Wace irin alaƙa ce tsakanin China da Rasha?

- Marubuci, Ankur Shah
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Editor, BBC Global China Unit
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 8
A yayin da suke tafiya cikin dandalin Tiananmen a birnin Beijing a watan Satumbar da ta gabata, Shugaban China Xi Jinping da Shugaban Rasha Vladimir Putin sun bayyana suna tattaunawa kan yiwuwar dashen gaɓoɓi zai iya tsawaita rayuwar ɗan Adam sosai.
"Za a iya ci gaba da dashen gaɓoɓin jiki ba tare da tsayawa ba. Duk tsawon lokacin da mutum ya rayu, yana ƙara zama kamar matashi, har ma yana iya kai wa ga wanda ba zai mutu ba." in ji mai fassarar Putin.
"Wasu na hasashen cewa a wannan ƙarni, mutane za su iya rayuwa har zuwa shekara 150," in ji mai fassarar Xi Jinping.

Asalin hoton, Kremlin Press Office/Anadolu via Getty Images)
Wannan wata tattaunawa ce da ta dace da shugabanni biyu masu ƙarfi, waɗanda suka bayyana juna a matsayin abokan kut-da-kut, kuma bayan jimillar shekaru 39 suna kan mulki, babu alamar suna shirin sauka.
Wannan ya ba da wani sabon haske kan dangantakar da mutane da dama ke ɗauka a matsayin wadda ba a cika fahimtarta ba. Wannan ɗan tattaunawa da ba a shirya ba na daga cikin ƙalilan da ke nuna irin dangantaka mai sirri sosai da ke tsakaninsu.
Putin zai koma Beijing a wannan makon, a daidai lokacin da ake cika shekaru 25 da rattaɓa hannu kan yarjejeniyar Kyakkyawar Maƙwabtaka da Haɗin kai tsakanin Rasha da China.
A yayin da Shugaban Amurka Donald Trump ya ziyarci Xi Jinping a makon da ya gabata, an tarbe shi da gagarumin liyafa mai cike da kayayyakin zinariya da kuma ziyara zuwa wani tsohon wurin ibada. Ziyarar Putin kuwa ta fi shiru, inda aka fitar da ƙaramin bayani tun kafin zuwansa.

Asalin hoton, EPA-EFE/REX/Shutterstock
Mai magana da yawun Kremlin ya ce suna fatan samun bayanai kai tsaye game da ganawar Trump da Xi Jinping.
Rahotanni sun ce Xi Jinping ya ambaci abokinsa Vladimir Putin ga Trump a makon da ya gabata, a lokacin da shugabannin biyu suka yayi tattaki a Zhongnanhai, wani wuri da aka saba rufe shi ga baƙi, inda aka yi dariya kan yadda Putin ya taɓa ziyartar wannan cibiyar siyasar Beijing.
A yayin da wasu a Washington ke fatan cewa Trump zai iya janye China daga Rasha, irin wannan fata na ƙara nuna kamar buri ne da ba shi da tushe mai ƙarfi.
China da Rasha sun sha bayyana dangantakarsu a 'yan shekarun nan a matsayin "abota mara iyaka". Amma wannan tambaya na da muhimmanci: menene ke gina wannan dangantaka, kuma shin za ta dawwama?
Ƙarkashin sharuddan China On Chinese terms
Masanin siyasa Alexander Gabuev ya bayyana cewa dangantakar China da Rasha ba ta da daidaito, domin China ce ke da rinjaye sosai. Ya ce yawancin yarjejeniyoyin da ake yi tsakanin su suna karkata ne bisa sharuɗɗan China, inda Rasha ke ƙara dogaro da Beijing.
A fannin tattalin arziki, China ita ce babbar abokiyar kasuwancin Rasha, yayin da Rasha ke da ƙaramin kaso a kasuwancin China.
Takunkumin Yammacin duniya ya ƙara tilasta Rasha dogaro da China, musamman wajen fasaha da kayayyakin masana'antu.
Kamfanoni kamar Huawei sun faɗaɗa aiki a Rasha bayan takunkumi daga Yamma, wanda ya sa China ta zama babbar hanyar Rasha wajen samun fasaha da ilimi.

Asalin hoton, EPA/Shutterstock
Tun bayan mamayar Ukraine a 2022, Rasha ta ƙara dogaro sosai da China wajen samun kayayyakin fasaha da sassan da take amfani da su a harkokin soji. Rahotanni sun nuna cewa yawancin fasahar da ke ƙarƙashin takunkumi da Rasha ke shigo da su daga China suke fitowa, wanda ya ƙaru cikin lokaci.
Wannan ya sa dangantakar Moscow da Beijing ta zama marar daidaito, inda Rasha ke dogaro fiye da China. Duk da haka, Rasha na ƙoƙarin nuna cewa ba ta son zama ƙasa mai bin umarnin Beijing.
Jami'i Dmitry Trenin ya ce Rasha tana ganin kanta a matsayin babbar ƙasa, don haka ba za ta zama ƙaramin aboki ba ko mai bin umarni kai tsaye ba. Amma duk da wannan matsayi, Rasha ba ta da wasu zaɓuɓɓuka masu ƙarfi kamar China, musamman bayan takunkumin Yamma.
A halin yanzu, China na da muhimmiyar rawa a kasuwancin Rasha, amma ƙarfin siyasar Rasha ne ke hana China yin rinjaye kai tsaye a kanta.

