Jerin jihohi da biranen Najeriya da ambaliya za ta shafa a 2026

Asalin hoton, Getty Images
Ministan albarkatun ruwa da tsafta Farfesa Joseph Terlumun Utsev, ya yi gargadi cewa garuruwa 14,118 a kananan hukumomi 266 a jihohi 33 hadi da Abuja na cikin hadarin fuskantar ambaliya a wannan shekara ta 2026.
Ministan ya bayyana hakan ne, a Fadar Shugaban Kasa a Abuja, ranar Laraba, yayin gabatar da rahoton shekara-shekara na bana a kan yanayin da za a iya fuskanta na ambaliya.
Taron ya gabatar hasashe da ke cike da shedu kan yuwuwar ambaliya, wanda hakan ya ba wa gwamnati da masu ruwa da tsaki da hukumomi da gwamnatocin jihohi da na kananan hukumomi da saurn al'umma domin su shirya tunkarar daminar bana kan yadda ambaliyar za ta iya kasancewa.
Matakan da za a dauka za su zama na kandagarkin samar da bayanai da wuri da kare rayukan da harkokin da jama'a ke rayuwa da su da kare kayayyakin amfanin jama'a da kuma rage illar da ambaliyar za ta iya yi ga harkokin tattalin arziki.
Jihihi 33 da za su fuskanci babbar ambaliya

Asalin hoton, Getty Images
Ministan ya bayyana jihohin da ke fusknatar hadarin na ambaliya a bana inda suka hada da
- Abia
- Adamawa
- Anambra
- Bauchi
- Bayelsa
- Benue
- Borno
- Cross River
- Delta
- Ebonyi
- Edo
- Enugu
- Gombe
- Imo
- Jigawa
- Kaduna
- Kano
- Kebbi
- Kogi
- Kwara
- Lagos
- Nasarawa
- Niger
- Ogun
- Ondo
- Osun
- Oyo
- Plateau
- Rivers
- Sokoto
- Taraba
- Yobe
- Zamfara
- Abuja
Bayanin da ministan ya gabatar ya nuna cewa garuruwa 15,597 a kananan hukumomi 405 a jihohi 35 in banda Jihar Ekiti za su fuskanci matsakaiciyar ambaliya.
Jihohi 24 da za su fuskanci ƙaramar ambaliya

Asalin hoton, Getty Images
Ministan ya ce za a fuskanci ambaliya ƙarama a garuruwa 923 a ƙananan hukumomi 77 a jihohi 24.
- Adamawa
- Anambra
- Bauchi
- Bayelsa
- Benue
- Borno
- Cross River
- Delta
- Ebonyi
- Edo
- Jigawa
- Kaduna
- Kano
- Kebbi
- Kogi
- Nasarawa
- Niger
- Ogun
- Ondo
- Osun
- Oyo
- Sokoto
- Taraba
- Zamfara
Farfesa Utsev ya kara da cewa ana sa ran ambaliyar za ta yi tsanani ne a tsakanin watan nan na Afirilu da Nuwamba, inda ya kara da cewa za ta shafi aikin gona da dabbobi da kayayyakin jin dadin rayuwa na jama'a da muhalli da kuma hanyoyin rayuwar jama'a.
Ya ce, wannan shekarar garuruwa 9,021 a kananan hukumomi 188 a fadin Najeriya, suna cikin hadarin mummunar ambaliya a watan Afirilu da Mayu da Yuni, yayin da garuruwa 14,158 a kananan hukumomi 263 a watan Yuli da Agusta da kuma Satumba za su fuskanci ambaliyar mai girma.
Sai kuma cikin watan Oktoba da Nuwambainda garuruwa 11,575 a kananan hukumomi 224 za su kasance cikin hadarin gamuwa da mummunar ambaliyar.
Biranen da za a yi ambaliya

Asalin hoton, Getty Images
Ministan ya kuma bayyana cewa za a iya gamuwa da matsakaiciyar ambaliya a tsakanin watan Afirilu da Nuwamba, inda ake sa ran za ta shafi garuruwa 8,225 a kananan hukumomi 228.
Haka kuma ya ce za a iya samun ambaliya ta lokaci daya a manyan biranen kasar saboda tsananin ruwan sama da rashin kulawa da cibiyoyin ruwa da rashin gyara magudanun ruwa da hanyoyin ruwa da kuma rashin kayayyaki da za su iya jure wa ambaliya.
Biranen da za su iya gamuwa da wannan ambaliya sun hada da:
- Abakaliki
- Abeokuta
- Abuja
- Asaba
- Benin City
- Birnin–Kebbi
- Calabar
- Ibadan
- Kaduna
- Kano
- Lagos
- Makurdi
- Nguru
- Onitsha
- Oshogbo
- Port Harcourt
- Sokoto
- Warri
- Yola
Jihohin da ke bakin teku

Asalin hoton, Getty Images
Haka su ma yankunan da ke gabar teku za su iya fuskantar ambaliyar da suka haɗa da:
- Bayelsa
- Cross River
- Delta
- Lagos
- Ogun
- Rivers
- Ondo.
Ambaliayr za ta shafi harkokin kamun kifi da dazuka inda dabbobin dawa suke da kuma hanoyoyin da ruwa ke bi.
Ministan albarkatun ruwan ya yi kira ga gwamnatocin jihohi da kananan hukumomi da hukumomin bayar da agajin gaggawa da manoma da shugabannin al'umma da su dauki matakan gaggawa da suka dace domin shirya wa ambaliyar.











