"Matata ce ta sauya alkiblar rayuwata" - Mikel Arteta

Asalin hoton, Getty Images
A duniyar kwallon kafa, an fi sanin Mikel Arteta a matsayin tsohon dan wasa kuma koci, amma wane ne ainihin wannan fitaccen mutumim?
Arteta ya fara sana'arsa ta kwallon kafa a matakin ƙwararru tare da Barcelona a shekarar 1999, inda ya taka leda a matsayin ɗanwasan tsakiya. Sai dai bai samu damar taka rawa sosai a kungiyar Barcelona ba, lamarin da ya sa daga baya aka tura shi aro zuwa Paris Saint-Germain (PSG).
A shekarar 2002 ya koma Rangers ta Scotland, inda ya lashe kofin gasar Lig a kakarsa ta farko da kungiyar.
Daga nan ya koma ƙasarsa ta Sifaniya, inda ya rattaba hannu da Real Sociedad, kafin daga baya ya ci gaba da gina kansa a gasar Premier League ta Ingila.
Arteta ya koma Everton a shekarar 2005, inda ya zama daya daga cikin jiga-jigan kungiyar. A lokacin zamansa a Everton, an zabe shi a matsayin gwarzon dan wasan kungiyar sau biyu.
Daga bisani ya koma Arsenal a shekarar 2011 kan kudi kusan fam miliyan 10. A lokacin da yake ɗanwasa a Arsenal, ya taimaka wa ƙungiyar lashe FA Cup sau biyu kafin ya yi murabus daga taka leda.
Ko da yake Arteta bai taɓa wakiltar tawagar manyan ƴan wasan Sifaniya ba, ya buga wa ƙasarsa wasa a matakan gasar matasa.
Bayan yin ritaya daga ƙwallon ƙafa, ya shiga harkar horaswa. A shekarar 2016, an naɗa shi a matsayin mataimakin kocin Manchester City a ƙarƙashin jagorancin Pep Guardiola, inda ya samu ƙwarewa mai yawa a fannin horaswa.
Daga baya ya koma Arsenal a matsayin babban koci. A kakarsa ta farko a wannan muƙamin, ya jagoranci kungiyar ta lashe kofin FA.
A halin yanzu, Arteta na daga cikin kocin da ya fi daɗewa a jan ragamar Arsenal a tarihi, kuma ana kallonsa a matsayin daya daga cikin fitattun matasan kociyoyin ƙwallon ƙafa a Turai.
A wata hira da ya taɓa yi, Arteta ya bayyana cewa matarsa ta taka muhimmiyar rawa wajen sauya alkiblar rayuwarsa da sana'arsa, abin da ya sa ya yaba mata a matsayin ɗaya daga cikin manyan ginshiƙan nasarorinsa.
Daga La Masia zuwa Arsenal: Sifaniya zuwa Ingila

Asalin hoton, Getty Images
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
An haifi Mikel Arteta a birnin San Sebastián a kasar Sifaniya, inda ya fara buga kwallo tun yana yaro a kungiyar matasa ta Antiguoko. A can ne ya yi wasa tare da wani wanda daga baya ya zama fitaccen dan wasan duniya, Xabi Alonso.
Daga bisani Arteta ya koma makarantar horas da matasa ta La Masia ta Barcelona, wadda ta yi suna wajen fitar da manyan 'yan kwallo. A lokacin zamansa a makarantar, ya yi mu'amala da fitattun 'yan wasa irin su Andrés Iniesta da Víctor Valdés da kuma Xavi Hernández.
A La Masia ne kuma ya hadu da kyaftin din Barcelona a lokacin, Pep Guardiola, wanda daga baya ya zama jagora kuma malamin da ya taimaka masa a harkar koyarwa a fannin taka leda.
Arteta ya ce ya girma a cikin muhalli tare da kwanciyar hankali, inda ake bai wa wasanni muhimmanci, wannan ya ba shi babbar dama wajen bunkasa baiwar da yake da ita.
Ya bayyana cewa mafi yawan lokutansa na kuruciya sun kasance ne tsakanin buga kwallo da nishadi da kuma zuwa bakin teku domin shakatawa.
A lokacin da yake makarantar horas da matasa ta Barcelona, Arteta ya kulla abota ta musamman da Pepe Reina, wanda daga baya ya zama golan Liverpool.
Arteta ya ce sun hadu ne tun ranar farko da ya isa makarantar.
"Pepe Reina abokina ne. Mun kasance makusanta sosai. Mun zauna a daki daya na tsawon shekara uku. Daya daga cikin muhimman abubuwan tunawa a rayuwata shi ne lokacin da na shafe tare da shi."
Ya taka leda a PSG da Rangers da kuma Everton