Asalin hoton, AFP via Getty Images
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A cewar Marcin Kaczmarski na Jami'ar Glasgow, China ta fahimci cewa akwai babban rashin daidaito a dangantakarta da Rasha, amma tana guje wa duk wani mataki da zai iya tayar da hankali ko haifar da rikici a cikin Rasha. Saboda haka, ba ta matsa mata lamba kai tsaye.
Haka kuma, Alexander Gabuev ya ce ko da China ta yi ƙoƙarin tilasta wa Rasha wani abu, Rasha ba ƙasa ba ce da za ta karɓa cikin sauƙi. Ya kawo misali lokacin ziyarar Xi Jinping a Moscow a 2023, inda aka ce ya gargadi Putin kada ya yi amfani da makaman nukiliya a Ukraine, amma jim kaɗan bayan haka Rasha ta ɗauki matakin tura makaman nukiliya zuwa Belarus, abin da aka gani a matsayin nuna ƙin matsin waje.
Yaƙin Ukraine ya sa Rasha ta zama mai nauyi a wasu fannoni, amma kuma ya ƙara darajarta ga China, musamman a fannin soja da gwajin fasaha. Rasha na kuma samar da muhimmiyar albarkatun makamashi ga China.
Putin ya kuma bayyana cewa ƙasashen biyu na shirin ƙara zurfafa haɗin gwiwa a fannin mai da gas, wanda zai ƙara ƙarfafa dangantakarsu.

Asalin hoton, Bloomberg via Getty Images
Wataƙila yana nufin bututun iskar gas na Power of Siberia 2, wanda kamfanin Gazprom da kamfanin man China suka ruwaito cewa sun ƙulla yarjejeniya ta farko bayan shekaru na tattaunawa da suka dakata.
Idan aka kammala gina bututun, zai iya zama babban sauyi, domin zai riƙa isar da kusan biliyan 50 na cubic metres na iskar gas daga Rasha zuwa China ta hanyar Mongolia.
Ga China, yayin da rikici ke ci gaba a mashigin Hormuz, dogaro da makamashin Rasha na fara nuna amfani. Wannan ba batun farashi kaɗai ba ne, har ma da tabbatar da tsaron makamashin cikin gida a duniya da ke ƙara zama mai rashin tabbas.
China da Rasha: Abokan hulɗa ba ƙawaye ba
Masana sun bayyana cewa dangantakar China da Rasha ba ƙawayen juna bane sai dai abokan hulɗa.
Wannan yana nufin kowace ƙasa ba ta tilasta bin umarnin ɗaya ba, wanda ke ba dangantakar ƙarfin jure matsaloli.
Bobo Lo, tsohon mataimakin shugaban ofishin jakadancin Ostireliya a Moscow, ya ce wannan ne ya sa dangantakar ke ci gaba duk da hasashen cewa za ta rushe.
Masu sharhi na Yamma sun sha kallon dangantakar a hanyoyi biyu: ko dai a matsayin ƙawayen da ke gwagwarmaya da Yamma, ko kuma abokan hulɗa wanda haɗin gwiwarsu me rauni ne da ke gab da rushewa. Amma a zahiri, dangantakar ta zama mai muhimmanci kuma ɓangarorin biyu suna more juna, har ma idan dangantakarsu da Yamma ta inganta, suna da dalilai masu ƙarfi na ci gaba da hulɗa.

Asalin hoton, Bloomberg via Getty Images
China da Rasha na da dalilai da yawa da ke sa dangantakarsu ta ƙara ƙarfi. Daga cikin su akwai kan iyakar da ke tsakanin su mai tsawon kilomita 4,300, wadda a baya ta kasance wajen tashin hankali. Haka kuma, tattalin arzikinsu ma inda Rasha na fitar da mai, iskar gas da albarkatun ƙasa, yayin da China ke samar da babbar kasuwa ta masana'antu.
Bugu da ƙari, ƙasashen biyu na da ra'ayi iri ɗaya na adawa da tsarin duniya da Amurka ke jagoranta. Ba kamar ƙasashen Yamma ba, ba sa yawan sukar juna kan batutuwan cikin gida ko na kare haƙƙin ɗan adam.
Misalai sun haɗa da batun Xinjiang a China da kuma mutuwar ɗan adawar Rasha Alexei Navalny, inda duk da suka daga Yamma, Beijing da Moscow ke watsi da su. Masana sun ce wannan rashin tsoma baki a harkokin juna ya sa dangantakarsu ta zama kamar haɗin gwiwa mai fa'ida ga bangarorin biyu a matakin ƙasa da ƙasa.

