Me ya sa Tinubu da Atiku ke cacar baki kan tallafin man fetur?

Asalin hoton, FB/Multiple
- Marubuci, Rabiatu Kabir Runka
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Journalist
- Aiko rahoto daga, BBC Abuja
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 3
A Najeriya wata sabuwar cacar baki ce ta kaure tsakanin tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar da kuma shugaban kasar Bola Tinubu.
Cacar bakin ta kaure ne bayan da ɗan takarar shugaban ƙasa a jam'iyar ADCn yace zai mayar da tallafin man fetur idan ya ci zaɓe a 2027.
To amma cikin wani martani da Shugaba Tinubu ya yi ga kalaman, ya ce soki Atikun da cewa bai fahimci tsarin tattalin arziki ba.
''Waɗannan kalamai na nuna tsantsar jahiltar fannin shugabanci da tsarin tattalin arziki'', kamar yadda ya bayyana.
Yayin da yake zantawa da tawagar gwamnan Osun a ofishinsa, Shugaba Tinubu ya ce kafin hawansa mulki kimanin jihohin ƙasar 27 ba sa iya biyan alabashin ma'aikantsu, balle kuɗin ƴanfansho.
''Jihohin da dama kan zo suna roƙon gwamnatin tarayya, saboda ba sa iya yin komai, saboda rashin kuɗi'',in ji Shugaba Tinubu.
Shugaba Tinubu ya sha bayyana cewa ya ƙara yawan kason da gwamnatin tarayya ke bai wa jihohi.
Ko a cikin makon nan ne dai minisitan kuɗin ƙasar, Taiwo Oyedele ya ce cikin abubuwan da ake yi da kuɗin tallafin har da raba wa jihohi da ƙananan hukumomi.
Wane iƙirari Atiku ya yi ?
Atiku Abubakar ya yi alƙawarin cewa zai mayar da tallafin man fetur a ƙasar idan ya hau kan mulki a shekarar ta 2027.
A tattaunawar da ya yi da kafafen yaɗa labarai a jiya Laraba, Atiku ya ce cire tallafin bai yi amfani ba kasancewar "ba a ga abin da aka yi da kuɗin ba".
"Ina kuɗin suke? Ya kamata a ce an yi amfani da su wajen maganin talauci da rashin zuwa makaranta, da sauran su".
A lokacin da aka tambaye shi ko zai mayar da tallafin man fetur ɗin idan ya ci zaɓe a 2027, sai ya ce: "Zan mayar, kuma duk wani wanda ya saci kudin zai dawo da su".
Gabanin babban zaɓen 2023, Atiku Abubakar ya taɓa yin alƙawarin cewa zai sayar da matatun man fetur na ƙasar
Martanin fadar shugaban ƙasar
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Abdul'aziz Abdul'aziz ɗaya daga cikin masu magana da yawun shugaban Najeriya ya ce a lokacin da yaƙin neman zaɓen 2023 Atiku ya yi batun cire tallafi har ma da sayar da matatun mai da kamfanin mai na Najeriya.
"To menene ya canza mutumin da yake kan gaba wajen iƙirarin cire tallafin mai, shine zai zo yanzu yana wadannan kalamai, har ma yana cewa zai soke wannan tsari, bayan kuma shine kan gaba wajen yin wadannan maganganu a baya ." cewar Abdul'aziz
Fadar shugaban Najeriyar ta yi iƙirarin cewa tsarin cin hanci da rashawar dake cikin tsarin tallafin man fetur ba ƙarami bane, "kuma yanzu duk an daina sakamakon an rufe wannan tagar ta yin wannan abubuwan da mutane suka saba na yin cucuwa.
Abdul'aziz ya buƙaci tsohon mataimakin shugaban Najeriyar Atiku da ya taimaka ya basu sunayen mutanen da suka sace kudin tallafin kamar yadda ya yi iƙirari.
A ranar 29 ga watan Mayun 2023, Tinubu ya sanar a cikin jawabinsa na karɓar mulki cewa "tallafi ya ƙare", lamarin da ya taka rawa wajen tashin farashin litar man fetur da hauhawar farashi a kusan kowane fanni na ƙasar.
Sai dai an yi ta cece-ku-ce kan rashin ganin alfanun hakan bayan da aka samu ƙarin tsadar rayuwa a ƙasar.
Ko ƴan Najeriya sun gani a ƙasa?
Cire tallafin man fetur na daga cikin manyan matakan da gwamnatin Bola Tinubu ta ɗauka waɗanda suka kawo gagarumin sauyi a tattalin arziƙin ƙasar.
Farfesa Ahmed Adamu, masani kan harkokin man fetur kuma malami a jami'ar Philomath University da ke Abuja, babban birnin Najeriya ya ce rashin ganin amfanin cire tallafin man fetur a Najeriya na da alaƙa da farashin dalar Amurka.
A cewarsa darajar dalar Amurka ta nunka bayan cire tallafin man fetur, wannan ya sanya alfanun da ake tunanin za a samu daga ƙarin kuɗaɗen da gwamnatin Najeriya ta samu daga cire tallafi bai yiwu ba.
Masanin tattalin arziƙi Dr Shamsudden Muhammad ya ce "ba a ga wani alfanu da cire tallafin ya kawo wa Najeriya ba ya zuwa yanzu, in baya ga biyan buƙatun wasu ƙungiyoyin duniya da wasu ƙasashen duniya da suka matsa a cire tallafin.
Ya bayyana cewa irin waɗannan hukumomi su ne Hukumar Lamuni ta Duniya (IMF) da kuma Bankin Duniya (World Bank).












