Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Me dokokin Najeriya suka ce kan mallaka da amfani da jirgin naɗar hoto?
Fitaccen ɗan gwagwarmayar nan mai fafutikar kare haƙƙin bil'adama a Najeriya, Omoyele Sowore ya nuna damuwa kan kamu da jami'an DSS suka yi wa ƴarjaridar nan Zainab Sodiq, wadda ke ɗaukar rahotonnin ayyukan na Sowore.
Sowore ya yi ikrarin cewa ba an kama zainab domin aikinta ba ne, an kama ne domin shi, saboda jami'an na DSS sun san cewa tana da kusanci da shi.
Sai dai cikin wata sanarwa da hukumar DSS ta fitar, ta ce sun tsare ƴarjaridar ne kuma suna bincikenta kan mallaka da kuma amfani da jirgin ɗaukar hoto na duron ba tare da cikakken izini ba.
Sanarwar ta ƙara da cewa jami'an DSS da ke filin jirgin sama na Legas ne suka fara tsare Zainab a ranar 6 ga watan Yuli a kan hanyarta ta zuwa Abuja, bayan samunta jirgin ɗaukar hoto mai shawagi a sama ba tare da takardar shaidar amfani da shi.
Daga baya sun bar ta ta ci gaba da tafiya, amma sun shaida mata cewa ta je shalkwatarta da ke Abuja a ranar Laraba, domin amsa wasu tambayoyi.
"An kuma fara binciken. Kuma muna yin hakan ne bisa dokokin duniya da na Najeriya kan ƙa;idojin mafani da jirgin ɗaukar hoto ta sama, musamman game da batun karya dokokin sirri da tsaron al'umma,'' in ji sanarwar ta DSS.
To amma haramun ne mallakar duron da amfani da shi a Najeriya? Ga abin da masana shari'a ke cewa.
End of Ƙarin wasu labaran masu alaƙa
Dokokin sufurin sama ta Najeriya na 2023
Hukumar kula da sufurin sama ta Najeriya ce ke da alhakin lura da abubuwan da ke zirga-zirga a shafi sararin samaniyar ƙasar, ciki har da jiragen ɗaukar hoto da aka fi sani da duron, da jirage marasa matuƙa.
Sashe na 21 na Dokar ta 2023 ne ya yi magana kan buƙatar takardar shaida, da yin rajista da amfani da jiragen duron.
Dokar ta kara jiragen durun zuwa nau'uka daban-daban dangane da girmansu, akwai manya da matsakaita da ƙanana da ƴanƙanana da kuma mitsi-mitsi
Haka kuma amfani da jiragen na da nau'uka kamar: Wanda kowa zai iya yi, da wanda suka keɓanta ga wasu mutane da kuma waɗanda dole sai an yarje musu.
Wanan ne zai tantance ko mai amfani da jirgin zaio buƙaci izini ko a a kafain aiki da shi.
Ga wasu abubuwan da dokar ta ce:
Rajista:
- Mutum ba zai yi amfani da jirgin farar hula ba, ciki har da maras matuƙi (duron) hai sai ya fara yin rajista da hukumar kula da sufurin sararin samaniyar Najeriya (NCAA) sanna kuma ta ba shi takardar shaidar yin rajista.
- Dole ne wanda ya mallaki jirgin ko wanda ke amfani da shi ya zama shi ne ya yi masa rajistar da kansa
- Mutanen da aka yarje wa su mallaki jirgin ɗaukar hoton sun haɗa da: Ƴan Najeriya da ƴanƙasashen waje masu takardun shaidar zama na dindindin a Najeriya da kuma kamfanonin da suke yi rajista kuma suke harkokinsu a Najeriya, ko suke aiki da hukukomin Najeriya.
- Ɗan ƙasar waje na iya bai wa ɗan Najeriya ko wata hukuma ta gwamnati hayar jirgin ɗaukar hoton, kuma za a ba wa jirgin damar yin aiki muddin an yi masa rajista, tare da tabbatar da cewa takardar shaidar ta ƙunshi sunaye da adiresoshin masu shi da kuma waɗanda ke sarrafa shi.
Ƙa'idojin amfani da shi
- Dole ne masu amfani da jirgin ɗaukar hotonsu mallaki takardar shaidar samun damar amfani da shi.
- Ana sabunta wannan rajista bayan shekara biyar domin tabbatar da cewa masu amfani da shi na bin ƙa'idojin amfanin.
- Domin tabbatar da tsaro, hukumar NCAA ta wajabta cewa dole sai masu aiki da shi sun samu sahalewar jami'an tsaro da takardar shaidar amfani da jirgin shi kaɗai domin rage hatsarin amfani da shi wajen aikata miyagun laifuka.
Wuraren da aka hana amfani da jirgin ɗaukar hoto:
- Akwai wuraren da aka haramta wa jirgen ɗaukar hoto ta shawagi a samansu, kamar filayen jirage da sararin samaniyar wasu ƙasashen.
- Haka kuma an takaita wa jiragen ɗaukar hoto shawagi a sama mutane, ko shawagi a cikin daddare.
- Idan aka samu wani aukuwar hatsari ko karya dokar kariya, mai amfani da jirgi zai kai rahoton hakan ga hukumomin.
- Laifi ne wani ya yi amfani da jirgin hoto domin jefa wani abu da zai zama lahani ga mutane ko dukiyarsu.
- Ya kamata kowane jirgi ya yi rajista da inshora da zai iya biyan irin hatsarin da zai iya fuskanta.
- Laifi ne a yi amfani da jirgin ɗaukar hoto wajen leken asiri ko naɗar bidiyon mutane ko kadarorinsu b tare da izininsu ba.
Dokar ta NCAA ta 2023 ta kuma yi magana a fayyace kan ladabtarwar da za a yi wa mutumin da aka samu da karya dokokin.
Ko Zainab ta cika waɗannan ƙa'idoji?
Dangane da batun Zainab Sodiq, Omoyele Sowore ya ce jirgin ɗaukar hoton nasa ne ba na Zainab ba, yana mai cewa ita Zainab kawai taimaka masa ta yi wajen ɗauko shi daga Legas don kai masa Abuja.
Babu dai tabbas kan ko Sowore ya yi wa jirgin ɗaukar hoton rajista da hukumar NCAA, kamar yadda dokar amfani da shi ya tanada.
Haka kuma babu tabbas ko yana amfani da shi ba bisa ƙa'ida ba.
An samu ƙaruwar amfani da jirage masara matuƙa a Najeriya a fannoni da dama, kama daga naɗar film da fannin noma da tsaro da ma duba girman wata ɓarna kamar ambaliya.
A baya BBC ta taɓa yin wani labari na yadda wata ƙungiyar agaji ke amfani jirage marasa matuƙa wajen kai magunguna cikin sauri ga wasu ƙauyukan gaɓar ruwa a jihar Bayelsa da ke kudu maso kudancin Najeriya, domin tabbatar da mutane na samun magungunan da suke buƙata.