Yaushe za a kubutar da daliban Borno da Kwara? — ADC

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

a Najeriya yayin da ake ci gaba da murnar kuuto daliban jihar Oyo, da ke kuu maso kudancin Najeriya, Jam'iyyar adawa ta ADC a Najeriya, ta yi kira gwamnatin kasar akan ta ƙara yin hoɓɓasa da azamar kamar yadda ta yi wajen kubutar da ɗaliban Oyo ga sauran dailban ƙasar da ke hannun 'yan bindiga.

Jam'iyyar ta ADC na ganin ya zama wajibi a kara mayar da hankali wajen tattara bayanan sirri, da karfafa hadin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro na kasar, da kokarin gano tushen matsalar tsaro don magance ta.

Faisal Kabiru, ɗaya ne daga cikin masu magana da yawun ADCn a Najeriya, ya shaida wa BBC cewa, abin da gwamnatin Najeriya ba wani abin gwaninta ba ne domin ta manta da wasu mutane da aka sace a wasu jihohin kasar.

Ya ce," Gwamnatin Najeriya ta yi biris da mutanen da aka sace a Kwara da Borno dama sauran mutanen da aka sace a wasu jihohin kasar, sam gwamnati ta nuna ba ta damu da su ba don koma maganarsu ba'a yi."

"Wannan shi ne kiranmu ga gwamnatin tarayyar Najeriya, yadda ta sanya idanu akan yadda aka kubutar da daliban Oyo , to su sauran wadanda ke hannun 'yan bindiga a yanzu me suka yi wa gwamnati?".In ji shi.

Mai magana da yawun jam'iyyar ta ADC, ya ce, "Ya kamata gwamnati ta sani kubutar da mutane ko tsare mutane ba iya bakin kokari ba ne, babban abin da ya rataya a wuyan gwamnati shi ne ta kare rayuka da dukiyoyin al'umma."

Ya ce," A gwamnatin Bola Tinubu matsalar tsaro ta zama abin da aka ma saba da shi, kuma hakan shi ne babban abin da ya jefa Najeriya cikin matsalar tattalin arziki sannan ya janyo tsadar abinci da ma rashin wadataccen abincin."

A ranar 10 ga watan Yulin 2026 ne aka kubutar da dukkan ɗalibai da malaman makaranta da aka yi garkuwa da su a ƙaramar hukumar Orire ta jihar Oyo da ke Kudu maso Yammacin Najeriya.

Na sace daliban ne a wani hari da ƴan bindiga suka kai kan makarantu a Jihar Oyo a ranar 15 ga Mayu, 2026, inda aka sace mutum 46 da suka haɗa da dalibai 39 da malamai 7.

A jihar Borno ma an kai makamancin wannan hari, inda aka yi awon gaba da ɗalibai sama da 40 su ma, amma har yanzu babu labarin sakinsu.

Lamarin hare-haren 'yan bindiga da satar mutane don neman kudin fansa sun fi kamari ne a yankin arewacin Najeriya, inda ba kasafai aka saba ganin hakan ba a kudancin kasar, wadda ke fama da matsaloli na tsaro.