Shin Mahmoud Ahmadinejad zai zama raba-gardama ne a yaƙin Iran?

Asalin hoton, Isna
- Marubuci, Saeed Jafari
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Journalist
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 7
''Ya kamata a fahimci cewa wannan gwamnatin da aka tsana ta kusa kifewa. Da yardar Allah ta kusa watsewa, kuma babu wanda ya isa ya cece ta. Wannan mulkin ta kusa zuwa karshe kuma an kusa daina jin duriyarta a ban kasa."
Wannan jawabi ne na Mahmoud Ahmadinejad, daya daga cikin fitattun mutanen da suke tsananin adawa da Isra'ila.
Yanzu sunansa ya sake cigaba da amo a game da yakin Iran na wannan lokacin. A wani rahoton New York Times, an bayyana cewa kafin a fara yakin, Amurka da Ira'ila sun yi nazarin yiwuwar amfani da Ahmedinajad a yakin, da kuma saka shi a cikin maganar sabuwar gwamnatin Iran.
Mahmoud Ahmadinejad da makusantansa dai har yanzu ba su ce komai ba. Kuma yanzu babu cikakken bayani game da inda yake, da lafiyarsa.
Rahoton na New York Times ya dauki hankali matuka, inda har masana a Isra'ila da Amurka suka rika tattaunawa cikin mamaki.
Shin me ya sa Amurka da Isra'ila za su yi amfani da mutumin da tsawon lokaci yake adawa da su?

Asalin hoton, Getty Images
Ahmadinejad: Maƙiyin da ke da amfani ga Isra'ila?
Domin fahimtar labarin da kyau, dole mutum ya yi tariyar shekarun baya na yadda Ahmadinejad ya fara tashe a siyasar Iran.
An zabe shi ne a matsayin Magajin Garin Tehran a shekarar 2003.
Ya fara mulki ne da taken tabbatar da adalci da yaki da rashawa, amma cikin kankanin lokaci sai idon duniya ta koma kansa, ba wai don mulkinsa a gida ba, sai jawabinsa kan adawa da kafa yahudawa zalla.
A watan Oktoban 2005, a taron "Duniya ba tare da masu akidar Yahudawa zalla ba" Ahmadinejad ya ce za a yi rayuwa ba tare da Amurka da Isra'ila ba.
Wasu jami'an Isra'ila dai sun yi amannar akwai wasu matakai na Ahmadinejad da suka amfanar da kasar. A 2008 tsohon shugaban hukumar leken asirin Isra'ila Mossad Ephraim Halevi ya bayyana shi da "babbar kyautar Iran ga Isra'ila,' domin a cewarsa kalamansa ne suka Isra'ila ta dauki barazanar Iran da gaske.
Wannan ya sa masu sukar Ahmadinejad suke tambayar shin matakansa Isra'ila suka amfanar ko Iran?
Sai dai masoyansa na cewa ya dauki matakai masu muhimmanci domin inganta Iran da shirya ta, kuma burinsa shi ne kasar ta iya fuskantar Isra'ila da kasashen yamma ba taimakon su ba.
Sauya salo bayan yaƙi
Sai dai Mahmoud Ahmadinejad ya canja salo bayan ya kammala mulki. Ya samu sabani da Ali Khamenei, sannan ya koma gefe har ta kai yana iya sukar wasu matakan na gwamnati.
Sai dai duk da haka ya cigaba da kasancewa a kwamitin kwararru na bayar da shawara na kasar, kuma bai fuskanci kalubale sosai ba kamar wasu tsofaffin jagororin kasar ba.
A cikin shekarun ne ya sauya salo a kafofin sadarwa, inda ya fara wallafa sako da Ingilishi
Har ya taba taya kungiyar kwallon kafa ta Jami'ar Michigan murnar lashe kofi, sannan ya taba tsakuro baitocin wakokin Tupac Shakur dan Amurka.
Ya ma taba Yabawa da shugaban Amurka Donald Trump bisa abin da ya kira "yaki da rashawa a siyasar Amurka."

Asalin hoton, Getty Images
Raz Zimet, daraktan abubuwan da suka shafin Shi'a da Iran a cibiyar nazarin harkokin tsaro ta Isra'ila, ya ce ko a lokacin da Ahmadinejad yake mulki, mutum ne mai fuska biyu.
Ya ce, "mutum ne da yake bayyana cewa yana kiyayya da Isra'ila, amma a wani bangaren yake daukar matakan da suke sabani da abin da yake da'awa a kai."
Mr. Zimet ya kara da cewa Ahmadinejad na ta kokarin nuna wa duniya cewa shi yanzu mai saukin ra'ayi ne.
Sai dai ya kara da cewa har yanzu kididdiga na nuna cewa yana da dimbin masoya a sassan Iran din. Sai dai duk da haka sauya tsarin mulkin kasar zai yi wahala ganin irin adadin mutanen kasar na kusan miliyan 90
Ya kara da cewa babbar matsalar ita ce Ahmadinejad ba shi da wata kungiya mai karfi, sannan ba shi da goyon bayan dakarun juyin-juya-hali.
Tafiye-tafiye masu ɗaukar hankali
Ana kuma tambayoyi game da yanayin tafiye-tafiyensa. Wata mujalla mai suna New Lines ta ruwaito a ranar 5 ga Agustan 2025 cewa Ahmadinejad ya yi tafiya zuwa Guatemala da Hungary, lamarin da wasu ke ganin akwai alamar tambaya.
Ana dai ganin wuraren da ya ziyarta duk suna da na kut da kut da Isra'ila.
Ahmadinejad ya ziyarci Guatemala a 2023, kuma kasa ce da ta mayarda ofishin jakadancinta zuwa Jerusalem daga Tel Aviv bayan Amurka . Sannan Firaministan kasar na wancan lokacin, Viktor Orban na kusa ne da Isra'ila.
Kwana shida bayan ziyarsa a Budapest ne Isra'ila ta fara kaddamar da hare-hare a Iran.
Duk da cewa babu cikakkiyar hujjar alakanta al'amarin biyu, wasu na ganin akwai alamar tambaya.

