarewar wa'adin Farfesa Mahmood Yakubu wanda ya shugabanci hukumar na tsawon shekara 10.

Waɗanne manyan zarge-zarge ake yi wa Joash Amupitan?

Zargin alaƙa da jam'iyyar APC

Tun a makon da ya gabata ne aka bankaɗo wani shafin X (Twitter) mai ɗauke da sunan shugaban hukumar ta Inec, Joash Ojo Amupitan, da ake zargin nasa ne, inda aka gano cewa ya wallafa wasu ra'ayoyi da suke nuna goyon baya ga jam'iyya mai mulki ta APC a shekarar 2023.

Duk da yake hukumar zaɓen ƙasar ta musanta zargin, inda ta ce Amupitan ba shi da shafi a X, wasu da suka ce sun yi binciken ƙwaƙwaf sun gano lambar waya da kuma adireshin imel masu alaƙa da shafin, wadanda suka ce sun yi daidai da waɗanda shugaban Inec ɗin ya gabatar a lokacin da ya ke aiki a jami'ar jihar Filato da kuma bayanan da ya gabatar kafin naɗa shi muƙamin.

A ranar Juma'a 11 ga watan Afrilu fitaccen marubucin nan mai tarin mabiya a kafafen sada zumunta mai yawan janyo ce-ce-ku-ce Farfesa Farooq Kperogi ya wallafa wani abu da 'yan Najeriya suka kalla a matsayin tonan asiri ga shugaban na INEC Farfesa Amupitan.

A shafinsa na X Farfesa Kperogi ya wallafa cewa bayan bin diddigi na shekara da shekaru na wallafe-wallafen da Amupitan ya yi a shafinsa na X ya gano cewa mutumin da aka nada ya jagoranci INEC "ɗan jam'iyyar APC ne" kuma mai goyon bayan shugaba Tinubu.

Kperogi ya yi ta bin ƙwaƙƙwafin bayanan da shugaban na INEC ya riƙa wallafawa masu alaƙa da shugaban Najeriya Tinubu.

Sai dai daga bisani an sauya sunan shafin na X zuwa @SundayVibe00, inda aka kulle duka bayanan shafin.

BBC ba ta iya tabbatar da ingancin bayanin ba, amma masu shafukan sada zumunta na ta wallafa shi a matsayin wanda Amupitan ya wallafa a baya.

Zargin nuna ɓangaranci na addini

xxx

Asalin hoton, Multiple

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Tun a farko-farkon naɗin Amupitan, malaman addini a Najeriya suka fara matsin lamba kan a tsige shi saboda zargin "nuna ƙiyayya ga Musulmai".

Majalisar ƙoli kan harkokin Shari'ar musulunci a Najeriya (SCSN) ta bayyana shi a matsayin barazana ga amincin tsarin dimokraɗiyyar Najeriya.

Shugaban Majalisar Ƙolin Dr Bashir Aliyu Umar jaddada iƙirarin cewa Amupitan ba zai yi adalci ba saboda wasu ra'ayoyin da ya bayyana a baya waɗanda suka nuna cewa ya karkata zuwa wani ɓangare na al'ummar ƙasar,

Don haka ba za a amince da zaɓen da zai gudanar ba, a cewar Dr Bashir.

A wata hirar da ya yi da BBC, Sheikh Bashir, ya yi gargadin cewa Musulmin Najeriya ba za su amince ko halasta duk wani sakamakon zaɓe da aka gudanar ƙarƙashin jagorancin Amupitan ba.

Sheikh Umar ya ce matsayar majalisar ta samo asali ne a kan abin da ta bayyana a matsayin abubuwan da shugaban hukumar ta INEC ya aikata a baya, musamman ma wani taƙaitaccen bayani na shari'a da ake zargin ya rubuta wanda ke nuna cewa ya amince da batun cewa ana yi wa Kirista kisan kiyashi a Najeriya – iƙirarin da gwamnatin tarayyar ƙasar ta sha musantawa.

