Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

KAI TSAYE, Yaƙin Iran da sauran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya

Wannan shafi na kawo muku sahihan bayanai dangane da wainar da ake toyawa a yaƙin da Amurka da Isra'ila ke yi da Iran da kuma sauran abubuwan da ke faruwa a sassan duniya

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Usman MINJIBIR da Abdullahi Bello

  1. An kashe ƴan ƙungiyar Al-Shabab guda 27

    Rahotanni daga Somalia na cewa dakarun gwamnati sun kashe mayaƙan Al‑Shabab 27, ciki har da manyan kwamandojinsu, a wani samame da suka kai a kudancin ƙasar.

    Rahoton ya ce an gudanar da samamen ne a jihar Jubaland, kuma ya samu goyon bayan hare-haren jirage marasa matuƙi daga ƙawayen ƙasa da ƙasa.

    A baya dai sojojin Amurka sun kai irin waɗannan hare-hare ta sama domin taimaka wa Somalia a yaƙin da take yi da Al‑Shabab.

    Alshabab dai ta shafe sama da shekaru 20 tana tayar da ƙayar baya, da nufin kifar da gwamnati da kuma ƙaƙaba tsauraran dokokin addini.

  2. Mutum 700 aka kashe a Sudan sakamakon hare-hare

    Babban jami’in kula da ayyukan jinƙai na Majalisar Ɗinkin Duniya, Tom Fletcher, ya ce kusan mutane 700 aka kashe, sakamakon hare-haren jiragen sama marasa matuƙa a Sudan tun daga watan Janairu da ya gabata.

    Ya ce yana cikin damuwa matuƙa kan yadda hare-haren ke ƙaruwa cikin sauri, yana mai cewa shekara 3 na yaƙin basasa sun haifar da mafi girman matsalar jin kai a duniya.

    Wakilin BBC ya ce, Massad Boulos wakilin Donald Trump a harkokin Afirka, ya nuna damuwa kan yadda ake samun ƙaruwar fararen hula da ke rasa rayukansu sakamakon hare-haren jirage marasa matuƙi.

    Ya yi kira ga sojojin Sudan da kuma dakarun rundunar RSF da su amince da tsagaita wuta.

  3. Yadda jam'iyyar ADC ke gudanar da babban taronta a Abuja

  4. Yadda ƴansandan Girka ke ɗaukar ƴan cirani aiki

    Wani bincike da BBC ta yi ya bankaɗo sheda mai yawa iri daban-daban da ke nuna yadda 'yansandan Girka, tsawon shekaru suke, daukar 'yan-ci-rani aiki, domin su rika tilasta wa sauran 'yan-ci-rani komawa ta cikin kogin kasar da ke iyaka da Turkiyya.

    Tilasta wa 'yan ci-rani , ko 'yan gudun hijira su koma abu ne da doka ta haramta a dokokin duniya.

    Shedar da aka samu daga 'yan-ci-rani da kuma kafofi na 'yansanda ta nuna cewa, hukumomin kasar ta Girka sun rika dukar 'yan Afghanistan da pakistan da 'yan wasu kasashen aikin sojan haya tun wajen shekara ta 2020 a birnin Evros, inda iyakar kasashen biyu na Girka da Turkiyya take cikin kogi.

    Gwamnatin Girka ba ta ce amsa wa BBC bukatar jin bahasinta ba.

  5. Mai kamfanin Evergrande ya amsa laifukan zamba cikin aminci

    Wata kotun China a birnin Shenzen ta ce mai katafaren kamfanin nan, da ya durƙushe, na harkokin gidaje, Evergrande, ya amsa laifukan da aka tuhume shi da su na zamba da almundahana a shari'arsa.

    A wata sanarwa da ta fitar kotun ta ce Hui Ka Yan, ya nuna nadama a kan abubuwan da ya yi.

    Kamfanin na Evergrande a baya ya taɓa kasancewa mafi girma a harkar gidaje a China, inda darajarsa a kasuwar hannun jari ta kai sama da dala miliyan dubu 50.

    Kamfanin ya durƙushe, tare da bashin biliyoyin dala, bayan ya faɗaɗa girmansa sosai.