Asalin hoton, Getty Images
Rahoton mujallar The Atlantic
Kafin rahoton New York Times, akwai mujallar The Atlantic a Amurka da ta ruwaito an kai hari a gidan Ahmadinejad a Tehran.
Sai rahoton ya bayyana cewa ba a kai harin domin a kashe shi kamar yadda makusantansa suka bayyana.
Rahoton ya kara da cewa an kai hari ne kan jami'an tsaron da suke kusa da gidan, domin a cewar su, suna sa ido sosai kan harkokin sa.
Rahoton na New York Times ya kara fadada wannan bayanin ne, domin rahoton ya nuna cewa Ahmadinejad na same da shirye-shiryen Amurka na kifar da gwamnatin kasar.
Sai dai mujallar ta kara da cewa daga bisani an bar shi a baya a shirye-shiryen.
Wannan ya sa lamarin ke da daure kai. Shin idan ya san da shirin kai harin, shin ta wacce hanya ya kwarmata bayaninga hukumomin kasar?
Idan kuma bai da masaniya, me ya sa masu shirye-shiryen suka yi tsammanin zai taka rawar?
Wadannan tambayoyin ba su da cikakkiyar amsa.
Abubuwan da ke ɗaure wa masanan Amurka kai
Masanan Amurka guda uku da suka zanta da BBC sun bayyana da wahala a ce Amurka da Isra'ila na da burin mayar da Ahmadinejad mulki.
Max Abrahams, masanin siyasa a Jami'ar Northeastern ya ce an yada labaran karya sosai a game da yakin Iran.
Ya ce zai yi wahala a ce Ahmadinejad wanda ya yi five wajen adawa da Isra'ila kuma ya yi kokari wajen inganta nukilyar Iran ne Amurka za ta so ya koma mulki.
Shi ma Ilan Berman ya ce zai yi wahala a iya fahimta tare da cewa akwai amfani da Ahmadinejad a cikin tsare-tsaren Amurka da Isra'ila.
A nasa bangaren, Michael Rubin, a wanda tsohon jami'in Pentagon ne, ya ce labarin kanzon kurege ne kawai, sannan ya ce New York Times ya yi amfani da wasu wadanda ba a so a bayyana su da yawa a rahoton.

Asalin hoton, khamenei.ir
Suka daga Isra'ila
Ba kamar masana daga Amurka ba da suka bayyana rashin aminta da batun, wasu masana da 'yanjarida a Isra'ila a Isra'ila cewa suke idan har akwai wannan alakar, ke nan Isra'ila ba ta san yanayin mulkin Iran ba
Danny Citrinovich, wani masani ne a cibiyar nazarin harkokin tsaro a Isra'ila, ya wallafa a shaguna na X cewa akwai rashin fahimtar yanayin mulkin Iran da yanayin mutanen kasar a yunkurin amfani da Ahmadinejad a yakin.
Citrinovich ya bayyana cewa matukar ana so a mayar da Ahmadinejad mulki, to sai an wargaza dukkan bangarorin mulki na Iran.
Sai dai ya ce "hakan banzai taba yiwuwa ba ta hanyar amfani da jiragen sama da soji."
Yossi Melman, fitaccen dan jarida ne kuma mai sharhi kan al'amuran yau da kullum ya ce "labarin kanzon kurege ne."
Raz Zimet, ya kara da cewa mulkin Iran na da matakai da bangarori da yawa, sannan yanayin mutanen kasar na da daure kai.

Asalin hoton, Getty Images
Me ya sa aka dawo da maganar Ahmadinejad?
A yanzu tambayar ita ce me ya sa ake maganar Ahmadinejad?
Watakila a samu amsar idan aka yi nazarin wasu abubuwa guda uku a game da shi: Daukaka da tarihin da kuma nesanta kansa da ya dan yi daga jagoran addinin Iran.
Ahmadinejad fitaccen mutum ne sosai a fading Iran kuma ya fahimci yanayin kasar sosai da yanayin mulkinta.
Sannan kuma ya tana samun sabani da jagoran addinin kasar.
Masana na ganin wadannan abubuwan ne suka sa ya zama wanda zai fi saukin amfani da shi a wannan yanayi da ake ciki.
Na dole su yi amfani da shi domin ya kasance abokinsu ba, sai dai kawai a matsayin wanda zai musu aiki na wucin-gadi.
Sai dai masana na nanata cewa Ahmadinejad na da wasu kalubalen da za su yi nasa cikas.
Sun bayyana cewa ba shi da karfin fada a ji, sannan ba shi da goyon bayan sojoji da dakarun juyin-juya-hali.











