Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Me ya sa wayoyin hannu suka rage yawan hira tsakanin mutane?
- Marubuci, Redacción
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Mundo
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 7
Ba lallai bane ku lura, amma alƙaluma sun tabbatar cewa: a kowacce shekara yawan maganar da mutane ke yi na ƙara raguwa.
Ko babu komai, wannan ne zahirin abin da ke faruwa a tsakanin al'adun jama'ar, Yamma kamar yadda wani nazari da aka wallafa a mujallar *Perspectives on Psychological Science* ya nuna.
Marubutan binciken sun nazarci yawan lokutan da mahalarta kusan 2,000 na kowane zamani, daga ƙasashe da dama ciki har da Amurka, Mexico, Australia da wasu ƙasashen Turai, suke magana a cikin yini.
Bayan nazarin bayanan da aka tattara cikin tsawon shekara 15, sun gano wata bayyananniyar dabi'a ta raguwar kalmomi: mutane sun daina furta fiye da kalmomi 300 a kowace rana.
Gaba ɗaya, hakan na nufin kusan kalmomi 110,000 a shekara, kwatankwacin abubuwan da ke cikin ɗan gajeren labari.
Ko da yake masana kimiyya Valeria Pfeifer da Matthias Mehl sun ce samfurin mahalartan ba a tsara shi ba ne domin gano musabbabai, saurin yaɗuwar amfani da wayoyin hannu, intanet da kafafen sada zumunta a cikin shekaru da dama da suka wuce na iya yin tasiri kan yadda mutane suka rage magana ko hira da juna.
Sai kuma annobar Covid-19, wadda ta tilasta wa mutane da dama zaman keɓantuwar jama'a, sannan kuma aikin gida da bunƙasar fasahohin da ba sa buƙatar hulɗar kai tsaye.
Sai dai Mehl ya amince cewa akwai al'ummomin "masu fifita ƙungiya", waɗanda sakamakon binciken da aka samu daga mutane sama da 2,000 da aka nazarta ba zai dace da su ba.
Ta yaya kuka gano cewa yawan maganar mutane na raguwa a kowacce shekara?
A 2007, mun wallafa wani bincike kan ƙarancin bambance-bambancen da ke tsakanin jinsi wajen amfani da kalmomi a rayuwar yau da kullum [maza da mata suna furta kusan adadin kalmomi iri ɗaya].
Kuma mutane sun damu cewa samfurin mahalartanmu ya yi kaɗan.
Saboda haka, bayan shekaru 17 mun dawo da wani samfurin da ya kusan ninka na farko sau huɗu, wanda ya ƙunshi mutane sama da 2,000.
Dokta Pfeiffer ta ce, "Ina da sakamakon, kuma akwai kusan kalmomi 12,000."
Sai na amsa, "Lallai akwai kuskure, ai hakan ba zai yiwu ba. Dole ne a ce akwai kusan kalmomi 16,000, domin wannan shi ne abin da muka gano a lokacin."
Ta sake duba alkaluman, kuma tun farko daidai suke.
Saboda haka mun yi mamakin ganin cewa kusan kalmomi 4,000 sun ɓace cikin kusan shekaru 17.
Hasashena na farko shi ne cewa wayoyin hannu sun maye gurbin yadda muke magana, muna amfani da manyan yatsunmu fiye da yadda muke yi a baya, muna aika saƙonni da yawa, kuma maganar mu ta ragu sosai. Shin abin da kuka lura kenan?
Ba mu binciki wannan batu kai tsaye a cikin binciken ba.
Amma ina da cikakken yaƙinin cewa mun maye gurbin kaso mai girma na kalmomin da ake furtawa da kalmomin da ake rubutawa.
A gaskiya ma, ba zan yi mamaki ba idan jimillar yawan kalmominmu ta fi ta da ba, domin muna yin rubuce-rubuce masu yawa ta imel, saƙonnin rubutu da kuma a kafafen sada zumunta.
Amma abu mafi ban sha'awa kuma mafi muhimmanci shi ne cewa idan muna rasa waɗannan kalmomi saboda na'urorinmu na dijital, to tambayar ita ce ko waɗanda suka taso da fasahar dijital, wato matasa, sun rasa kalmomi fiye da sauran mutane.
Kuma mun iya tabbatar da hakan.
Don haka muka raba mahalartanmu gida biyu: rukuni na masu ƙasa da shekara 25 da kuma wani rukuni na masu sama da shekara 25.
Kuma kamar yadda ake tsammani, mun gano cewa raguwar ta fi yawa a cikin rukuni na matasa.
A matsakaici, hakan ya kai kalmomi 338 a rana.
Mahalarta mafi ƙanƙantar shekaru, waɗanda ke ƙasa da shekara 25, sun rasa kalmomi 451.
Masu shekaru sama da haka sun rasa kalmomi 314.
Wannan na nuna cewa muna rasa kalmomi saboda waɗannan na'urori.
"Raguwar ikon tattaunawa dabi'a ce ta al'ummomin 'na Yamma kuma masu fifita mutum ɗaya'," in ji Matthias Mehl.
Shin kun san takamaiman kalmomin da muke rasawa da kuma irin tattaunawar da wataƙila muka daina yi yanzu?
Da alama abin da muka rasa shi ne babban ɓangare na ƙananan tattaunawar yau da kullum da muke yi a baya.
Saboda tsarin zamantakewa ya sauya sosai har yau akwai ƙarancin damar musayar ƴan kalmomi da abin da masana ke kira "raunin alaƙa".
Waɗannan su ne mutanen da muke haɗuwa da su a wurare daban-daban, waɗanda ba su taka muhimmiyar rawa musamman a rayuwarmu ba, amma muke sake haɗuwa da su akai-akai kuma a da muna da wata alaƙa da su.