''Har yanzu muna kan bakarmu, saboda shi shugaban hukumar zaɓe bai fito ya musanta cewa wannan abun ba haka ba ne. Ya na nan kan iƙirarinsa, bai ma ga cewa wannan wani abu ne da zai fito ya yi magana a kai ba,'' in ji shi Sheikh Umar.

A baya-bayan nan ma, cikin wata sanarwa da majalisar ƙolin ta fitar a makon jiya ta nuna takaicinta ga matsayar Gwamnatin Tarayya na ƙin sauraren ƙungiyoyi masu neman a sauke Farfesa Amupitan daga muƙaminsa.

Ta ce yana daga cikin mutanen da suka "rubuta wasiƙa ga Amurka" wadda ta kai ga ayyana Najeriya a matsayin ƙasar da "ake kashe Kiristoci".

"Muna kaɗa ƙuri'ar yanke ƙauna ga Shugaban INEC. Gwamnatin Tarayya ya kamata ta maye gurbinsa da wani Kiristan da zai iya haƙurin zama da abokan zamansa Musulmai da sauran mabiya addinai".

Ba mu yarda da Amupitan ba - Jam'iyyun adawa

Wani zargin da ake yi wa shugaban na Inec ya fito ne daga jam'iyyun adawa a ƙasar, inda suka ce ba su da natsuwar cewa Amupitan zai musu adalci, inda har aka gudanar da zanga-zanga a ƙasar da buƙatar a tsige shi ko ya yi murabus.

Tun bayan da hukumar zaɓe ta INEC ta bayyana cewar Sanata David Mark ba shi ne shugaban jam'iyyar ADC ba, ta kuma cire sunansa daga shafinta da sauran jagorarin da suke ƙarkashinsa bisa dogaro da wani hukuncin kotu, 'yan jam'iyyar ta ADC ɓangaren Sanata David Mark suke ta caccakar shugaban hukumar.

A wani taron da suka gudanar a ranar 2 ga watan Afrilu, 'yan jam'iyyar ta ADC ɓangaren Sanata David Mark sun yi kira ga shugaban hukumar INEC ya yi gaggawar sauka daga muƙaminsa ko kuma gwamnati ta cire shi.

Daga bisani shugabancin David Mark da sauran jagorrin jam'iyyar sun jagoranci zanga-zanga a birnin tarayyar ƙasar Abuja, inda suka ce suna fargabar ADC da sauran jam'iyyun adawar ƙasar ba za su samu adalci ba a zaɓen da za a yi a 2027 matuƙar Farfesa Amupitan ne ke shugabantar INEC.

Ita ma babbar jam'iyyar adawa ta PDP ba a bar ta a baya ba wajen nuna rashin amincewa da jagorancin Amupitan.

Jam'iyyar ɓangaren Kabiru Tanimu Turaki wanda ya yi wani taron haɗin gwiwa da jam'iyyar ADC, ya nuna shakkunsa bisa abin da ya kira rashin tabbas da kasancewa "ɗan amshin shata" ga jam'iyyar APC mai mulki da suka gani a tattare da Farfesa Amupitan.

Ko zarge-zagen za su shafi zaɓen 2027?

Auwal Musa Rafsanjani, jagoran ƙungiyar Transparency International da ke sanya ido kan harkokin zaɓe a Najeriya, ya ce zarge-zargen sun yi tasiri a zukatan ƴan Najeriya, kuma hakan zai sa su ƙi yarda da duk wani sakamakon zaɓe da Amupitan ɗin zai gabatar.

Ya ce hakan zai iya sa a iya samun ƙaurace wa zaɓe ko kuma a riƙa nuna wa juna yatsa bayan sakamakon zaɓen idan har ba a canza shugaban Inec ɗin ba.

"Ƴan Najeriya da dama suna ganin ba zai iya adalci ba, ba zai yi gaskiya ba..., duka waɗannan al'amura ne da suke daɗa sa ƴan Najeriya su nesanta tunanin za a yi gaskiya da adalci," in ji shi.

