Me ya sa Fafaroma Leo zai kai ziyara masallaci?

    • Marubuci, Nomsa Maseko (Algeria) and Paul Njie (Cameroon)
  • Lokacin karatu: Minti 5

A ranar Litinin ne Fafaroma Leo XIV ya fara balaguronsa mafi tsawo tun bayan hawa kan muƙamin, inda zai ziyarci ƙasashen Algeria da Kamaru da Angola da kuma Equatorial Guinea.

Fadar Vatican ta ce maƙasudin balaguron shi ne domin janyo hankalin duniya zuwa nahiyar Afirka.

Fiye da kashi 20% na mabiya ɗariƙar Katolika na duniya na rayuwa ne a nahiyar. Wasu majiyoyi daga fadar Vatican sun bayyana Cocin Katolika a Afirka a matsayin "mai ƙarfi".

Yawan mabiya Katolika a nahiyar na ƙaruwa cikin sauri fiye da kowane yanki na duniya, kamar yadda alƙaluman Vatican suka nuna.

An bayyana ziyarar a matsayin abin da Fafaroma Leo yake matuƙar so.

Wuri na farko da zai fara zuwa shi ne ƙasar Algeria, ƙasar da ba ta da mabiya Katolika da yawa, sai dai tana da wuri mai muhimmanci a tarihin addinin Kirista.

A Algeria ne aka haifi Saint Augustine, masanin tauhidi da falsafa, wanda ke da tasiri sosai a aƙidar Augustine.

Wannan ne karon farko da wani fafaroma zai kai ziyara a ƙasar, kuma daga cikin abubuwan da ake sa ran zai gudanar a ƙasar ta arewacin nahiyar Afirka akwai tattaunawa da mabiya addinin Musulunci da kuma tattaunawa kan batun ci-rani ta tekun Meditaraniya.

A wani ɓangare na tabbatar da ƙudurinsa na fahimtar juna tsakanin mabiya addinai daban-daban, Fafaroman zai kai ziyara a katafaren masallacin birnin Algiers.

"Wannan abin jin daɗi ne saboda zai ƙara danƙon alaƙar da ke tsakanin addinan biyu, waɗanda suke da tarihi iri ɗaya," in ji wani mazaunin birnin Algiers Marwa Melki.

Har wa yau a birnin, Fafaroman zai yi jawabi ga mabiya Katolika a majami'ar Basilica of Our Lady of Africa.

"Abin da nake dakon ji daga bakin fafaroma...mutumin da zai sake ƙarfafa mana gwiwa a kan addininmu da kuma ƙarfafa manufarmu a Afirka, shi ne gina sabuwar duniya. Duniyar da za ta zama cike da zaman lafiya, inda mutane za su rayu cikin lumana," in ji shugaban majami'ar, Father Peter Claver Cough.

Ziyarar na zuwa ne a daidai lokacin da ƙungiyoyin kare hakkin bil'adama ke nuna damuwa kan yadda ake muzguna wa tsiraru mabiya wasu addinan.

Algeria na da mabiya aƙidar Sunna da yawa. A shekarun baya kotuna a Algeria sun riƙa ɗaure mabiya addinin Kirista da Musulmai masu bin aƙidar Ahmadi, bisa zargin cewa suna yin "ibadar da ba a amince da ita ba" ko kuma sun saɓa wa Musulunci.

A wata sanarwa ta baya-bayan nan, ƙungiyar kare hakkin bil'adama ta Human Rights Watch ta ce mabiya tsirarun addinai na "fuskantar matsi ta hanyar shari'a da kuma ta ɓangaren gwamnati, abin da ke daƙile ƴancinsu na yin addini hankali kwance."

Haka nan an yi ƙorafi kan muzguna wa ƴan ci-rani da ƴan gudun hijira bayan da aka kori dubban mutane daga ƙasar a shekarar 2024 da 2025, cikin su har da mata da yara.

Silar sasanci

Ƙasa ta gaba da zai yada zango ita ce Kamaru, inda fafaroma ya ce yana sa ran isar da saƙon zaman lafiya da haɗin kai.

Ƙasar da kusan kashi 40% na al'ummarta mabiya cocin Katolika ne, ta kwashe kusan shekara 10 tana fama da rikicin ƴan awaren yankin masu amfani da turancin Ingilishi.

Majalisar Dinkin Duniya ta yi ƙiyasin cewa aƙalla mutum 6,000 aka kashe sannan sama da mutum rabin miliyan suka rasa muhallansu sanadiyyar rikicin.

Fafaroma zai kai ziyara birnin Bamenda, babban birnin arewa maso yammacin Kamaru, wanda ya kasance cibiyar rikicin.

A Bamenda, fafaroma zai gudanar da taron neman zaman lafiya da adalci a filin jirgin sama na birnin, inda za a gayyaci wakilai daga dukkan addinai.

Mazauna birnin sun ce suna sa ran taron da fafaroman zai yi zai zamo silar sasanci tsakanin al'umma.

"Wakilin ubangiji a doron ƙasa zai zo – Na san cewa kowace matsala za ta kau," in ji Ernestine Afanwi, mai shekara 45 wadda ta yi gudun hijira daga garinsu bayan an lalata gidansu da shagonsu.

A cikin shekaru uku da suka gabata, ita da ƴaƴanta shida suna zaune ne a wani sansanin ƴan gudun hijira da ke birnin Yaounde.

"Idan har na yi ido biyu da fafaroma, zan faɗa masa duk matsalolina sannan na roƙe shi ya albarkaci wannan ƙasa," in ji ta.

Rikicin na yankin Ambazonia na Kamaru bai samu kulawa daga ƙasashen duniya ba.

Sai dai magabacin Fafaroma Leo, wato marigayi Fafaroma Francis, ya riƙa nuna damuwa kan rikicin tare da buƙatar cocin ta yi addu'ar samun zaman lafiya a ƙasar ta Kamaru.

Malaman ɗariƙar Katolika na daga cikin waɗanda ake kai wa hari a yankin, inda ƴan aware suka riƙa yin garkuwa da su.

A watan Nuwamban 2025 lokacin da aka yi garkuwa da malaman kirista biyar da fasto ɗaya, Fafaroma Leo ya yi kira da a sake su ba tare da ɓata lokaci ba.

Gabanin isar Fafaroman, ana ta kiraye-kiraye ga gwamnati da kuma ƴan awaren da su nuna halin dattako domin a yi komai cikin nasara.

Farfesa Willibroad Dze-Ngwa, mashahurin masanin tarihi kuma mai sharhi kan zaman lafiya da rikice-rikice, ya buƙaci shugaban Kamaru Paul Biya ya yafe tare da sakin fursunonin siyasa, musamman waɗanda aka alaƙanta da rikicin da ake fama da shi.

''Fafaroma tambari ne na zaman lafiya da sasantawa," in ji shi.

"Saboda haka ina ganin ya kamata ziyarar da zai kawo ta zo daidai da sakin nasu, saboda hakan ya zamo abin jin daɗi ga fafaroma da shugaban ƙasa da kuma waɗanda aka kulle."

Wannan ba shi ne karon farko da Kamaru ke karɓar baƙuncin fafaroma ba.

Fafaroma John Paul II ya ziyarci ƙasar sau biyu – a shekarar 1985 da 1995 – haka ma fafaroma Benedict XVI ya ziyarci ƙasar a shekarar 2009.

Daga Kamaru, fafaroma Leo zai tafi Angola, sannan daga ƙarshe zai ziyarci Equatorial Guinea.

Angola da Equitorial Guinea duk suna da mabiya cocin Katolika masu yawa.