Makaman yaƙi 9 da za su sauya fasalin yaƙe-yaƙe a duniya

Asalin hoton, US Air Force
Makaman yaƙi na fuskantar gagarumin sauyi tun bayan fara ƙera makaman nukiliya. Tsawon kusan ƙarni guda, ƙarfin sojoji ya dogara ne kan ƙarfin makamai, abubuwan fashewa, manyan makamai masu linzami masu dogon zango da jiragen yaƙi masu saurin gaske.
Yanzu salon yaƙi na ƙara karkata zuwa makaman da ba a iya ganinsu cikin sauƙi, waɗanda ke amfani da fasahar AI, fasahar laturoni da kuma tsaron sararin samaniya.
Yayin da ƙasashe ke binciken samar da sabbin makamai bisa fasahohin da ba a iya gani ko gano su cikin sauƙi, yadda aka saba tsarin yaƙi na bindiga da sojoji na iya sauyawa.
Ga wasu daga cikin makamai tara da ake ganin za su taka muhimmiyar rawa a yaƙe-yaƙen nan gaba:
1. Makamin hasken Laser

Asalin hoton, shutterstock
Wannan makami na amfani da haske mai ƙarfi ne wajen harba shi kuma yana iya ƙona ko lalata makaman abokan gaba, kamar jiragen sama, motoci, na'urorin gano makamai da kuma abubuwan fashewa.
Ɗaya daga cikin abubuwan da suka bambanta shi da sauran makamai shi ne ƙarancin kuɗin da ake kashewa wajen amfani da shi.
Hasken makamin ba ya ƙarewa matuƙar akwai isasshen makamashi da zai ci gaba da tafiyar da shi.
An ƙera irin wannan makami musamman domin kare sararin samaniya daga ƙananan jirage marasa matuƙa, waɗanda ake iya samarwa cikin sauƙi kuma da ƙarancin kuɗi.
2. Tururin maganaɗisun wutar lantarki

Asalin hoton, Ciidanka Cirka ee Maraykanka
Waɗannan makamai suna amfani da maganaɗisun lantarki (electromagnetic waves) ko na rediyo masu ƙarfi wajen lalata na'urorin lantarki. Ƙarfinsu na iya kai wa na tururin na'urar ɗumama girki kusan sau 150,000.
Ba sa kai hari ga jirgi mara matuƙi amma ana amfani da su wajen aika waɗannan maganaɗisu masu ƙarfi zuwa wani yanki domin lalata na'urorin jirage marasa matuƙi da dama a lokaci guda.
3. Ƙirƙirarriyar Basirar AI

Asalin hoton, Getty Images
Waɗannan makamai ne masu iya kare kai ta hanyar amfani da fasahar AI wajen gano barazana da bibiyarta har zuwa inda take da kuma kai mata hari.
Maimakon mutum ya riƙa sarrafa makamin da hannu, tsarin na iya amfani da bayanan da na'urorinsa suka tattara wajen yanke matakan da suka dace cikin sauri.
Duk da cewa mutane za su ci gaba da sarrafa wasu daga cikin waɗannan makamai, amfani da su masu cin gashin kansu, ana ta muhawara da tambayoyi kan yadda za a tabbatar da cewa mutum na da cikakken iko kan shawarar kai hari.
4. Makamin sauti

Asalin hoton, Alamy
Wannan makami na amfani da na'urorin sauti wajen haddasa tangarɗa, ruɗani ko kuma lalata dodon kunne.
Wannan makamin ya bambanta da sautin lasifika masu ƙarfi da ake ɗora wa manyan motoci, waɗanda ake amfani da su wajen tarwatsa taron jama'a ko dakile masu fashin teku.
5. Makaman masu cin nisan zango

Asalin hoton, Alamy
Waɗannan makamai ne da ke amfani da makamai masu linzami waɗanda ake harbawa cikin tsananin sauri.
Makaman na amfani da maganaɗisu da wutar lantarki maimakon garin bindiga ko abubuwan fashewa na sinadarai wajen harba makaman.
Saboda tsananin saurinsu, suna da wahalar ganowa ko tarewa kafin su kai ga inda aka nufa.
6. Hasken zafi

Asalin hoton, Getty Images
Wannan makami ne na makamashi da aka ƙera domin kai hari ga mutane ta hanyar haska shi.
Daga cikinsa akwai zafi wanda zai iya ƙona fata tare da haddasa zafi mai tsanani ba tare da barin tabo na dindindin ba.
An kuma ƙera wasu nau'ikansa domin dakatar da abokan gaba ta hanyar kashe musu gani ta ɗan lokaci.
7. Makaman sararin samaniya

Asalin hoton, Getty Images
Waɗannan makamai ne da ake aika su zuwa sararin samaniya domin kai hare-hare kan wuraren da ke doron ƙasa.
Ana aika kan makamin zuwa sararin samaniya kafin ya dawo ƙasa domin kai hari, da kuma zama makaman kariyaa.
Masana na ganin irin waɗannan makamai na iya kauce wa wasu tsarin kariyar makamai masu linzami da ƙasashe ke amfani da su.
8. Jiragen yaƙi da jirage marasa matuƙa

Asalin hoton, Getty Images
Sabbin jiragen yaƙi masu amfani da basirar AI kamar YFQ-42A da YFQ-44A na rundunar sojin saman Amurka an ƙera su ne domin su yi aiki ba tare da matuƙa ba.
Za su iya yin aiki tare da jiragen yaƙi masu matuƙa ko kuma su gudanar da ayyuka da kansu.
Masu haɓaka fasahar na cewa AI ta fara nuna cewa za ta iya yin wasu ayyukan yaƙin sama cikin sauri da inganci fiye da yadda ɗan adam ke yi.
Makaman nuna basirar ƙwaƙwalwa

Asalin hoton, Getty Images
Waɗannan makamai ne da har yanzu suke matakin gwaji, waɗanda aka ƙera domin kawo cikas ga basirar ƙwaƙwalwa ko wasu gabobin aiki da kuma saurare ga abokan gaba.
Ana tunanin suna amfani da makamashi, na'urorin sauti ko wasu nau'ikan fasaha.
Ana ta hasashe da nuna yadda makamin zai iya kasancewa a fina-finar da tatsuniyoyi, amma har yanzu babu wata hujja tabbatacciya da ke nuna cewa an samar da irin wannan makami ko yana aiki yadda ake hasashe.