Asalin hoton, Getty Images
Mikel Arteta yana da shekara 17 ne lokacin da ya koma kungiyar Paris Saint-Germain (PSG) ta Faransa a matsayin buga mata wasannin aro. A can ne ya hadu da Mauricio Pochettino, wanda ya ce ya taka muhimmiyar rawa wajen taimaka masa a rayuwarsa da sana'arsa.
Arteta ya bayyana Pochettino a matsayin babban yayansa kuma aboki na kusa.
"Mauricio Pochettino ya kasance tamkar garkuwa a gare ni. Yana kare ni a kowane hali kuma ya ba ni kwarin gwiwa sosai," in ji Arteta.
A lokacin zamansa a PSG, ya zura kwallo biyar a wasa 53. Bayan karewar yarjejeniyar buga wasannin aron, PSG ta yi kokarin rike shi, amma ya zabi komawa Barcelona.
A watan Fabrairun 2002, Arteta ya koma kungiyar Rangers ta Scotland kan kudi fam miliyan shida. Ya yi kakar wasa ta farko a Glasgow a kan ganiya, inda cikin karamin lokaci ya zama daya daga cikin fitattun 'yan wasan kungiyar.
Ko da yake ya koma Sifaniya bayan kaka biyu, Arteta ya ce Rangers ce ta taimaka masa wajen kaiwa matakin da ya ba shi damar taka leda a gasar Premier League ta Ingila.
A shekarar 2004 ya koma Spain bayan ya rattaba hannu kan yarjejeniyar euro miliyan 5.2, amma bai samu damar taka leda sosai ba, inda ya buga wasanni uku kacal a rabin farko na kakar wasa.
Saboda haka, a shekarar 2005 ya koma Everton a kan kwantiragin shekara biyar bayan kungiyar ta biya kudin sayensa fam miliyan biyu.
Arteta ya ce zaman da ya yi a Everton na daga cikin mafi kyawun lokutan rayuwarsa a kwallon kafa.
Saboda rawar da ya taka a Goodison Park, an zabi Arteta a matsayin gwarzon dan wasan Everton na kakar wasa sau biyu a jere.
Yana da shekara 29 lokacin da zamansa a Everton ya zo karshe. Ya ce kungiyar ta ba shi duk abin da dan wasa ke bukata domin samun nasara.
Daga bisani ya koma Arsenal, inda lokacinsa a kungiyar ya zama wani sabon babi a rayuwarsa, wato shiga harkar koyarwa, wadda daga karshe ta kai shi ga zama daya daga cikin fitattun kociyoyin kwallon kafa a Turai.
Ta yaya matar Mikel Arteta ta sauya rayuwarsa?

Asalin hoton, Getty Images
A lokacin da yake taka leda a Rangers ta Scotland, Mikel Arteta ya hadu da matar da daga baya ta zama abokiyar rayuwarsa, Lorena, a wani rangadi da ya kai birnin San Sebastián na kasar Sifaniya.
Lorena, wadda 'yar wasan kwaikwayo ce kuma mai yin tallace-tallace wadda take da asali da Argentina da Sifaniya, yanzu tana tare da Arteta da suka haifi yara uku.
Arteta ya ce ba zai iya raba nasarorin da ya samu a ciki da wajen filin wasa da rawar da matarsa ta taka a rayuwarsa ba.
"Ta sauya rayuwata. Ta sauya yadda nake kallon rayuwa," in ji Arteta.
Kocin Arsenal din ya bayyana cewa shi da matarsa sun sha fuskantar lokutan farin ciki da kuma kalubale iri-iri tare.
Ya kara da cewa kasancewar matarsa a kusa da shi abu ne da yake ba shi nutsuwa da farin ciki.
Arteta ya ce a duniyar kwallon kafa, 'yan wasa da kociyoyi sukan mayar da hankali sosai kan kungiyoyin da suke fafatawa da su, amma akwai wani muhimmin bangare na rayuwa da bai kamata a yi watsi da shi ba.
Arteta na da shekara 24 lokacin da ya koma Real Sociedad bayan zamansa a Rangers.
Ya bayyana cewa babban dalilin komawarsa Sifaniya shi ne kokarinsa na hada kan iyalinsa, a daidai lokacin da dangantakar iyayensa ke fuskantar barazanar rushewa saboda yin nisa da su.
"Ban taba ganin cewa komawa Sifaniya shi ne mataki mafi dacewa ba. Amma nauyi ne da ya rataya a wuyana na hada kan iyalina da kuma sake hada su wuri guda."
Wadannan kalamai na nuna cewa baya ga nasarorin da ya samu a filin kwallo, Arteta ya fuskanci kalubale a rayuwa ba wai kawai a fannin taka leda ba, inda iyali da dangantaka suka zama muhimman abubuwan da suka tsara rayuwarsa da kuma halayensa a matsayin mutum kuma jagora.
Bambanci Arsenal ta baya da ta yanzu karkashin Mikel Arteta

