KAI TSAYE, Conte ya bar Napoli shekara ɗaya tsakani da lashe Serie A

Wannan shafi ne da zai ke kawo muku labaran wasannin BBC Hausa daga Litinin 25 zuwa Lahadi 31 ga watan Mayun 2026.

Taƙaitattu

  • Conte ya bar Napoli shekara ɗaya tsakani da lashe Serie A
  • Messi ya ji rauni, ko zai shafi zuwansa gasar kofin duniya?
  • Pabregas ya kai Como Champions League a karon farko a tarihin ƙungiyar
  • United da Arsenal da PSG na son Fernandes, AC Milan za ta riƙe Modric
  • Iraola ya yi ban kwana da Bournemouth, bayan samun gurbin Europa League
  • Rangers ce ta lashe kofin Premier League na Naigeria na bana
  • Ku shiga zaurenmu na BBC Hausa WhatsApp
  • Djokovic ta tirki rawa bayan kai wa zagaye na biyu a French Open
  • Za ku iya tafka muhara a shafnmu na sada zumunta a BBC Hausa Facebook

Rahoto kai-tsaye

Mohammed Abdu

  1. Rangers ta amince da ɗaukar Lawrence Shankland, Rangers

    Ƙungiyar Rangers ta cimma yarjejeniya da Heart of Midlothian kan ɗaukar ƙyaftin ɗinsu, Lawrence Shankland da zarar an kammala yi masa gwajin koshin lafiya da za a yi masa a kwanaki masu zuwa.

    Ɗan wasan na tawagar Scotland, wanda aka dade ana danganta shi da komawa Ibrox, ana sa ran zai zama cefanen farko na sabon koci, Danny Rohl a wannan bazarar.

    Shankland mai shekaru 30 ya taka muhimmiyar rawa wajen jagorantar Hearts zuwa matsayi na biyu a wannan kakar.

    Tun zuwansa Hearts a 2022, ya zura ƙwallaye 88 a wasa 171 da ya buga wa ƙungiyar. Haka kuma, yana cikin ƴan wasa mafi zura kwallaye a Scottish Premiership tun bayan fara gasar a 2013.

    A jimlace kuma, Shankland ya zura kwallaye 236 a wasanni 494 da ya buga a matakin ƙungiya, sannan ya zura kwallaye huɗu a wasa 18 da ya buga wa tawagar Scotland.

    Live

    Asalin hoton, SNS

  2. , Daga Jaridu

    Kyaftin din Tottenham Cristian Romero, mai shekara 28, zai so hadewa da dan kasarsa Argentina, Diego Simeone a Atletico Madrid. (Teamtalk)

    Ana sa ran dan bayan Crystal Palace Maxence Lacroix, mai shekara 26, zai bar kungiyar a bazara, inda kungiyoyin Firimiya da yawa ke son dan wasan na Faransa.(RMC Sport)

    Tottenham na duba yuwuwar neman mai tsaron ragar Benfica Anatoliy Trubin, dan Ukraine mai shekara 24, a bazara. (A Bola)

    Darektan wasanni na AC Milan Igli Tare na da kwarin gwiwa cewa tsohon dan wasan tsakiya na Croatia Luka Modric, mai shekara 40, zai sake kulla yarjejeniyar zama a kungiyar tsawon karin shekara daya. (DAZN via Football Italia)

    Live

    Asalin hoton, Getty Images

  3. Fabregas ya kai Como zuwa Champions League a tarihi, Champions League

    Kungiyar Como ta Cesc Fabregas ta samu tikitin shiga gasar Champions League a karon farko a tarihinta, bayan da ta doke Cremonese da ci 4-1 a ranar karshe ta kakar Serie A.

    Wannan nasara ta Como, tare da doke AC Milan 2-1 a hannun Cagliari, ya tabbatar da cewa Como ta kare a matsayi na huɗun teburi, wanda ya ba su tikitin zuwa gasar zakarun Turai. A daya bangaren kuma, wannan sakamako ya tabbatar da faduwar Cremonese zuwa Serie B.

    Tsohon ɗan wasan Arsenal da Chelsea da Barcelona, Fabregas mai shekara 39, ya bayyana cewa wannan nasara tana daga cikin manyan nasarorin rayuwarsa.

    Kafin wasan, Como na bukatar nasara tare da fatan ko AC Milan ko Roma za su rasa maki, domin ta samu tikitin Champions League.

    Roma ta doke Hellas Verona, wadda ta kare a matsayi ta uku, amma rashin nasarar Milan da Cagliari ya bai wa Como damar tsallaka Milan zuwa huɗu na farko.

    Wannan kuma ya janyo Juventus ta rasa tikitin Champions League. Juventus ta fara wasa ranar Lahadi a matsayi na shida kuma tana bukatar nasara tare da fatan wasu ƙungiyoyi su yi kuskure.

    A wasan hamayya da Torino, wanda aka jinkirta na awa ɗaya saboda dalilan tsaro bayan rikici tsakanin magoya baya, Juventus ta tashi 2-2.

    A karshe, sakamakon Roma da Como ya tabbatar da cewa Juventus za ta buga gasar Europa League a kakar wasa mai zuwa.

    Liv

    Asalin hoton, Getty Images

  4. Conte ya bar Napoli kaka ɗaya da lashe Serie A, Napoli

    Kocin Napoli, Antonio Conte, ya sanar cewa zai bar ƙungiyar a karshen wannan kakar, watanni 12 kacal bayan da ya jagorance su zuwa lashe kofin Serie A.

    Tsohon kocin Chelsea da Tottenham ya karɓi ragamar Napoli a shekarar 2024, kuma a kakarsa ta farko ya jagoranceta zuwa lashe kofin gasar Serie A, wanda shi ne na huɗu a tarihin ƙungiyar ɗin.

    Sai dai a wannan kakar, Napoli ta kare a matsayi na biyu da maki 11 tsakani da Inter Milan, wadda ta lashe kofin bana.

    A gasar Champions League – wacce Conte ya sha wahala wajen samun nasara a cikinta – Napoli ta kasa kaiwa matakin zagaye na biyu.

    Bayan da Napoli ta doke Udinese da ci 1-0 a wasan su na karshe a kakar a ranar Lahadi, Conte ya sanar da ficewarsa a wani taron manema labarai tare da shugaba, Aurelio De Laurentiis.

    Lokacin da aka tambaye shi ko zai iya zama sabon kocin tawagar ƙasar Italiya, Conte ya ce: “Shawarata ita ce a ɗauki Pep Guardiola.”

    Conte ya kusan barin Napoli a bazarar da ta gabata, amma aka shawo kansa ya ci gaba bayan tattaunawa da De Laurentiis.

    Napoli ta ƙara ɗaukar sabbin ƴan wasa kamar Kevin De Bruyne da Rasmus Højlund, amma raunin da wasu daga fitattun ƴan wasa, ya sa Conte ya kasa kare kofin da ya ɗauka.

    Liv

    Asalin hoton, Getty Images

  5. Barkanmu da shiga fagen labarin wasanni

    Jama'a barkanmu da kasancewa a cikin shirin labarin wasanni da za mu ke sanar da ku wainar da ake toyawa daga wannan ranar zuwa Asabar 18 ga watan Afirilu.

    Sunana Mohammed Abdu za ku iya tafka muhawara a BBC Hausa Facebook ko kuma ku bibiyi labaran da muke wallafawa a BBC Hausa WhatsApp.