Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yaushe ɗarikar Tijjaniya ta shiga Najeriya kuma mene ne aƙidunta?
- Marubuci, Isiyaku Muhammed
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 6
Darikar Tijjaniyya na daga cikin manyan ɗarikun Musulunci da suka yi tasiri sosai a nahiyar Afirka, musamman a Arewacin Najeriya, inda malamai da mabiyanta ke bayyana cewa koyarwarta na ta'allaƙa ne kan zikiri, istigfari, salatin Annabi (SAW) da kuma riƙo da koyarwar Alƙur'ani da Sunnah.
Sanannen malamin darikar Tijjaniyya a Najeriya Sheikh Halliru Maraya ya yi bayani dalla-dalla kan tarihin kafuwar ɗarikar, manyan ƙa'idojinta, yadda ta shiga Najeriya, tasirinta ga al'umma, da kuma batutuwan da suka shafi reshen da ake kira "Faila" da kuma shugabancin ɗarikar a yau.
Ya jaddada cewa ainihin manufar Tijjaniyya ita ce kusantar Allah, bin Manzon Allah (SAW), da kuma kyautata zamantakewa tsakanin al'umma.
Asalin ɗarikar Tijjaniyya
A cewar Sheikh Halliru Maraya, an assasa ɗarikar Tijjaniyya ne a shekara ta 1196 Hijiriyya, daidai da 1782 Miladiyya, a wani gari mai suna ƙaryatu Abu Samkun da ke jihar Albayat a ƙasar Aljeriya.
A cewar malamin, garin ƙarami ne idan aka kwatanta da wasu yankuna, domin yana da faɗin murabba'in kilomita 585 ne kacal, wanda ya yi daidai da hekta 58,500, sannan malamin ya ce jihar Kaduna ta fi garin girma da kusan sau 78.
Shehin ya ce a lokacin ne Ahmadu Tijjani ya ga Manzon Allah (SAW) ido-da-ido, sannan ya nanata cewa ganin Manzon Allah ba wani abu ba ne da ya saɓa wa Alƙur'ani ko Hadisi, domin a cewarsa akwai waliyyai da dama da suka taɓa ganin Manzon Allah (SAW).
An dai haifi Sheikh Ahmadu Tijjani a ranar Alhamis 13 ga Safar shekara ta 1150 Hijiriyya, wanda ya yi daidai da 3 ga Yunin 1737 Miladiyya.
Shi ne ya assasa ɗarikar Tijjaniyya, amma Sheikh Halliru Maraya ya jaddada cewa ɗarikar ba ta zo da wani sabon abu ba.
A cewarsa, abubuwan da ake yi a cikinta kamar istigfari, salatin Annabi da hailala duk suna cikin koyarwar Musulunci tun da daɗewa.
Ya ce: "Kamar yadda ake da mazhabobin Malikiyya da Hanafiyya a ɓangaren fikihu, haka kuma akwai Ƙadiriyya, Tijjaniyya da Shaziliyya a ɓangaren zikiri."
Manyan abubuwan da ɗarikar ta ƙunsa
A cewar Sheikh Halliru Maraya, Tijjaniyya tana koyar da: Istigfari da Salatin Annabi da Hailala ne.
Ya ce duk wanda ke cikin ɗarikar yana gudanar da abin da ake kira Lazimin Safe, wanda ya ƙunshi: Istigfari 100 da Salatin Annabi 100 da Hailala 100.
Haka kuma bayan la'asar ana yin irin wannan zikiri a sirrance wanda ake kira Lazimin Yamma.
Sannan akwai Wazifa, wacce ta ƙunshi: Istigfari 30 da Salatul Fatihi 50 da Hailala 100 da Jauharatul Kamali 12.
Sai dai ya ƙara da cewa wanda bai iya Jauharatul Kamali ba yana iya yin Salatul Fatihi 20 a madadinsa.
Baya ga haka shehin malamin ya ce ɗarikar tana koyar da: Bin Allah da Bin Manzon Allah (SAW) da Zikirin Juma'a.