Tabbas, yanzu idan na fita yawo da kare na da safe, yawanci nakan saka belun kunne domin sauraron labarai kuma ba na gaishe da maƙwabci na.
Ko kuma idan na je babban kanti kuma ina sauraron wani podcast a layin biyan kuɗi, don haka ba na samun damar yin hira da mai karɓar kuɗi.
Shin irin wannan hulɗar ce ta yau da kullum kuke nufi?
Ƙwarai, abin da nake nufi kenan.
Kuma muna ci gaba da faɗaɗa iyakokin hakan.
Yanzu za ka iya biyan kuɗin abincinka a gidan cin abinci ta hanyar matsa wayarka kusa da rasit, ka duba lambar shafi sannan ka biya da wayarka.
Ba sai ka yi magana da mai hidimar abinci ba.
Haka abin yake kuma idan ya zo ga neman kwatance.
Ban san wanda har yanzu ke tambayar hanya ba idan bai san inda zai je ba, musamman idan yana da wayar hannu.
Waɗannan su ne ainihin irin tattaunawar da nake ganin muna rasa.
Kuma yana da ban sha'awa a tambaya: shin hakan yana da muhimmanci?
Yana sa rayuwarmu ta fi sauƙi, ko ba haka ba?
Za mu iya sauraron podcast yayin da muke yawo da karnukanmu.
Don haka ina ganin neman inganci ne ya sa muka rasa waɗannan tattaunawar ba-zata.
Akwai wani gidan burodi a garinmu; ni asali ɗan Jamus ne, yanzu ina zaune a Arizona [Amurka], kuma gidan burodin yana da kyau ƙwarai.
Na shiga, sai mutumin ya ce min, "Sannu, Matthias."
Sai na yi tunani a raina, "Kai, ta gane ni."
Ina ganin abin da muke kuma rasa shi ne waɗannan ƙananan lokutan jin ana cikinka da al'umma da muke samu a irin waɗannan tattaunawar ba-zata.
Lokacin da muke yawo da karnukanmu kuma muka gaishe da maƙwabci, muna jin an gane mu, muna jin an lura da mu, muna jin wannan ɗan ƙaramin lokacin kasancewa cikin wata al'umma.
Ba irin zurfin jin kasancewa tare da iyali ba ne, amma yana sa mutum jin daɗi.
Kuma ina ganin a lokacin da ake cewa muna fuskantar wata annobar kaɗaici, warewar jama'a na samun muhimmanci sosai.
Ina ganin waɗannan ƙananan lokutan da ake ganin ka, ake gane ka, kuma ka ji wani ɗan ƙima a kanka, na iya zama masu muhimmanci ƙwarai.
Bayananku sun tsaya a 2019, wato kafin kullen da aka yi saboda annobar Corona da kuma sauyin da ta kawo na gudanar da aiki daga gida. Kuna da wata fahimta kan abin da ya faru tun bayan fara annobar?
A halin yanzu ana gudanar da wasu bincike kuma za mu iya nazarinsu cikin ƴan shekaru masu zuwa.
Saboda haka ba mu da bayanan kai tsaye, amma ba ni da wani dalilin da zai sa in yi tunanin cewa wannan dabi'a ta juya baya.
Domin annobar wani yanayi ne da ya haifar da warewa mai yawa.
Lokaci ne da ba za mu iya yin irin waɗannan tattaunawar ba-zata ba saboda dole ne mu kiyaye tazara tsakanin jama'a.
Bayan annobar ta lafa, mutane da dama sun ba da rahoton wata irin kasala ta zamantakewa, kamar yadda hulɗar jama'a ta ƙara wahala, kuma karɓar baƙi ko fita ya zama mafi rikitarwa.
Don haka ina ganin wataƙila mun murmure kaɗan daga wannan koma bayan da ya shafi annobar, amma gaba ɗaya zan yi mamaki sosai idan har mun iya juyar da wannan dabi'a da gaske.
Kuna da wata hanya da za mu iya sauya wannan yanayi?
Ban san wani saddabaru da zai yi tasiri ba, amma na yi magana game da masana biyu, Gillian Sandström da Nicholas Epley, waɗanda suka rubuta littattafai biyu: Once Upon a Stranger da A Little More Social.
Na karanta su ne bayan abin da muka lura da shi na cewa muna rasa waɗannan kalmomi.
Ana iya taƙaita saƙonsu kamar haka: ku yi ƙoƙari, ku ƙara hulɗarku da mutane.
Saboda haka na sanya wa kaina wannan buri: duk lokacin da na yi tunanin "ina ganin zan iya yin magana da wannan mutumin yanzu", sai kawai in yi hakan.
Akwai wani abu da ya ɗauki lokaci kafin in fahimce shi:
Muna magana kan waɗannan ƙananan lokutan jin kasancewa cikin wata al'umma, kuma wannan shi ne abin da nake ɗauka daga waɗannan tattaunawar, amma ina ganin al'umma gaba ɗaya za ta iya amfana da su fiye da haka.
Don haka, da zarar na gaishe da maƙwabci na a titi na ce "Sannu", na ɗan ji wannan ma'anar "ina cikin wannan unguwa."
Amma a lokaci guda, irin wannan ƙaramar hulɗa ita ma tana da tasirin kwantar da hankali.
Tana gaya mana: "Ka saurara, ina ganinka, ba ni da wata muguwar manufa a kanka."
Kuma ina ganin a zamaninmu, inda ba kawai muke fuskantar annobar warewar jama'a ba, har ma da ƙalubalen rarrabuwar kawuna mai tsanani, wannan na iya zama wata dama ta kusantar da juna kaɗan.