Ko Iran za ta iya kai wa ƙasashen Turai hari?

..

Asalin hoton, Reuters

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 4

Iran na iya kai hare-hare kan sansanonin sojin Amurka da ke Turai idan Donald Trump ya sake kai wa Iran hari, a cewar jaridar Financial Times, wadda ta ce ta samu wannan bayani daga majiyoyin da ke kusa da hukumomin Iran.

Idan hakan ta faru, zai iya faɗaɗa girman yaƙin sosai, domin rikicin zai iya wuce iyakokin Gabas ta Tsakiya ya bazu zuwa wasu yankuna.

A lokaci guda kuma, Iran na fuskantar wata matsala daban. A cewar CNN, Tehran na ci gaba da rasa cikakken iko a kan Mashigar Hormuz , ɗaya daga cikin muhimman hanyoyin ruwa da ake bi wajen jigilar man fetur da samar da shi a duniya.

Mashigar Hormuz na da matuƙar muhimmanci ga kasuwannin makamashi na duniya, saboda babban kaso na man fetur da iskar gas da ake fitarwa daga ƙasashen Gulf na ratsawa ta wannan hanya.

Barazanar Iran ga Turai

A cewar jaridar Financial Times, jami'an tsaron Iran na nazarin yiwuwar kai hare-hare kan wuraren da Amurka ke da muradunta a kudu maso gabashin Turai.

Daga cikin wuraren da ake ganin za su iya zama ababan kai wa hari akwai sansanin jiragen sama na Bezmer da ke Bulgaria.

Jaridar ta ce majiyoyinta sun bayyana cewa a watan da ya gabata, Amurka ta samu izinin amfani da sansanin domin sake cika man jiragen sama. Wani wurin da ake ganin Iran din za ta iya kai wa hari shi ne Cyprus.

A watan Maris, an kai hari da jirgi marar matuƙi kan sansanin sojin Birtaniya na Akrotiri da ke tsibirin Cyprus.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

A lokacin, jami'an kasashen Yamma sun yi hasashen cewa Iran na iya kasancewa tana da hannu a harin. Sai dai sun ce mai yiwuwa an harbo jirgin ne daga ƙungiyoyin da ke da alaƙa da Tehran maimakon a turo shi kai tsaye daga Iran.

Haka kuma, jami'an tsaron Iran na nazarin yiwuwar kai hare-hare kan kebul ɗin intanet da ke ƙarƙashin teku a yankin Mashigar Hormuz idan rikici ya ƙara tsananta.

Majiyoyin da suka zanta da Financial Times sun ce tsaurin matsayar da Tehran ke nunawa a yanzu na da alaƙa da sauyin fahimta a tsakanin shugabannin Iran.

Ana ƙara samun masu ra'ayin cewa wani sabon yaƙi tsakanin Iran da maƙiyanta ba abin mamaki ba ne, sai dai tambayar ita ce yaushe zai ɓarke.

A halin yanzu kuma, tattaunawar dawo da cikakkiyar 'yancin zirga-zirgar jiragen ruwa a Mashigar Hormuz ta tsaya cik.

A ranar Talata, Donald Trump ya ce a halin yanzu babu wata tattaunawa ko wata hulɗa da aka shirya da Tehran.

Wakilan Rundunar Kare Juyin Juya Halin Musulunci ta Iran (IRGC) da sauran manyan hafsoshin soja suna gargadin cewa idan wani sabon babban yaƙi ya ɓarke, Iran na iya sauya dabarunta na baya.

A baya, Tehran ta fi mayar da hankali wajen kai hare-hare kan sansanonin sojin Amurka, makamashi da sauran muhimman wurare a Gabas ta Tsakiya.

Amma yanzu, wasu wurare da ke wajen wannan yanki ma na iya zama ababan kai wa hari.

Ɗaya daga cikin waɗanda suka yi magana da Financial Times ya ce idan Amurka ta ɗauki matakin da Iran ke gani a matsayin tsokana ko hari to komai zai iya faruwa.

