Lokuta biyar da Boko Haram ta 'kashe' manyan sojojin Najeriya a 2026

Asalin hoton, Nigerian Armed Forces
Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da mutuwar wani babban kwamandanta da ke jagorantar sansaninta na Munguno a jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya, a wani harin Boko Haram.
Cikin wata sanarwa da kakakin rundunar Operation Hadin Kai, mai yaƙi da Boko Haram, Kanal Sani Uba ya fitar ya ce kwamandan - wanda bai a ambaci sunansa ba - ya gamu da ajalin nasa ne bayan da motar da yake ciki ta taka wani abin fashewar da mayaƙan suka dasa.
Sojojin sun kuma nuna alhininsu kan rasuwar babban jami'in da kuma sojojin da ke tare da shi a lokacin.
Mutuwar babban jami'in sojin na zuwa ne ƙasa da mako ɗaya bayan rahotannin da suka ce mayaƙan na Boko Haram sun kashe jagoran sansanin sojin Najeriya da ke garin Benisheikh, Brigediya Janar OO Braimah, a wani harin cikin dare da suka kai sansanin.
Ba wannan ne karon farko da mayaƙan Boko Haram ke kai hare-hare kan manyan sojojin ƙasar da ke yaƙin da ƙungiyar a jihar Borno ba.
Ta hanyar bibiyar rahotonnin wasu jaridun ƙasar da sanarwar sojojin ke fitarwa, mun duba jagororin sansanonin soji biyar da aka kashe a hare-haren Boko Haram a 2026.
Shugaban sansanin Damasak - Janairu
A cikin watan Janairun wannan shekara ne mayaƙan ISWAP suka kai hari sansanonin sojin Damasak da ke ƙaramar hukumar Mobbar, tare da kashe babban jami'in sojin sansanin mai muƙamin Manjo.
A lokacin harin Jaridar Vanguard a ƙasar ta ce babban sojin wanda ke jagorantar sansanin na kan aikin sintiri ne a ƙafa tare da sojojinsa kusan 30, lokacin da suka ci karo da maharan waɗanda suka dasa musu abubuwan fashewar.
Rahotonni a lokacin sun ce harin ya tilasta wa sojojin barin sansanonin kodayake daga baya wasu sun koma.
Shugaban sansanin Kukawa - Maris
A farkon watan Maris ne kuma mayaƙan Boko Haram suka ƙaddamar da wani hari kan sansanin soji Kukawa da ke jihar ta Borno.
A lokacin aukuwar harin Jaridar Daily Trust ta bayar da rahoton cewa maharan sun ƙaddamar da harin da tsakar dare tare da kashe jagoran sansanin mai suna Laftanal Kanar Umar Faruq.
Bayanai sun ce a lokacin harin mayaƙan na Boko Haram sun ƙona motocin sojoji masu yawa tare da sace harsasai.
"Ba zan iya tabbatar da adadin sojojin da suka mutu ba, amma dai har da jagoran sansanin'', kamar yadda wata majiyar tsaro ta shaida wa jaridar a lokacin
Konduga - Maris
Maris ya kasance watan da mayaƙan Boko Haram, musamman tsagin ISWAP suka zafafa ƙaddamar da hare-hare kan sansanonin soji a Borno.
Cikin wani bidiyo da ƙungiyar wallafa a kafar yaɗa labaranta ta Amaq ta nuna yadda ta kai hare-hare tare da ƙona motocin soji a sansanoni daban-daban a jihar Borno.
Cikin sansanonin da aka kai har da sansanin bataliya ta 222 da ke Konduga, tare da kashe jagoran sansanin mai suna Laftanal Kanal S.I Iliyasu, kamar yadda Jaridar Daily Trust ta ruwaito a lokacin.
Mayanti - Maris
Baya ga Konduga, wani sansanin sojin da mayaƙan Boko Haram suka kai wa hari shi ne sansanin Mayanti da ke ƙaramar hukumar Bama.
A lokacin harin rahotonni sun ce mayaƙan na sunkashe jagoran sansanin mai suna Manjo U.I Mairiga.
Daga bidiyon da ISWAP ta fitar ta yi iƙirarin kai harin cikin dare tare da kashe sojoji masu yawa.
Benisheikh - Afrilu
A farkon wannan wata na Afrilu ne kuma mayaƙan Boko Haram suka kai hari sansanonin soji na Benisheikh da inda suka yi arangama da sojoji.
Bayanai sun nuna cewa mayaƙan sun auka wa sansanin cikin dare tare da buɗe wuta kan sojojin, lamarin da ya yi sanadiyyar kisan babban kwamandan rundunar mai suna Birgediya janar OO Braimah da wasu sojoji.
Cikin wata sanarwa da shalkwatar tsaron Najeriya ta fitar, ta ce sojojin sun samu nasarar daƙile harin bayan da suka mayar da martani da cikin jajircewa da ƙwarewa da kuma ƙarfin makamai.
Tuni dai shugaban Najeriya ya aike da saƙon jaje ga iyalan sojojin da suka mutu sakamakon a harin.
Monguno - Afrilu
A ƴan kwanakin nan ne kuma jagoran sansanin soji da ke Munguno ya rasa ransa sakamakon taka abin fashewa da motarsa ta yi bayan harin Boko Haram.
Rundunar sojin ƙasar ta tabbatar da mutuwar babban jami'in sojin, cikin wata sanar da ta fitar.
''Dakarun ƙaramar rundunar ta 3 na Rundunar Hadin Kai sun fuskanci harin ƴanta'adda a Charlie 13 da ke Monguno, inda aka yi musayar wuta tsakaninsu da dakarunmu, inda suka yi nasarar korar mayaƙan da yankin'', in ji sanarwar.
''Sai dai abin takaici babban jami'in sojin sansanin, wanda ya yi niyyar zuwa wurin da aka yiu gumurzun domin gane wa idanunsa, ya gamu da ajalisan bayan da motar da wani abin fashewa da mayaƙan suka dasa, lamarin da ya yi sanadiyyar rasa ransa tare da wasu sojoji shida da ke tare da shi'', kamar yadda sanarwar sojojin ta yi ƙarin haske.
Tinubu ya gana da manyan hafsoshin tsaro
A ranar Litinin ne shugaban Najeriya Bola Tinubu ya yi ganwar sirri da manyan hafsoshin tsaron ƙasar a fadarsa.
Cikin waɗanda suka halarci ganawar sun haɗa da babban hafsan tsaron ƙasar, da babban hafsa sojin ƙasa da na sama da na ruwa da shugaban hukumar tattara bayanan sirri da daraktan hukumar tsaron farin kaya da kuma babban sifeton ƴan sandan ƙasar.
Bayanai na nuna cewa ganawar ba ta rasa nasaba da ƙaruwar matsalar tsaron ƙasar, da kuma tattauna sabbin matakai.
Ganawar na zuwa ne jim kaɗan bayan wata ganawar da musamman da babban hafsan tsaron ƙasar da kuma takwaransa na Faransa, kamar yadda jarudun ƙasar suka ambato.











