Muhammad ya sake zama sunan da aka fi sanya wa jarirai a Ingila da Wales

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Sunan Muhammad ya sake zama sunan da mahaifa suka fi saka wa ƴaƴansu maza a Ingila da Wales a shekarar 2025.

Hukumar ƙididdiga ta Ingila ce ta sanar da hakan a wani rahoto da ta fitar ranar Alhamis dangane da sunayen da aka fi sanya wa yara a shekarar da ta gabata.

Wannan dai shi ne karo na uku a jere da sunan na Muhamamd ke zama wanda aka fi sanya wa yara a Ingila da Wales - sunan ne ja-gaba a shekarun 2023 da 2024 da kuma 2025.

Muhammad, Mohammed ko Muhammed?

Bugu da ƙari, sunan na Muhammad ne ya kasance a sahun gaba a jerin sunayen yara maza a kowane wata a tsawon shekarar 2025.

Alƙaluman sun nuna cewa an sanya wa jarirai maza 5,957 suna Muhammad, yayin da sauran hanyoyin rubuta sunan ma suka kasance cikin sunayen da aka fi zaɓa.

Sunan Mohammed ya zo na 20 a jerin sunayen da aka fi sanya wa yara, inda yara 1,712 suka samu wannan suna.

Shi ma Mohammad ya zo na 55, inda aka sanya wa yara 895 wannan suna.

Me ya sa Muhammad ya zama ja-gaba?

Clare Green, wata ƙwararriya da ke rubuce-rubuce ga shafin sanya wa yara suna mai suna Nameberry, ta ce ba ta yi mamakin ganin sunayen Muhammad ya sake zama na farko a jadawalin sunayen da aka fi sanya wa yara ba.

"Sauye-sauye a saman jadawalin suna faruwa ne a hankali sosai, kuma da zarar wani suna ya zama sananne, yawanci yana ci gaba da zama sananne na dogon lokaci."

Ƙwararriyar ta kuma ƙara da cewa nason da sunayen ke yi ka iya zama ƙarin dalilin yaɗuwar sunayen.

"Sunaye na iya ƙara samun karɓuwa a hankali; idan mutane da yawa suna sanya wa 'ya'yansu wani suna, sauran iyaye ma suna ci gaba da jin sunan kuma za su fara son shi. Hakan kuma yana ƙara yaɗuwarsa kamar wutar daji."

Sauran sunaye

A jerin sunayen jarirai maza da aka fi sanyawa baya ga Muhammad, sunan Noah ne na biyu sai kuma Leo da Luca da Arthur.

Sauran da ke biye musu sun haɗa da Oliver da George da Oscar da Theodore da kuma Freddie.

Dangane kuma da sunan jarirai mata sunan Olivia ne ya zama kan gaba inda kuma sunan ya kwashe shekaru 10 a jere yana ɗaukar wannan kambi, inda aka saka wa yara mata 5,000 sunan.

Sauran da ke biye mata suna haɗa da Lily da Amelia da Isla da Florence da Freya da Poppy da Elisie da Ivy sai kuma Isabella.