Me ya sa babu sunan Abdussalam Gwarzo a jerin ‘yan takarar gwamnan Kano?

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 3

Jam'iyyar adawa ta NDC ta ce ta yi amanar cewa matsala ce aka samu wajen tantance jerin sunayen 'yan takara da Hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta fitar inda aka cire sunan Aminu Abdussalam Gwarzo a matsayin ɗan takarar gwamna na jam'iyyar a Jihar Kano.

Ba a dai ga sunan Gwarzo ba a cikin jerin sunayen da hukumar ta fitar a karshen makon nan ba, wanda ya kunshi ƴan takara 17 daga jam'iyyun siyasa daban-daban.

Jam'iyyun All Progressives Congress (APC), da Peoples Democratic Party (PDP) da kuma African Democratic Congress (ADC) na daga cikin jam'iyyun da ke da 'yan takara a cikin jerin sunayen.

Dakta Dr Yusuf Ibrahim Kofar mata sakataren kungiyar kwankwasiya, ya shaida wa BBC cewa lamarin bai tayar masu da hankali ba.

''Na farko dai dan takararmu na gwamna a jihar Kano, kwamared Aminu Abdulsalam Gwarzo ya riga ya yi rajista da jam'iyyar NDC kuma ya yi ta akan lokaci, sannan abu na biyu kuma shi ne bai yi rajista da jam'iyya biyu ba, a don haka wannan hukunci na kotun koli ba zai taba shi ba,'' in ji shi.

Ya ce bayan zaben fitar da gwani shi ne ya samu nasara a zaben kuma sunansa aka kai hedikwatar jam'iyyar ta kasa, daga nan aka kai sunansa ofishin hukumar zabe ta INEC.

''Duk an yi wannan kuma babu inda aka sami kuskure, duk sunansa ne, shi ya sa muke ganin wannan wani kuskure ne aka samu wajen buga sunayen ta kwamfuta wanda muke tunanin nan da ranar Litinin mai zuwa za a warware a gyara,” in ji shi.

Yusuf Ibrahim Kofar Mata ya ce uwar jam'yyar ta kasa ta tabbatar cewa ba ta yi kuskure ba kuma ta bi hanyoyin da suka da ce wajen gabatar da takardun ɗan takarar gwamna na jam'iyyar.

Ya kuma kara da cewa kawo yanzu hukumar zabe ta INEC ba ta turo masu da takadar da ke dauke da jerin sunnayen 'yan takarar su ba.

A cikin watan Maris na 2026 ne Aminu Abdussalam ya sauka daga mukamin mataimakin gwamnan jihar Kano bayan rana gari da gwamna Abba Kabir Yusuf wanda ya koma jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya.

A cikin wata sanarwa mataimakin gwamnan ya ce ya ɗauki matakin ne domin tabbatar da zaman lafiya a jihar Kano da guje wa haifar da tsaiko a harkokin mulkin jihar.

Ajiye aikin nasa ya zo ne bayan da majalisar dokokin jihar ta fara yunƙurin tsige shi saboda wasu zarge-zarge da ta ce suna da alaƙa da almundahanar kuɗaɗe, zargin da mataimakin gwamnan ya sha musantawa.

An fara samun tsamin dangantaka tsakanin ɓangaren gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf da mataimakin nasa ne tun bayan da gwamnan ya sauya sheka daga jam'iyyar NNPP zuwa APC tare da wasu kwamishinoninsa.

Shi dai Gwarzo bai bi shi zuwa APC ba, yayin da ya ci gaba da zama a NNPP wadda ke karkashin jagorancin tsohon gwamnan jihar Kano Rabiu Kwankwaso.

Daga baya Gwarzo ya bi Kwankwaso zuwa jam’iyyar NDC, inda tsohon gwamnan na jihar Kano ke mara wa Peter Obi baya a matsayin mataimakin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar a zaben 2027.

Haka nan shi ma kwamared Abdussalam ya samu tikitin tsayawa takarar gwamnan Kano a jam’iyyar, inda zai kalubalanci tsohon abokin tafiyarsa, wato gwamnan jihar Abba Kabir Yusuf.