Ƙa'idojin ɗarikar
Sheikh Halliru Maraya ya bayyana cewa Tijjaniyya tana ginuwa ne bisa wasu muhimman ƙa'idoji da suka haɗa da:
- Riko da Alƙur'ani
- Bin Sunnah
- Nisantar saɓon Allah
- Cin Halal da guje wa haram
- Nisantar cutar da bayin Allah
- Bayar da haƙƙoƙin bayin Allah
Sharuɗɗan shiga ɗarikar
A cewar Sheikh Halliru Maraya, kafin mutum ya shiga ɗarikar sai ya amince da wasu sharuɗɗa:
- Yin sallah cikin jam'i
- Yin sallah a kan lokaci
- Bin iyaye
- Daina shan sigari (A wurin mafi yawan malamai)
- Ba a fita idan an shiga (Abin nufi shi ne riƙe alƙawarin ba zai daina zikira ba)
- Rashin ziyartar wasu waliyyai domin neman taimako ko madadi
- Sannan ana so a samu shaidar shiga ɗarikar
Shigar Tijjaniyya Najeriya
Sheikh Halliru Maraya ya ce babu tabbataccen lokaci guda da tarihi ya tabbatar da shigowar Tijjaniyya Najeriya.
Sai dai akwai bayanai da dama da ke nuna cewa Sheikh Umarul Futi yana daga cikin waɗanda suka taka muhimmiyar rawa wajen yada ɗarikar.
A cewarsa malamin, Sheikh Umarul Futi ne ya auri ƴar Sarkin Musulmi Muhammad Bello.
Sheikh Maraya ya ce ya zauna a wurare kamar Zariya, Kano, Kukawa da Bauchi da sauran su.
Tarihi ya nuna cewa ya zo Najeriya tsakanin shekarar 1831 ko 1832, wato bayan kafuwar ɗarikar da kusan shekaru 49 zuwa 50.
Sai dai Sheikh Halliru Maraya ya ce akwai shaidu da ke nuna cewa tun kafin isowarsa ana Tijjaniyya a Unguwar Madabo da ke Kano.
Saboda haka ya ce: "Za a iya cewa Sheikh Umarul Futi ya jaddada ɗarikar ne, amma akwai alamu cewa Tijjaniyya ta riga ta shiga Najeriya kafin zuwansa."
Shehin malamain ya bayyana cewa tun kafin ɗarikar ta cika shekara 50 da kafuwa ta riga ta shiga Najeriya.
Tasirin ɗarikar Tijjaniyya
Sheikh Halliru Maraya ya bayyana wasu abubuwa da ya ce tasirantuwa da ɗarikar suka janyo kamar haka:
- Tarbiyantar da mabiyanta
A cewar Sheikh Halliru Maraya, babban tasirin ɗarikar shi ne tarbiyyar mabiyanta su nisanci saɓa wa dokokin Allah da Manzon Allah da dokokin ƙasa da son zaman lafiya.
Ya yi iƙirarin cewa idan aka duba gidajen yari, da wahala a samu ɗan Tijjaniyya wanda ya karɓi ɗarika sosai kuma yake da zawiyya da ya riƙa.
- Zaman lafiya tsakanin jama'a
Ya ce ɗarikar tana koyar da ganin sauran Musulmi a matsayin ƴan'uwa ba tare da kafirta su ba, sannan ya ce tana ƙarfafa zaman lafiya da masu sauran addinai.
- Ƙarfafa neman ilimi
Shehin ya ce ɗarikar ta taka rawa sosai wajen haddar Alƙur'ani da neman ilimi, domin a cewarsa, mahaddatan Alƙur'ani da yawa da suka yi fice a yankin nan sun fito ne daga gidajen Tijjaniyya.
- Zamantakewa
Sheikh Maraya ya ce ɗarikar na koyar da girmama iyaye, sannan mata su mutunta mazansu, su kuma maza su kiyaye haƙƙoƙin iyalansu.
Faila
A game da ko akwai rarrabuwa a tsakanin ƴan ɗarikar, Sheikh Halliru Maraya ya bayyana cewa akwai bambance-bambancen ra'ayi tsakanin mabiyan ɗarikar kamar yadda ake samu a kowace al'umma.
