An yanke wa tsohon uban daba Keffe D hukunci kan kisan Tupac
An yanke wa Duane Davis, wanda aka fi sani da Keffe D, hukuncin ɗaurin shekaru 40 a gidan yari bisa samunsa da laifin shirya kisan fitaccen mawaƙin rap, Tupac Shakur.
A watan Satumba, wata tawagar alƙalai ta same shi da laifin kitsa kisan kan ta amfani da makami mai haɗari, dangane da harbin da aka yi wa mawaƙin a wani harin kwanton ɓauna da mota a birnin Las Vegas, ranar 7 ga Satumba, 1996.
Davis ya ce zai ɗaukaka ƙara kan hukuncin.
Hukuncin da aka yanke wa Davis, mai shekaru 63, shi ne na farko da aka samu a wannan tsohuwar shari'ar kisan da ta ɗauki hankalin masoyan hip-hop tsawon kusan shekaru 30.
Masu gabatar da ƙara sun bayyana cewa, duk da cewa Davis bai harbe mawaƙin da kansa ba, shi ne ya jagoranci ƙungiyar da ta aikata kisan. A cikin littafin tarihin rayuwarsa da ya wallafa, Davis ya amince cewa shi ne ya samar da bindigar da aka yi amfani da ita wajen aikata laifin.
Muhimman hujjojin da aka gabatar a shari'ar sun haɗa da kalaman Davis da ya sha furtawa a bainar jama'a, inda ya amince cewa yana cikin wata farar mota kirar Cadillac da aka harba harsasan da suka kashe mawaƙin daga cikinta.
A lokacin da aka kashe shi, Shakur yana da shekaru 25 kuma yana kan ganiyarsa a fagen waƙoƙin rap, inda ya kasance ɗaya daga cikin mawaƙan da suka fi tasiri a wannan fanni. Ya sayar waƙoƙinsa sama da miliyan 75 a faɗin duniya.
Tsawon shekaru 30, binciken kisan nasa ya kasance ɗaya daga cikin fitattun shari'o'in kisan da suka daɗe ba tare da an gano waɗanda suka aikata su a Amurka ba.