    A wata rana nan gaba ne za a yanke wa Mista Hui Ka Yan hukunci

  6. Iran ta yi asarar dala biliyan 270 a yaƙin Amurka da Isra'ila

    Gwamnatin Iran na ta ƙoƙarin yin kiyasin asarar da ta yi sakamakon yaƙin da ta yi da Amurka da Iran domin sanya asarar a cikin buƙatunta na tattaunawa da Amurka, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Tasnin news ya rawaito.

    Da take magana ga kaffaen watsa labaran ƙasar Russia, mai magana da yawun gwamnati, Fatemeh Mohajerani ta ce ƙiyasin fari ya nuna cewa ƙasar tayi asarar da ta kai dalar Amurka biliyan 270 kuma alƙaluman za su iya sauyawa.

    Ta kuma ƙara da cewa jami'ai a Iran na ci gaba da yin ƙiyasin wanda ta ce sun haɗa da duba ga gine-ginen da aka lalata da kuma kuɗin shigar da ƙasar ta rasa sakamakon rufe masana'antu.

    Biyan diyya na ɗaya daga cikin buƙatun da ke ƙunshe a cikin daftarin yarjejeniya da Amurka a ƙarshen mako.

  7. Shekaru 12 bayan sace ƴan matan Chibok

    Yayin da ake cika shekaru 12 cif-cif da sace ƴan matan makarantar garin Chibok su 272 da ƙungiyar Boko Haram ta yi a shekarar 2014, masu fafutukar ganin an saki ƴan matan da ake kira da "BringBackOurGirls" suna neman amsa dangane da inda ragowar ƴan matan suke.

    Aƙalla ƴan mata 187 ne aka ceto ko kuma suka tsere daga hannun waɗanda suka sace su, inda har yanzu ba a san makomar ƴan matan guda 83 ba.

    Wannan ne ya sa ƙungiyar ta BringBackOurGirls ke neman sanin a halin da suke ciki.

    A watan sanarwa da ƙungiyar ta fitar ta zayyana wasu buƙatu da ta ce suna neman bayani a kansu ciki har da sanin halin da ragowar ƴan matan 83 suke ciki.

  8. Kotun tarayya ta bayar da belin Nasiru El-Rufai amma ta jiha ba ta amince ba

    Babbar kotun tarayya da ke Kaduna ta bayar da belin Malam Nasiru El-Rufai dangane da shari'ar da ke tsakaninsa da hukumar hana almundahana ta Najeriya, ICPC.

    Sai dai kuma wata babbar kotun jiha da ke Kaduna ta ɗage zaman sauraren buƙatar bayar da belin tsohon gwamnan.

    Yanzu haka dai Malam Nasiru El Rufai zai ci gaba da kasancewa a hannun hukumar ta ICPC har zuwa ranar 21 ga watan Afrilu ranar da kotun ta jiha ta sanya domin sake sauraron buƙatar belin.

    Hukumar ta ICPC dai na tuhumar tsohon gwamnan na jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai da zarge-zarge da dama da suka haɗa da:

    • Karkatar da kadarorin gwamnati ba bisa ƙa'ida.
    • Mallakar kadarorin jama'a ba bisa ƙa'ida ba.
    • Halasta kuɗaɗen haram.

    Hukumar ta ICPC ta ce an shigar da karar ne domin a bi diddigin zargin da ake yi.

    Haka kuma, ICPC ta bayyana cewa akwai wata ƙara ta daban da aka shigar a Babbar Kotun Jihar wadda ta shafi El-Rufai da wani Amadu Sule.

    A cikin wannan ƙarar, ana zargin su da amfani da muƙami ba bisa ƙa'ida ba da damfara, yunƙurin aikata damfara, da kuma fifita wasu ba bisa ka'ida ba.

    Hukumar ta ce an shigar da duka ƙararrakin biyu ne a ranar 18 ga Maris, 2026, kuma an riga an miƙa wa El-Rufai sammaci yadda ya kamata.

  9. Barazana da ƙarfin soji ba za su sa Iraniyawa su yi gizau ba - Pezeshkian

    Shugaban Iran Masoud Pezeshkian ya ce a shirye Iran take domin ci gaba da tattaunawa sannan kuma hulɗar jakadanci ita ce hanyar da ta fi kowacce wajen wanzar da zaman lafiya.

