Abin da sabon rahoton Amurka ya ce kan Fulani a Najeriya

Asalin hoton, Getty Images
Wani rahoton Amurka ya yi iƙirarin cewa Fulani masu gwagwarmaya da makamai na ci gaba da gagarumar mamaya a gonakin Kiristoci da kai miyagun hare-hare a kan wuraren addinan Kiristanci da na Musulmai.
Ya ce a 'yan shekarun nan, masu gwagwarmaya da makamai daga tsatson Fulani sun tafka miyagun hare-hare a kan al'ummomi da ba lallai kawai Kiristoci ba a Najeriya.
Ya ce da yawan ƙungiyoyin Fulani 'yan ta-da-ƙayar-baya na ƙaddamar da hare-hare, amma akwai wasu waɗanda lokaci-lokaci suna haɗa gwiwa da gungun 'yan fashin daji, da kuma sanannun ƙungiyoyin 'yan ta'adda don yaɗa wata fassarar addinin Musulunci ta tarzoma.
Najeriya, musamman yankin arewacinta na fama da rikice-rikice masu nasaba da ƙabilanci ko addini.
A baya-bayan nan shugaban Amurka Donald Trump ya yi zargin cewa ana "gallaza wa Kiristoci" a Najeriya, zargin da hukumomin ƙasar suka musa.
Tun farko rahoton wanda Hukumar Amurka kan tabbatar da ƴancin addinai a duniya ta wallafa ya ce ya yi nazari ne a kan rawar da Fulani 'yan ta-da-ƙayar-baya ke takawa wajen taɓarɓarewar ƴancin addinai a Nijeriya, ta hanyar fayyace duk wani tudu da gangare na rikice-rikicen al'ummomi Musulmai da Kiristoci a baya-bayan nan da kuma ci gaba da keta 'yancin gudanar da addini da Fulani masu tafka aika-aika ke yi.
Sai dai ƙungiyoyin Fulani a Najeriya sun sha musanta zargin da ake yi musu na shiga ayyukan laifi.
A wata tattaunawa da ya yi da BBC cikin watan Fabarairu, shugaban ƙungiyar makiyaya ta Najeriya - MACBAN - Baba Othman Nganzerma ya bayyana Miyetti Allah da kasancewa ƙungiyar masu sana'ar kiwo, ba tare da la'akari da addini ko ƙabila ba.
Ya ce ya yi mamakin yadda ƙasar Amurka ta kira sunan ƙungiyar a wani rahoto da ta fitar tana neman a sanya wa ƙungiyar takunkumi.
''Mu a tarihin ƙungiyarmu hukumomin Najeriya ba su taɓa zarginmu da wani laifin tallafa wa ta'addanci ko matsalar tsaro a Najeriya ba'', in ji Nganzerma.
Rahoton na Amurka a ɓangare ɗaya ya yi bayani game da ƙoƙari da gazawa daga ɓangaren gwamnatin Najeriya da ƙungiyoyin fararen hula wajen inganta haɗin kai da kyautata tsaro da rage salo-salo na ayyukan tashin hankali.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Ya ce alu'mmar Fulani ƙabila ce mai rinjayen Musulmai da suka fi yawa a arewacin Najeriya da kuma sauran ƙasashen Afirka ta Yamma masu maƙwabtaka, inda yawansu ya kai miliyan 14 da rabi a cikin jama'ar Najeriya mai mutum fiye da miliyan 242.
Kiwo in ji rahoton shi ne muhimmiyar sana'ar Fulani da yawa kuma shi ne abin da aka fi sanin su da shi sai dai suna fuskantar tsangwama saboda hakan.
Rahoton ya ce aƙidun tashin hankali na addini da ƙaruwar ƙarancin albarkatun ƙasa da gasa da bunƙasar yawan jama'a da talauci da sauran matsaloli sun cusa al'ummar Fulani cikin matsalolin rashin kwanciyar hankalin Nijeriya.
Ya yi ƙiyasin cewa Fulani 'yan ta-da-ƙayar-baya mai yiwuwa su 30,000 ne ke tafka aika-aika a faɗin Najeriya, inda asali suka fi zama a arewa maso yamma kafin su fara ƙaura zuwa yankin Arewa ta tsakiya, da kuma ƙara danganawa kudu.
Ya ce tashin hankalin Fulani 'yan ta-da-ƙayar-baya ya janyo kashe-kashe mafi yawa a tsakanin mabiya addinai daban-daban a Nijeriya a shekarar 2025, idan aka kwatanta da hare-haren ƙungiyoyin 'yan ta-da-ƙayar-baya da da gungun masu aikata laifuka.
Rahoton na Amurka ya yi zargin cewa Fulani mahara ba su bar Musulmai ba, kuma suna kai farmaki kan garken shanu sannan su ƙaddamar da hari a kan garuruwan Musulmai waɗanda ba Fulani ba.
Haka zalika in ji rahoton da yawan 'yan ta-da-ƙayar-bayan suna kai hari kan garuruwan Kiristoci a yankin Arewa ta tsakiyar Najeriya, sannan kuma ana ganin ƙaruwar lamarin a jihohin kudu, inda suke ƙona gidaje da coci-coci kuma suna satar mutane don yin garkuwa da su tare da aikata fyaɗe da aikata kisan kai.
Rahoton ya yi zargin cewa hare-haren Fulani 'yan ta-da-ƙayar-baya sun tilasta wa mutum miliyan 1.3 a yankin Middle Belt tserewa daga muhallansu.
Da gaske ƙungiyoyin Miyetti Allah na da alaƙa da ta'addanci a Najeriya?
Masanin tsaro a Najeriya, kuma shugaban kamfanin Beacon Consulting and Intelligence Limited mai nazari kan tsaro a yankin Sahel, Kabiru Adamu ya ce ƙungiyoyin biyu ba sa cikin waɗanda ke haifar da matsalar tsaro a Najeriya.
''Dalili kuwa shi ne akwai dokar hana yaɗuwar ta'addaanci ta 2022 a Najeriya, dokar ce ke lura da komai da ya shafui ta'addanci, kuma a ƙarƙashin dokar akwai wasu ƙungiyoyi shida da gwamnati ta ayyana a matsayin ƙungiyoyin ta'addanci, kuma a duka shidan babu wata ƙungiyar Fulani a ciki,'' in ji shi.
Haka kuma masanin tsaron ya ce a ƙarƙashin dokar akwai jerin wasu ƙungiyoyi 135 da aka ayyana da cewa sun taimaka wa ayyukan ta'addanci ta hanyar kuɗi ko wasu hanyoyin.
''To kuma duka cikin wannan jeri babu ɗaya daga cikin ƙungiyoyin Miyetti Allah ko Kautal Hore a cikinsu,'' kamar yadda ya yi ƙarin haske.
Ya kuma ce bisa binciken da kamfaninsa yake yi sun gano cewa ƙungiyoyin - da ke neman Amurka ta ayyana Najeriya cikin jerin ƙasashen da ake gallaza wa Kiristoci - sun sha zargin ƙungiyoyin Fulani da hannu a kashe-kashe Kiristoci, kodayake babu wata shaida da suka gabatar kan hakan.