Asalin hoton, Getty Images
Mikel Arteta ya koma Arsenal a shekarar 2011 kan kudi fam miliyan 10, inda ya ci gaba da taka leda har zuwa lokacin da ya yi ritaya daga buga kwallon kafa.
Tun farkon zuwansa kungiyar, mutane da dama sun lura cewa yana da halayen shugabanci.
"Na fara magana da mutane, na fara hada kan kowa. Na karfafa wa kungiyar gwiwa ta hanyar gaya musu cewa idan muka yi aiki tare, za mu iya cimma abin da muke so."
Yayin da ya kusa daina buga kwallon kafa, Arteta ya fara karkata hankalinsa sosai ga harkar koyarwa fiye da taka leda.
Daga baya ya koma Arsenal a matsayin koci, a lokacin da kungiyar ke fama da matsaloli ta fuskar tsari da kuma sakamako a filin wasa.
"Akwai matsaloli da dama. Matsalar ta yi zurfi sosai."
Maimakon ya yi gaggawar sallamar 'yan wasa ko sake gina kungiyar gaba daya, Arteta ya mayar da hankali wajen gina su da bunkasa kwarewarsu.
Ya fi karkata wajen inganta tunanin 'yan wasa, karfafa musu gwiwa, da gyara yanayin zuciyarsu tare da dasa musu kishin nasara domin dawo da Arsenal matsayinta na daya daga cikin manyan kungiyoyin Ingila.
Daga lokacin Arteta ya dasa bishiyar zaitun a wajen ofishinsa, wadda ke wakiltar tushen kungiyar da kuma burinsa na ganin ta dore.
Arteta, wanda ya taba zama dan wasan Arsenal kafin daga baya ya zama kocinta, bai taba lashe Premier League a matsayin dan wasa ba. Sai dai daga baya ya samu wannan nasara a matsayin koci, bayan da kungiyar ta yi sama da shekara 20 rabonta da kofin.
Ya lashe FA Cup a matsayin dan wasa, sannan ya sake daukin kofin a matsayin kocin Arsenal.
Mafi muhimmanci, ya jagoranci Arsenal zuwa lashe gasar Premier League bayan shekaru 22 rabon ta da kofin, a kakar wasa ta 2025/26.
Haka kuma ya karfafa kungiyar ta hanyar inganta sassa daban-daban a filin wasa, sannan ya kai Arsenal zuwa wasan karshe a UEFA Champions League.
Arteta ya amfana daga koyarwar manyan kociyoyi irin su Pep Guardiola, Arsène Wenger da José Mourinho. Kuma a yau yana daga cikin kociyoyin da suka fi dadewa suna jan ragamar kungiya a gasar Premier League.
Lokacin da ya koma Manchester City a matsayin mataimakin Pep Guardiola yana da shekara 34 kacal, jim kadan bayan yin ritaya daga taka leda. A cewarsa, a lokacin ne ya fara kirkirar salon koyarwarsa na musamman.
Daga yaron da ya taso a makarantar La Masia ta Barcelona amma bai samu gurbin buga wasannin ba, zuwa daya daga cikin kociyoyin da suka sauya akalar Arsenal, tafiyar Mikel Arteta ta kasance cike da jajircewa, shugabanci da darussan rayuwa.
Sai dai a cewarsa, babu wanda ya yi tasiri a rayuwarsa fiye da matarsa Lorena.
"Ta sauya rayuwata. Ta sauya yadda nake kallon rayuwa."
Wannan ne ya sa Arteta ke ganin nasarorinsa ba kawai sakamakon kwallo ba ne, har ma da tasirin mutanen da suka tsaya tare da shi, musamman matarsa Lorena, wadda ya ce ita ce ta sauya alkiblar rayuwarsa.





























