Me ya rage wa Pantami, Gwarzo da ƴantakarar gwamna da INEC ta cire sunayensu?

    • Marubuci, Abdullahi Bello Diginza
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 4

Yayin da ƴan Najeriya ci gaba da muhawara kan sunayen ƴankatar gwaman da hukumar zaɓen ƙasar INEC ta fitar, tuni wasu wasu da ba su ga sunayensu suka fara mayar da matani.

Jerin sunayen ƴantakarar da INEC ta fitar a ƙarshen mako ya zo wa wasu jam'iyyu da magoya bayansu da mamaki, inda hukumar ta ƙi sanya wasu fitattun ƴansiyasa cikin jerin ƴantakarar da za su fafata a zaɓen na 2027

Daga cikin fitattun sunayen da ba su bayyana a cikin jerin ba akwai na tsohon ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Isa Ali Ibrahim Pantami, da ke takarar gwamnan jihar Gombe a ƙarƙashin jam'iyyar PDP.

Haka ma akwai sunan ɗantakarar gwamnan Kano na jam'iyyar NDC, Comdr Aminu Abdussalam Gwarzo da Musa Shugaba-Abdullahi ɗantakarar gwammnan Nasarawa na NDC da kuma Ladi Adebutu, ɗantakarar gwamnan Ogun daga PDP.

Ɓacewar sunanayen waɗannan ƴantakara ya haifar da muhawara a tsakanin masana siyasa da masu ruwa da tsaki kan abin da doka ta tanada a irin wannan yanayi.

Yayin da wasu ke kallon matakin a matsayin cikas ga burin siyasar waɗannan ƴan takara, wasu kuma na ganin har yanzu akwai hanyoyin da za su iya bi domin neman hakkinsu.

Tambayar da ta fi ɗaukar hankalin jama'a ita ce ko cire suna daga jerin ƙarshe na INEC na nufin ƙarshen takarar mutum gaba ɗaya, ko kuwa har yanzu akwai damar komawa kotu ko ɗaukar wasu matakan doka domin neman a dawo da sunan.

Kan haka ne muka tuntuɓi masana dokokin Najeriya don jin sauran abin da ya rage wa ƴankatarar da aka cire sunayen nasu.

Me ya sa INEC ta cire sunayen mutanen?

Farfesa Nasiru Adamu Aliyu, babban lauya ne a Najeriya, kuma malami a sashen koyar da aikin lauya na Jami'ar Bayero da ke Kano, ya ce INEC ta yi la'akari ne da wani sabon hukuncin da Kotun Ƙoli ta yi wa jam'iyyar ZLP, wanda ya ce idan mutum ba ya cikin rajistar mambobi da jam'iyya ta miƙa wa INEC to ba ɗan jam'iyya ba ne, don haka ba zai yi takara a wannan jam'iyya ba.

Shi ma Barista Danbaba Gangei, wani lauya kuma masanin dokokin zaɓe a Najeriya ya ce akwai wani hukuncin kotun ƙoli da INEC da dogara da shi da ya ce idan mutum yayi takara a wata jam'iyya, ba zai iya shiga wata ba, ballantana ma ya tsaya mata takara, indai bai fito fili ya janye takarar farkon da ya yi a jam'iyyar farkon ba.

''Dole ne idan mutum yana so sai ya fita daga wata jam'iyyar, kuma ya sanar da hakan a hukumance, ta hanyar sanarwa a rubuce'', in ji shi.

Ya ƙara da cewa akwai dokar da ke cewa idan ba a tura sunan mutum kwana 21 kafin rana 10 ga watan Mayun, wato kwana 21 kafin zaɓen fitar da gwani ba zai yi takara ba.

Ko INEC na da hurumin cire sunan ɗantakara?

Ɗaya daga cikin tambayoyin da ƴan ƙasar da dama ke yi ita ce ko INEC na da hurumin cire sunan ɗantakarar da aka miƙa mata?

Farfesa Nasiru Aliyu SAN ya ce sam hukumar ba ta da hurumin cire sunan kowane ɗantakara.

''Abin da doka ta ba ta dama shi ne da karɓi sunayen ƴantakara daga jam'iyyu, sannan ta wallafa su domin tsayawa zaɓe'', in ji shi.

Ya ce in ma da matsala kan saɓa ƙa'ida na yadda wani ya zama ɗantakara kotu ce kawai za ta tantance hakan, ta kuma bayar da umarnin cire sunansa.

Shi ma Barista Danbaba Gangei, ya ce hukumar zaɓen ba ta hurumin cire sunayen ƴantakara.

''Ko da an bayar da sunan ba daidai ba, ko kuma an saɓa ƙa'ida wajen bayar da sunan, INEC ba ta da hurumin cire suna'', in ji shi.

Ya ci gaba da cewa kotu ce kawai ke da wannan hurumi na cewa a cire sunan wane ko a saka sunan wane.

Wane zaɓi ne ya rage musu?

Farfesa Nasiru Adamu Aliyu ya ce mutanen da ba su ga sunayensu ba suna da zaɓi biyu da suka rage musu a wannan kokawa.

A cewar masanin shari'ar zaɓi na farko shi ne ƴantakarar tare da jam'iyyunsu su tuntuɓi hukumar INEC da kansu a hukumance don jin dalilan da suka saka INEC cire sunayen nasu.

''Idan abu ne da za su warware tsakaninsu, shikenan sai a magance matsalar daga nan hukumar ta shigar sunayen nasu domin ci gaba da takararsu'', in ji malamin Jami'ar.

Babban lauyan ya kuma ƙara da cewa idan ba a warware matsalar a hukumar INEC ba to sai mataki na gaba.

''Matakin na gaba shi ne shigar da INEC ƙara a gaban kotun domin neman kotu ta tilasta wa hukumar mayar da sunayen nasu'', kamar yadda ya yi ƙarin haske.

Ya ci gaba da cewa kotu ce za ta warware zare da abawa kan wannan batu bayan sauraron duka ɓangarorin da hujjojin da suka gabatar mata.

"Idan INEC ta gamsu da hujjojin ƴantakarar za ta tilasta wa INEC mayar da sunayensu cikin jerin waɗanda za su yi takarar gwamna a zaɓen an 2027 da ke tafe'', in ji shi.

'Tsugune ba ta ƙare ba'

To sai dai Farfesa Nasiru Aliyu SAN ya ce bayan tiya akwai wata cacar, domin kuwa koda mutanen sun samu nasara a kotu, kawai wata matsalar da za su iya fuskanta.

''Matsalar ita ce idan sun yi nasara a babban zaɓen na 2027, za a iya shigar da su ƙara a kotunan sauraron ƙorafin zaɓe, a ƙalubalance su kan wannan batu'', in ji shi.

Malamin jami'ar ya ce kuma komai zai iya faruwa a wannan lokaci, domin kuwa kotu za ta iya ƙwace nasarar tasu.

''Ina ganin wannan batu zai haifar musu da cikas gaskiya'', in ji shi.