"Idan har aka ci gaba aka yi wannan zaɓe, haƙiƙa za a yi shi a cikin rauni da rashin yarda da rashin jin daɗi, kuma jama'a ƴan ƙasa da dama duk yadda aka yi zaɓen nan, ba za su iya yarda an yi shi kan gaskiya da adalci ba".

Ya ce matakin da ya fi tasiri a zukatan ƴan Najeriya shi ne batun addini, musamman yadda ake zargin sa da nuna ƙiyayyarsa ƙarara ga wani bangare na al’umma.

Masana kimiyyar siyasa irin su Farfesa Abubakar Kari na jami'ar Abuja, na ganin irin waɗannan zarge-zarge na iya taɓa ƙimar hukumar zaɓen.

"Zarge-zargen sun yi babban tabo ga hukumar da kuma shi kansa Amupitan ɗin, amma wannan ba yana nufin zarge-zargen da ake masa gaskiya ne ko ba gaskiya ba".

Farfesa Kari ya ƙara da cewa ko dai shugaba Tinubu ya cire shi a muƙamin ko kuma ya yi murabus ko kuma a ci gaba kiraye-kirayen sauke shi har a shiga zaɓe.

"Kuma hakan ba zai yi wa dimokraɗiyya kyau ba," in ji shi.

INEC ta musanta zargin alaƙar shugabanta da APC

Amupitan

Asalin hoton, X/Inec

Sai dai duk da waɗannan zarge-zarge, hukumar INEC ta yi kira ga 'yan Najeriya su yi watsi da "ƙagaggun labaran ƙarya da ake yaɗawa" game da shugaban hukumar Farfesa Amupitan.

Hukumar ta ce zargin baki ɗayansa "ƙarya ne" kuma tsararren abu ne. "Domin kawar da shakku a zukatan mutane, shuganam INEC ba shi da wani shafi a X.

"Babu wani lokacin da ya taɓa fitowa ya yi sharhi kan siyasar jam'iyyun," in ji sanarwar.

Bayan nan, INEC ta ce tana sane da laifukan intanet da mutane suke aikatawa, suna amfani da hoton Amupitan suna samar da wani shafi domin ɓata masa suna, INEC ta ce tuni ta miƙa wannan ƙorafi ga hukumomin da suka dace domin ɗaukar mataki.

Shugabannin INEC daga 1999-2026

Shugabanni shida ne suka jagoranci hukumar zaɓen Najeriya Inec tun daga komawar ƙasar tsarin dimokraɗiyya kuma sun fuskanci ƙalubale daban-daban yayin gudanar da zaɓuka a fadin kasar.

Ga jerin shugabannin hukumar a Najeriya tun bayan komawar kasar mulkin dimokuraɗiyya a shekarar 1999:

  • Ephraim Akpata (1998 – 2000): Shi ne ya jagoranci INEC lokacin zaben 1999, wanda ya kawo gwamnatin farar hula ta farko bayan mulkin soja.
  • Dr. Abel Guobadia (2000 – 2005): Ya karɓi ragamar hukumar bayan rasuwar Akpata.
  • Farfesa Maurice Iwu (2005 – 2010): Ya jagoranci zaben shekarar 2007.
  • Farfesa Attahiru Jega (2010 – 2015): Ya yi suna bayan zaɓukan da suka kayar da Buhari da kuma nasararsa a 2015 da kuma yadda ya gabatar da na'urar tantance masu kada kuri'a (card reader) a zaɓen.
  • Farfesa Mahmood Yakubu (2015 – 2025): Ya jagoranci hukumar har zuwa gudanar da zabukan 2019 da 2023 da ya kawo Bola Ahmed Tinubu.
  • Farfesa Joash Ojo Amupitan (2025 zuwa yanzu) Tinubu ya naɗa shi a matsayin shugaban hukumar INEC bayan ƙarewar wa'adin Farfesa Yakubu.