Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Me ya sa Dangote ya tsawaita sayar da hannayen jarin matatarsa?
Matatar Mai ta Dangote ta tsawaita wa'adin sayar da hannayen jarinsa na dala biliyan 1.6 da ƙarin mako biyu, wanda ake sa ran zai kasance ɗaya daga cikin manyan sayar da hannayen jari a Afirka.
An fara sayar da hannayen jarin ne a ranar 14 ga Satumba, kuma ana sa ran za a rufe shirin a ranar Talata 13 ga Oktoba, sai dai yanzu za a ci gaba da karɓar buƙatun saye har zuwa 27 ga Oktoba, bayan samun amincewar Hukumar hada-hadar hannayen jari ta Najeriya.
Matakin ya zo ne bayan attajirin ɗan kasuwa Aliko Dangote ya bayyana cewa yawan buƙatun sayen hannayen jarin ya zarce adadin kuɗin da kamfanin ke son sayarwa da ninki uku zuwa huɗu.
Kamfanin ya ce yana fatan jawo hankalin masu zuba jari na ƙananan matakai har miliyan 10, a wani yunƙuri na faɗaɗa mallakar jama'a a ɗaya daga cikin manyan kadarorin masana'antu a Afirka.
Sai dai kawo yanzu, kamfanin bai fitar da cikakken bayani kan adadin kuɗin da aka nemi zuba wa cikin hannayen jarin ba.
Me ya janyo tsawaita wa'adin?
Kamfanin Dangote ya ce ya yanke shawarar tsawaita wa'adin ne domin bai wa ƙarin masu zuba jari daga sassa daban-daban na Afirka damar shiga, musamman waɗanda suka fuskanci matsaloli wajen buɗe asusu da tantance bayanan shaida ko kuma cika wasu sharuɗɗan da ake buƙata.
Dangote ya ce an tsawaita wa'adin ne ba don tara ƙarin kuɗi ba sai domin bai wa mutane da dama damar shiga cikin tsarin mallakar kamfanin.
To amma Dr Kasimu Garba Kurfi, shugaban kamfanin hada-hadar hanayen jari na ATP ya ce ba haka batun yake ba.
''Duk wanda ka ga ya saka wa'adin sayar da abu, sannan ya tsawaita to bai samu abin da yake so ba ke nan'', in ji shi.
Dangane da batun da Dangote ya yi cewa ya samu ninki uku zuwa huɗu na abin da yake nema, Dr Kurfi ya ce ba a nan take ba.
''Ka san ba komai ba ne mutum , musamman ɗankasuwa zai fito fili ya bayyana maka gaskiyarsa ba, amma ina mai tabbatar maka inda ya samu abin da yake so da ba zai tsawaita ba'', in ji shi.
Dr Kurfi ya ce talakawa da dama ba su fito don sayen hannayen jarin ba.
Me ya janyo tsaikon sayar da hannayen jarin?
Dr Ƙasimu Kurfi ya ce akwai abubuwa guda biyu da suka janyo tsaikon sayar da hannayen jarin.
''Na farko shi ne sharaɗin tilasta mallakar email kafin sayen hannun jari, su talakawa ina ruwansu da imel?'', in ji shi.
Ya ce ko bankunan da ke ƙasar, inda sun saka sharaɗin mallakar imel kafin buɗe asusun, to da ba za su samu kwastomomi da yawa ba.
Abu na biyu da ya haifar da rashin sayen hannayen jarin shi ne sayar da su da naira da ake yi a cewar Dr Kurfi.
''Hakan ya taƙaita wa ƴan ƙasashen waje damar sayen, saboda dole an ce sai sun yi amfani da kuɗin naira'', kamar yadda ya yi ƙarin haske.
Hannayen jarin nawa Dangote zai sayar?
Kamfanin Dangote ya ƙudiri aniyar sayar da hannayen jari da darajarsu ta kai naira biliyan 4.1, inda aka sanya farashin kowanne kan naira 525.
Mafi ƙarancin adadin hannayen jarin da mutum zai iya saya shi ne guda 10, wanda kuɗinsu ya kai naira 5,250.
Idan aka sayar da dukkan hannayen jarin da aka fitar, kamfanin zai iya tara kuɗi kimanin naira tiriliyan 2.15, wato kusan dala biliyan 1.6.
Haka kuma, idan aka yi amfani da zaɓin ƙarin fitar da hannayen jari, adadin kuɗin da za a tara na iya kaiwa kusan dala biliyan 2.1.
Da farko, tayin ya haifar da gagarumar sha'awa tsakanin masu zuba jari kanana a Najeriya.
Inda da dama suka ɗauke shi a matsayin wata dama ta mallakar wani ɓangare na matatar mai da ta zama jigo a shirin Najeriya na rage dogaro da shigo da albarkatun man fetur daga ƙasashen waje.
Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito cewa yawan masu neman sayen hannayen jarin ya yi yawa har ya sanya wasu dandalin zuba jari a intanet suka fara fuskantar matsin lamba.
A lokaci guda kuma, kafafen sada zumunta sun cika da barkwanci da saƙonnin masu sha'awar zuba jarin, inda suke murnar yiwuwar zama masu hannun jari a Matatar Dangote.
Mene ne maƙasudin sayar da hannayen jarin?
Ɗaya daga cikin manyan manufofin tattara kuɗin shi ne taimaka wa shirin ninka aikin matatar daga ganga kusan 700,000 a rana zuwa ganga miliyan 1.4 a rana.
A farkon shekarar 2024 ne, matatar ta fara tace ɗanyen mai, kuma ta zama wani muhimmin ginshiƙi a ƙoƙarin Najeriya na rage shigo da man fetur daga ƙasashen waje tare da ƙara yawan man fetur da sauran kayayyakin da aka tace a cikin ƙasar.
Idan wannan faɗaɗawar ta yi nasara, za ta iya ƙara wa matatar ƙarfi a kasuwannin makamashi na yankin tare da haɓaka yawan kayayyaki da nau'o'insu da take samarwa.
Sai dai muhimmancin fitar da hannayen jarin ga jama'a (IPO) ya zarce batun matatar kaɗai.
Bisa farashin da aka sanya wa hannun jarin, matatar ta ƙiyasta darajarta zuwa kusan dala biliyan 47, kamar yadda lissafin da kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito lokacin da aka amince da tayin ya nuna.
Sai dai wasu masu zuba jari da masu nazarin harkokin kuɗi suna tambayar ko wannan ƙimanta darajar ya yi daidai da irin kuɗaɗen shiga da matatar ke samu da kuma hasashen bunƙasar da ake sa ran za ta samu a nan gaba.