Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Me ya sa Amurka da Iran suka gaza cimma matsaya a Pakistan?
Wakilan Amurka da na Iran sun tashin baram-baran ba tare da cimma matsaya ba a tataunawar da suka a Pakistan da nufin kawo ƙarshen yaƙin da ƙasashen biyu ke gwambazawa.
Tun da farko an cimma yarjejeniyar tsagaita wutar wucin gadi ta mako biyu bisa taimakon Pakistan, inda ƙasashen biyu suka amince da zama domin lalubo hanyoyin da za su kawo ƙarshen yaƙin.
Ɓangarorin biyu sun gabatar da sharaɗɗan da suke ganin sai an amince da su kafin kawo ƙarshen yaƙin.
Amurka, wadda ke samun goyon bayan Isra'ila a yaƙin ta gabatar da sharuɗɗa 15, yayin da Iran ta gabatar da 10.
To sai dai ɓangarorin biyu ba su samu matsaya ba, lamarin da ya sa tattaunawa ta watse ba tare da wata matsaya ba.
Me ya janyo rashin matsayar?
Ɓangarorin biyu sun bayar da dalilai masu cin karo da juna, a matsayin abin da ya sa aka gaza cimma matsaya a zaman nasu ƙarƙashin shiga tsakanin Pakistan.
Sun kuma zargi juna da haifar da haifar da gaza cimma matsayar tattaunawar.
Me Amurka ta ce?
Amurka ta ce ta gabatar da buƙatu masu "sauƙi" kuma "waɗanda suka dace", amma Iran ta ƙi amincewa.
Mataimakin shugaban Amurka, JD Vance ya ce shugaba Trump ya tura shi wakilci Pakistan tare da ba shi umarnin ''dagewa domin ganin an cimma matsayar zaman lafiya.''
Ya ce ''Mun yi duk abin a ya dace, amma mun gaza cimma wata matsaya saboda wata buƙata mai sauƙi da muka gabatar, wadda ita ce muke ganin ta fi dacewa da kowa''.
A jawabin da ya gabatar bayan kammala zaman, Mr Vance ya ce Amurka ta fayyace sharuɗɗanta, kuma ta sanar ƙarara cewa babu gudu ba ja da baya a kan su, ''amma Iran ba ta amince da buƙatun namu ba''.
Ya ce ''mun shafe sa'oi muna tattaunawa, amma ina baƙin cikin sanar da ku cewa ba mu cimma matsaya ba''.
Me Iran ta ce?
Kafofin watsa labaran Iran ɗin sun rawaito cewa buƙatun da Amurka ta gabatar da suka kira marasa kan gado ne suka hana samun ci gaba.
Sun ce Amurka ta nemi Iran ta yi watsi da hatta haƙƙinta na samar da shirin nukiliya na farar hula don samar da magunguna da kuma wutar lantarki, wani abu Iran ɗin ta ce ya yi kama da yin saranda ko miƙa wuya.
Wani abu da ya sake haifar da saɓanin shi ne batun matsayin mashigar Hormuz, da kuma batun tsagaita wuta a Lebanon.
"Duk da ƙoƙarin da wakilan Iran suka yi domin ganin komai ya tafi yadda ya dace, wasu ''buƙatu marasa amfani'' daga ɓangaren Amurka sun sa an gaza ƙulla yarjejeniya.
Da haka zaman tattaunawar ya tashi,'' a cewar kafar yaɗa labaran Iran ta IRIB a wani saƙo da ta wallafa a Telegram.
Babu dai tabbacin ko za a ƙara wani yunƙuri a cikin makonni biyun tsagaita wuta da aka ƙula, ko kuma akwai shirin gudanar da wani zaman na daban.
Tuni dai tawagogin ƙasashen biyu suka kama hanyar komawa ƙasashensu bayan zaman tattauanwar da bai yi nasara ba.