Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda mu'amala da mutane ke inganta kwakwalwarku da saka ku farin ciki
- Marubuci, Sarah Bell
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Global Health, BBC World Service
- Lokacin karatu: Minti 2
Shin kun san cewa shafe lokaci da wasu mutane na da alfanu ga lafiyarku kamar motsa jiki da cin abinci mai lafiya?
Yin mu'amala da mutane na da ban sha'awa, sai dai yana taimakawa wajen inganta lafiyar ƙwakwalwa, a cewar Ben Rein, likitan kula da ƙwaƙwalwa da ke Amurka.
"Idan muka yi hulɗa da wasu, sau tari muna jin daɗi. Saboda muna da abin da yake saka haka a cikin kwakwalwarmu - tsarin zamantakewa - wanda ke sa mu ji daɗi," kamar yadda ya shaida wa BBC.
Wasu sinadarai irinsu - oxytocin, dopamine, na ƙaruwa lokacin da muka yi mu'amala da mutane.
"Ya kamata mu riƙa amfani da irin waɗannan damarmaki da gaske ta hanyar mu'amala da mutane," in ji Rein, wanda ya bayyana muhimmancin mu'amala da abokai ga ƙwaƙwalwa a cikin littafinsa mai suna, ''Why Brains Need Friends: The Neuroscience of Social Connection''.
Rawar da sinadarin oxytocin ke taka wa yana da muhimmanci. An fi saninsa da sinadarin soyayya, ko kuma magani.
"Akwai kuma hujjar cewa yana rage raunuka da ake samu, zai kuma taimaka wa garkuwan jiki ƙashi wajen girma da kuma rage gajiya," in ji Rein.
Me ya sa rashin mu'amala ba shi da kyau?
Akwai tarin hujjar masana kimiyya da ke nuna yadda kaɗaici ke shafar kwakwalwa - abin da ke ƙara saka mutane cikin barazanar faɗa wa damuwa, fargaba, kashe kai, har ma da gajiyar da ba ta da kyau.
Tsananin kaɗaici - rashin mu'amala da mutane ko kuma yin kaɗan - shi ma yana iya janyo barazanar mutuwa. Wasu bincike sun ce kaɗaici na janyo kashi 32 na barzanar mutuwa.
Kaɗaici kaɗai ba zai kashe mutum ba, sai dai zai iya janyo ƙaruwar wasu abubuwa da za su jefa rayuwar mutum cikin barazana, kamar irin cutukan zuciya, ciwon suga da kuma cutar damuwa, in ji Rein.
Wannan yana sa jiki ya samu tarin gajiya, abin da zai jefa lafiyar mutum cikin barazana.
"Kasancewa cikin gajiya na tsawon lokaci ba shi da kyau ga kwakwalwa da kuma jijiyoyin jiki, sai dai suna iya janyo ƙarin abubuwa mara kyau ga jiki," a cewar Rein.
Me ya sa ba ma yawan mu'amala?
Idan mu'amala na saka mu farin ciki, me ya sa wasu mutane ba su cika yin sa ba?, in ji Rein.
Abin da yake saka haka shi ne "cire komai a rai," in ji shi, inda ya ce wasu mutane na cire abubuwan da suka taɓa haɗa su fuska da fuska da wani ɗan'adam.
Ya yi nuni da yadda ake ci gaba da ɓullo da tsare-tsare musamman a kantuna."Yanzu ba sai ka yi mu'amala da wanda za ka biya kuɗi wajensa ba - za ka ma iya sayan abin da kake so ta yanar gizo," in ji shi.
Tsananin kaɗaici da aka tilastawa mutane lokacin kullen annobar korona ta yi tasiri matuka, in ji Rein, abin da ya rage mana mu'amala da mutane, har bayan da annobar ta kare.
"Muna da buƙatar ci gaba da mu'amala kamar yadda muka saba yi a baya," in ji shi.