Sai dai ya ce: "ɗarikar ɗaya ce, amma masu yin ɗarikar suna iya samun saɓanin ra'ayi kan siyasa, zamantakewa ko wasu lamurran rayuwa."
Sai dai duk da wannan bambanci, ya ce mabiyan suna haɗe ne a wajen lazimi da sauran ginshikan darikar.
A game da waɗanda ake kira ƴan Faila, Shehin ya bayyana cewa kalmar Faila tana nufin "ambaliya", amma ma'anar ta a ɗarika ana nufin ambaliyar sanin Allah.
Ya danganta wannan fahimta da Sheikh Ibrahim Kaulaha, wanda ya haɗu da Sarkin Kano Abdullahi Bayero a lokacin hajjin shekarar 1937.
Malam Maraya ya ce bayan haka ya zo Najeriya a shekarar, sannan a shekarar 1946 wasu fitattun ƴan Najeriya uku suka je wajensa a Kaulaha:
Waɗanda suka ziyarce shi su ne: Sheikh Tijjani Zangon Barebari da Sheikh Sani Kafinga da Sheikh Umarul Falke
A cewarsa, mabiyan Faila na yau suna danganta kansu da Sheikh Ibrahim Kaulaha ne, amma ya jaddada cewa jagoran ɗarikar ya koyar da riƙo da Allah da bin Manzon Allah (SAW) ne da barin duk wani abu da ya saɓa wa shari'a.
Sheikh Halliru Maraya ya kawo misali da cewa: "A ranar da Sheikh Ibrahim Kaulaha zai rasu, aikin da ya yi na ƙarshe shi ne sallah. Saboda haka duk wanda ya ce yana binsa amma baya sallah, ya saɓa wa koyarwarsa."
Ya kuma bayyana cewa Sheikh Ibrahim Kaulaha ya taɓa cewa duk wani abu da aka jingina masa wanda ya saɓa wa Shari'a, to a yi watsi da shi.
Fitattun shehunan Tijjaniyya
Sheikh Halliru Maraya ya ce ɗarikar ta yi jiga-jigan shehunnai a Najeriya da ya ce sun yi tasiri sosai, inda ya ambata wasu daga ciki kamar haka:
- Sheikh Muhammadu Salga (Kano)
- Sheikh Mijin Yawa (Kano)
- Jiga-jigan Khalifofi
- Sheikh Tijjani Zango Bare-bare (Kano)
- Sheikh Atiku (Kano)
- Sheikh Mai Hula (Kano)
- Sheikh Gbirima (Nguru)
- Sheikh Malam Yahuzu Zaria
- Sheikh Ɗahiru Bauchi
- Sheikh Sharif Saleh
- Shaikh Isyaku Rabiu
- Sheikh Ahmad Ali Abul-Fathi
Sheikh Halliru Maraya ya bayyana cewa a yanzu khalifanci a mafi yawan gidajen Tijjaniyya yana tafiya ne ta hanyar magada ko waɗanda aka naɗa.
Ya yi misali da cewa bayan rasuwar Sheikh Ibrahim Khalifa, Sheikh Muhammadu Bashir ya gaji Sheikh Tijjani Zango Bare-bare.
Ya kuma bayyana cewa sheikh Injiniya Hassan Kafinga ya gaji Sheikh Sani Kafinga.
A ɓangaren Sheikh Atiku kuwa, Sheikh Tuhami ne khalifansa.
A game da Khalifan ɗarikar a yanzu, ya ce a Najeriya, tun da Sheikh Ibrahim Kaulaha ya naɗa khalifa, wanda Khalifan nasa ya ambata shi ne zai zama Khalifa a ƙasar.
Ya ce Khalifan Kaulahan ya naɗa Sarki Muhammadu Sanusi II ne a matsayin Khalifan ɗarikar.
Sai dai ya tabbatar da cewa akwai saɓani da bambancin ra'ayi, domin a cewarsa wasu za su iya bayyana ra'ayi saɓanin haka.
Amma Sheikh Maraya ya ƙara da cewa, "hakan ba ya canja ainihin ɗarikar Tijjaniyya. Abin da hakan ke iya shafa kawai shi ne siyasar shugabanci."