"Idan Amurka ta tsallake iyaka, Iran za ta kare kanta ko ta halin ƙaƙa. Za ta fita daga wannan yanki ta kuma kai hare-hare har zuwa Turai."

Iran ta taɓa gargaɗin Birtaniya a baya cewa sansanoninta na soja za su iya zama ababan farmaka.

A watan da ya gabata, Rundunar IRGC ta bayyana cewa "Duk wani sansani da aka yi amfani da shi wajen kai hari kan Iran za a ɗauke shi a matsayin halastaccen hari."

Yaya girman barazanar nan take?

..

Asalin hoton, Reuters

Siddharth Kaushal, wani masani a cibiyar binciken harkokin tsaro ta Birtaniya (RUSI), ya bayyana barazanar da Iran ke yi na kai hare-haren makamai masu linzami kan Turai a matsayin "gaskiya ce, amma tana da iyaka."

Ya ce Iran na iya amfani da makamai masu linzami masu matsakaicin zango, ciki har da waɗanda ke cikin jerin makaman Shahab, domin kai hari kan wuraren Amurka da ke kudanci da kuma kudu maso gabashin Turai.

Sai dai, irin waɗannan makamai na iya fuskantar matsaloli wajen kai wa inda aka nufa da kuma yin tasiri yadda ake so saboda tazararsu daga wurin da aka harba su.

Kaushal ya kuma yi imanin cewa Tehran na iya samun babbar fa'ida idan ta aiwatar da hare-hare ta hanyar ƙungiyoyin da ke mara mata baya, kamar ƴan bindiga a Iraki

da Hezbollah a Lebanon da kuma Houthi a Yemen.

Yaya yawan makaman da Iran take da su?

A nasa bangaren, Douglas Barry na Cibiyar Nazarin Harkokin Dabarun Duniya (IISS) ya ce Iran ta riga ta nuna a baya cewa tana da ikon kai hare-hare daga nesa.

A cewarsa, yunkurin kai hari kan sansanin sojin Amurka na Diego Garcia da ke Tekun Indiya ya nuna cewa Tehran na da makaman da za su iya kai wa nisan fiye da kilomita 2,000.

Sai dai Barry ya ce ba a san ainihin adadin irin waɗannan makamai da Iran ke da su ba. Ya kuma ce mai yiwuwa Tehran ta kasance a shirye ta yi amfani da ko da kaɗan daga cikinsu domin nuna ƙarfinta.

Duk da haka, babban ƙalubalen shi ne tasiri da daidaiton harbi.

"Yayin da nisan hari ke ƙaruwa, haka yake ƙara wahala a tabbatar da cikakken daidaito," in ji shi.

Iran ta taɓa gwada kai hare-hare zuwa wurare masu nisa a baya. Bayan Amurka da Isra'ila sun kai wa Iran hari a watan Fabrairu, Washington ta zargi Tehran da harba wasu makamai masu linzami zuwa Diego Garcia. Amma babu ɗaya daga cikinsu da ya kai inda aka nufa.

A watan Maris kuma, Turkiyya ta ce ta kakkaɓo wasu makamai masu linzami da Iran ta harba. A lokaci guda, wani jirgi marar matuƙi ya kai hari kan sansanin sojin Birtaniya na Akrotiri a Cyprus.

A cewar ɗaya daga cikin majiyoyin da Financial Times ta ambata, harin da aka kai kan sansanin Amurka a Jordan wanda ya kashe sojojin Amurka uku yana da muhimmanci sosai ga Iran.

Majiyar ta bayyana harin a matsayin hari mafi tasiri da Iran ta taɓa kaiwa.

A cewarta, wannan hari wani saƙon gargaɗi ne ga Turai:

"Ana iya kai musu hari da makamai masu linzami, kuma dole su fahimci inda suke a cikin wannan yaƙi."

Ta kuma ce duk wani babban kuskure da Amurka za ta yi, kamar kai hari kan muhimman ababen more rayuwa na Iran, na iya sa yaƙin ya faɗaɗa ya wuce iyakokin Gabas ta Tsakiya.