Arsenal da Chelsea na harin Hall, Liverpool da United na son Raum

Lokacin karatu: Minti 2

Arsenal da Chelsea ne kan gaba wajen harin ɗaukar ɗan wasan Newcastle Lewis Hall, sai dai Newcastle ɗin ba za ta bar ɗan wasan ya tafi ba. (Caught Offside)

Liverpool da Manchester United na son ɗauko ɗan wasan RB Leipzig David Raum ganin irin rawar da ya ke takawa a ziyarar neman ƴan wasan da suka yi a kakar wasanin da ake bugawa. (Teamtalk)

Mai tsaron ragar Brighton Bart Verbruggen na iya barin ƙungiyar a wannna kaka, inda mai tsaroin ragar ta Netherlands, ke duba ƙungiyoyi daban daban a don neman makoma. (Florian Plettenberg)

Chelsea na son ɗauko ɗan wasan Proto da Brazail William Gomes, don ƙara ingnata gaban ƙungiyar a kakar wasa mai zuwa. (Sport Witness)

Liverpool ta yi shirin sake miƙa sabon kwantaragi ga mai tsaron ragarta Alisson a kakar wasa mai zuwa. (Football Insider)

Tsohon ɗan wasan Liverpool da Paris Saint-Germain Georginio Wijnaldum na son komawa taka leda gasar Premier a kaka mai zuwa, yayin da kwantaraginsa da Al-Ettifag da ke Saudiya ke ƙarewa a kakar nan. (Sky Sports)

Sewansea ta sa Fam miliyan 15 a matsayin farashin da za ta siyar da ɗan wasan ta na gaba Zan Vipotnik, da ya zama ɗan wasan da ya fi kowanne zura ƙallo a raga a gasa Champoinship, inda ya ja hankalu daga Birghton. (Football Insider)

Jagorori a Newcastle na ci gaba da sa Eddie Howe a cikin tattaunawar da suke yi na shirye shiryensu na kakar wasa mai zuwa, duk da rashin tababs kan makomarsa na ci gaba da zama a ƙungiyar. (The I)

Real Madrid za ta c gaba da sauraron tayin kan ɗan wasan gaban Sapaniya Gonzalo Gracia, a kakar nan, sai dai ta ƙwallfa rai kan ɗan wasan gaban Brazil Endrick wanda ke mastayin dan wasan aro a Lyon.(The Athletic - subscription required)

Juventus za ta nemi da a siyar mata da Lios Opendaa kakar nan, bayan tayin da aka yi musu na siyen ɗan wasan da wa'adinsa na matsayin dan wasan aro a RB Leipzig zai zo ƙarshe a kakar nan . (Fabrizio Romano)