Mene ne sabon shirin tsaron ƙasa da Tinubu zai samar a Najeriya?

Tinubu

Asalin hoton, Fadar Shugaban Najeriya

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 4

A daidai lokacin da matsalar tsaro ke ci gaba da addabar sassa daban-daban na Najeriya, gwamnatin shugaban ƙasar Bola Ahmed Tinubu ta fitar da wani sabon shirin tsaro na shekara biyar, wanda ta ce zai zama jagora wajen tunkarar barazanar da ƙasar ke fuskanta.

Shirin na zuwa ne a yayin da ƴanƙasar ke ƙara nuna damuwa kan hare-haren ƴan ta'adda da satar mutane da rikice-rikicen manoma da makiyaya da kuma ayyukan masu garkuwa da mutane.

Sai dai tambayar da ƴanƙasar da dama ke yi ita ce ko wannan sabon tsarin zai iya kawo ƙarshen matsalar tsaro cikin shekaru biyar masu zuwa?

Masana harkokin tsaro na cewa nasarar irin wannan shiri ba ta ta'allaka ga rubuta manufofi kaɗai ba, illa ga yadda za a aiwatar da su, samar da isassun kuɗaɗe, inganta ayyukan hukumomin tsaro da kuma magance tushen matsalolin da ke haddasa rashin tsaro.

Cikin wannan muƙala mun tuntuɓi masana tsaro don jin da abubuwan da suka kama su kasance cikin shirin idan ana son a samu ingantaccen sakamako cikin shekaru biyar masu zuwa.

Me shirin zai ƙunsa?

Cikin wata sanarwa da gwamnatin Najeriya ta fitar kan sabon tsarin, ta ce shirin da aka ƙiyasta aiwatar da shi cikin shekara biyar zai mayar da hankali kan gano manyan barazanar tsaro da Najeriya ke fuskanta.

Da kuma tantance waɗanda suka fi buƙatar matakan gaggawa, da kuma tsara hanyoyin magance su cikin tsari mai ɗorewa.

''A ƙarƙashin shirin, gwamnati za ta gudanar da cikakken nazari kan matsalolin tsaro daban-daban da suka haɗa da ta'addanci da garkuwa da mutane domin neman kuɗin fansa da fashi da makami da rikice-rikicen cikin gida da sauran barazanar da ke shafar zaman lafiya a ƙasar'', kamar yadda sanarwar ta yi ƙarin haske.

Haka kuma, shirin zai fayyace irin sojoji da jami'an tsaro da kayan aiki da fasahohi da bayanan leƙen asiri da ake buƙata domin tunkarar barazanar tsaro a sassa daban-daban na ƙasar.

Sanarwar ta kuma ce shirin zai gano giɓin ta fannin kayan aiki da dabarun hukumomin tsaro, tare da tsara yadda za a cike giɓin a cikin shekara biyar ɗin.

Wani muhimmin ɓangare na shirin shi ne ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin sojoji da ƴan sanda da hukumomin leƙen asiri da sauran hukumomin tsaro, domin su yi aiki tare bisa manufa guda maimakon yadda ake zargin suna gudanar da ayyuka daban-daban a wasu lokuta.

Haka kuma, shirin zai zama jagora wajen tsara kasafin kuɗin tsaro da sayen kayan aiki na shekaru masu zuwa, domin tabbatar da cewa ana karkatar da kuɗaɗen zuwa wuraren da aka fi buƙata.

Gwamnati na fatan cewa wannan tsari zai taimaka wajen inganta yaƙi da rashin tsaro da kuma samar da ingantaccen tsarin samar da zaman lafiya.

Su wane ne jagororin shirin?

Tinubu da babban hafsan tsaron Najeriya

Asalin hoton, Fadar Shugaban Najeriya

Fadar shugaban ƙasar ta ce wasu fitattun masu ruwa da tsaki kan harkar tsaron ƙasar ne za su tafiyar da shirin ƙarƙashin jagorancin mai taimaka wa shugaban ƙasar na musamman kan harkokin tsaron cikin gida, Major General Adeyinka A. Famadewa, mai ritaya.

Mambobin kwamitin sun haɗa da mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, will coordinate and provide secretariat support for the 11-man committee the, Malam Nuhu Ribadu, da ministan tsaron ƙasar Janar Christopher Musa mai ritaya.

Sauran mambobin sun haɗa da

  • Ƙaramin ministan tsaro, Bello Muhammad Matawalle
  • Babban hafsan tsaron ƙasar Janar Olufemi Oluyede
  • Babban hafsan sojin ƙasa na Najeriya, Laftanar Janar Waidi Shaibu
  • Babban hafsan sojin saman ƙasar, Air Marshal Sunday Kelvin Aneke
  • Babban hafsan sojin ruwan ƙasar, Vice Admiral Idi Abbas.
  • Daraktan tsaro na farin kaya, Tosin Ajayi
  • Daraktan hukumar leƙen asiri, Ambassador Muhammed Muhammed

Me ya kamata shirin ya bai wa fifiko?

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Dr Kabiru Adamu, shugaban kamfanin Beacon Security mai nazarin tsaro a yankin Sahel ya ce akwai abubuwan da ya kamata shirin ya bai wa fifiko domin samun nasara.

A hirasa da BBC masanin tsaron ya ce samar da shirin abu ne mai muhimmanci, da ke nuna cewa shugaban ƙasar ba ya gamsuwa da matakan da ake ɗauka don magance matsalar tsaron ƙasar.

Ya ce babban abin da ya kamata shirin ya ƙunsa shi ne ƙarfafa hanyoyin gano maƙasudin matsalolin tsaron da ke addabar ƙasar.

Masanin tsaron ya ci gaba da cewa yana da kyau shirin ya kuma mayar da hanakali wajen bibiya da kuma nazarin tsaron ta hanyar la'akari da lokacin da ake ciki.

''Sannan akwai buƙatar kula da sojojin da kayan aikinsu da yadda suke gudanar da aikinsu, sai kuma inganta hanyoyin tattara bayanan sirri'', kamar yadda ya yi ƙarin haske.

Ya ci gaba da cewa akwai buƙatar yin sauye-sauye a fannin tsaron ƙasar ta hanyar shigar da abubuwa na zamani da ƙoƙarin haɗa kan jami'an tsaron ƙasar don yin aiki tare.

Kwalliya za ta biya kuɗin sabulu?

Masanin tsaron ya ce idan har gwamnati ta mayar da hankali wajen aiwatar da wanann shiri yadda ya kamata, kuma ta samu hadin kai daga ƴan ƙasar akwai alamun samun gagarumar raguwar matsalar.

Sai dai ya ce sai gwamnatin tarayya ta ɗauki wasu ƙarin matakan tabbatar da hakan.

"Yana da kyau kuma gwamnatin tarayya ta saka gwamnatocin jihohi a cikin wannan tsarin don yin aiki tare'', kamar yadda ya bayyana.

Masanin tsaron ya yi kira ga gwamnati ta haɗa hannu da duk masu ruwa da tsaki, kama daga shugabannin al'umma da jagororin addinai da masu bincike da ƴanjarida domin samun nasarar.

Daga ƙarshe ya sake jaddada buƙatar bibiya da sanya idanu daga gwamnati da kuma ladabtar da waɗanda aka samu da gazawa.