Coronavirus: An samu 'yan wasa biyar da cutar korona a Spaniya

Lionel Messi

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, A karon farko Lionel Messi ya yi atisaye a Barcelona ranar Juma'a tun bayan ata biyu
An wallafa

'Yan wasa biyar masu buga gasar Spaniya babba da karama na dauke da cutar korona in ji mahukunta wasannin.

Kawo yanzu ba a bayyana sunan 'yan kwallon da suka kamu da annobar ba, sai dai an killace su.

Za kuma a ci gaba da gwada su, kuma har sai sun warke kafin su koma atisaye cikin sauran 'yan wasa.

A makon jiya mahukuntan La Liga suka fara auna lafiyar 'yan kwallo da nufin shirye-shiryen fara atisaye don karkare kakar 2019-20.

Mahukuntan gasar La Liga na fatan ci gaba da gasar shekarar nan ba tare da 'yan kallo ba a cikin watan Yuni.

A makon jiya ne wasu kungiyoyin Spaniya suka fara atisaye ciki har da Barcelona.

Spaniya daya ce daga kasashen da cutar korona ta kassara a Turai, inda mutum 224,390 suka kamu da annobar sannan ta hallaka 26,621 kawo zuwa 10 ga watan Mayu.