Asalin hoton, Getty Images
Masana sun ce kyautata dangantaka tsakanin China da Rasha tana da dogon tarihi, tun daga zamanin shugabannin Tarayyar Soviet kamar Andropov, Chernenko, Gorbachev har zuwa Yeltsin. Wannan ya nuna cewa kusanci tsakanin ƙasashen ba sabon abu ba ne, sai dai ya ci gaba a sabon salo na zamani.
Wani mai sharhi daga China ya ce hoton da ake nunawa na cewa ƙasashen biyu ba sa rabuwa sau da yawa ana yin sa ne domin nuna haɗin kai da kwanciyar hankali. A zahiri, ana amfani da wannan dangantaka a matsayin kayan siyasa don rage bambance-bambancen ra'ayi da ke tsakanin su.
Duk da cewa duka biyun na adawa da abin da suke kira rinjayen Yamma, hanyoyinsu sun bambanta. Rasha na son tsarin duniya da zai kauce wa Amurka gaba ɗaya, yayin da China ke bin hanya mai hankali da jinkiri, tana ƙoƙarin guje wa rikici kai tsaye da Amurka domin ta ci gaba da tattaunawa da kuma kare muradunta na dogon lokaci.
Ɓangaren mutane a dangantakar China da Rasha
Duk da cewa ana yawan tattauna dangantakar China da Rasha a fannin siyasa da tsaro, akwai kuma alaƙar ɗan adam tsakanin al'ummominsu, musamman ta hanyar hulɗar jami'ai da tafiyoyin aiki a matakin gwamnati. Shugabanni kamar Vladimir Putin da Xi Jinping sun nuna kusanci a fili, inda Putin ya kai ziyara China sau da dama, kuma jami'an ƙasashen biyu na yawan aiki tare fiye da na wasu ƙasashe.
Sai dai tsohon jami'in diflomasiyyar Birtaniya a China, Charles Parton, ya ce wannan kusanci a matakin shugabanni ba lallai ya nuna kusanci tsakanin al'umma ba. Ya ce ba a ganin sha'awar al'ummar China na rayuwa ko karatu a Rasha kamar yadda ake gani a Ƙasashen Yamma.
Haka kuma, ya ce yawancin Rasha, idan aka ba su dama, sun fi son saka jari ko rayuwa a Ƙasashen Yamma kamar Paris ko London maimakon Beijing, abin da ke nuna cewa kusanci tsakanin gwamnati da gwamnati ya fi na mutane da mutane ƙarfi.

Asalin hoton, China News Service/VCG via Getty Images
Ba kowa ne ke yarda da wannan ra'ayi ba. Gabuev yana cewa hulɗar mutane tsakanin Rasha da China tana ƙaruwa cikin sauri, musamman saboda takunkumin Yammacin Turai da ƙuntata wa Rasha samun biza zuwa Turai, wanda hakan ke sa yawancin 'yan Rasha su juya zuwa China.
Yanzu ya zama sauƙi ga 'yan Rasha su je China, domin babu buƙatar biza tsakanin ƙasashen biyu. Ana samun jirage da dama daga Moscow zuwa manyan biranen China a kowace rana, kuma tafiya tana ɗaukar sa'o'i kaɗan kawai.
Haka kuma, 'yan Rasha suna ƙara amfani da wayoyin China da motoci na China, musamman bayan takunkumin Yamma.
A cewar Gabuev, wannan sauƙin tafiye-tafiye, amfani da kuɗi, da shirye-shiryen musayar ilimi da bincike suna ƙara kusantar da al'ummomin ƙasashen biyu fiye da da.

Asalin hoton, Sputnik/ Kremlin/ PA/Shutterstock
Ko da yake akwai rashin daidaito da ke ƙaruwa a dangantakar Moscow da Beijing, wanda zai iya zama rauni a dogon lokaci, duk wani hasashen cewa dangantakar za ta rushe nan kusa yana da nisa.
Duk da bambance-bambancen da ke tsakanin su, Lo ya ce haɗin gwiwar China da Rasha tana da ƙarfi kuma tana ci gaba da ɗorewa. A cewarsa, ɓangarorin biyu sun fahimci cewa wannan haɗin gwiwa yana da matuƙar muhimmanci kuma ba za a iya bari ya lalace ba, musamman saboda babu wasu hanyoyi masu sauƙi da za su iya maye gurbinsa idan suka daina aiki tare.