    Pezeshkian ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa ta waya da shugaban Faransa, Emmanuel Macron kamar yadda kafafen watsa labarai da dama suka rawaito.

    Rahotannin sun ce Pezeshkian ya faɗa wa Macron cewa barazana da matsin lamba da kuma ƙarfin soji ba za su warware komai ba illa ma su ƙara dagula matsalolin da Amurka ta "ƙirƙirarwa kanta".

    Shugaban na Iran ya kuma ƙara da cewa ya kamata Turai su ƙarfafa wa Amurka gwiwa wajen bin dokokin ƙasa da ƙasa

  10. Italiya ta dakatar da yarjejeniyar tsaro tsakaninta da Isra'ila

    Kafafen watsa labarai na ƙasar Italiya na rawaito cewa ƙasar ta dakatar da yarjejeniyar makamai da ke tsakaninta da Isra'ila.

    Firaiministar Italiya, Giorgia Meloni wadda ta shaida hakan kamar yadda kamfanonin dillancin labarai na cikin gidan ƙasar suka rawaito ta kuma nemi buƙatar lallai a buɗe mashigar Hormuz.

    Meloni ta ce gwamnatinta ta yanke hukuncin dakatar da sabunta yarjejeniyar wadda ake sabuntawa duk shekaru biyar, "saboda da yanayin da ake ciki.

    Italiya ce ƙasa ta uku bayan Amurka da Jamus da ke sayar wa Isra'ila makamai mafi yawa kamar yadda alƙaluman cibiyar Stockholm International Peave Research Instituion.

  11. Ƙungiyar ACF ta nemi a yi bincike kan harin kuskure a kasuwar Jilli

    A Najeriya, Ƙungiyar Tuntuɓa ta Arewacin ƙasar - Arewa Consultative Forum wato ACF, ta nemi a biya diyyar mutanen da aka kashe a harin jirgin sojin Najeriya a jihar Borno, wanda hukumomi suka ce bisa kuskure ne.

    Kungiyar ta kuma buƙaci a gaggauta gudanar da bincike domin gano gaskiyar lamarin tare da hukunta waɗanda ke da laifi.

    Sakataren watsa labarai na ƙungiyar, Farfesa Tukur Muhammad-Baba ya ce yana mamakin yadda ake samun irin waɗannan hare-hare na kuskure a garuwan yankin arewacin Najeriya amma kuma babu wani mataki da ake ɗauka.

    "An yi irin wannan a Nassarawa. An yi a Kaduna. An yi a Yobe. Amma har yanzu babu wani abun da ya fito daga binciken da ake cewa ana yi. Saboda haka muke kiran gwamnati da ta gaggauta yin bincike na gaskiya sannan a hukunta masu laifi," in ji Farfesa Tukur Muhammad-Baba.

  12. Sakamakon farko a Benin ya nuna Romuald Wadagni ne kan gaba

    Sakamakon farko-farko ya nuna cewa ministan kuɗi na Jamhuriyar Benin Romuald Wadagni , ya yi nasara da gagarumin rinjaye a zaɓen shugaban ƙasar, inda ya samu kashi 94 cikin ɗari na ƙuri'ar da aka kaɗa.

    Daman ana ganin shi zai yi nasara bayan da babbar jam'yyar hamayya ta gaza tsayar dan takararta. Kundin tsarin mulkin kasar ta Benin ya haramta wa shugaba mai-ci Patrice Talon sake neman takara.

    A don haka ya mara baya ga Mista wadagni, wanda yake da damar yin wa'adi biyu na shekara bakwai-bakwai.

    Tun da farko dan takara daya tilo da ya kalubalanci Mista Paul Hounkpè ya amsa cewa ya sha kaye bayan da ya ga yadda sakamakon ke kasancewa.

  13. China ta caccaki Amurka kan toshe tashoshin ruwan Iran

    Ma'aikatar wajen China ta yi alawadai da toshe tashoshin ruwan ƙasar Iran da Amurka ta yi inda ta bayyana al'amarin da "mai hatsari kuma rashin sanin ya kamata".

    A ranar Litinin ne dai jiragen yaƙin ruwan Amurka suka toshe tashoshin bayan da tattaunawa tsakanin Amurkar da Iran ta ci tura a Pakistan.

    Ma'aikatar harkokin wajen ta China ta bakin kakakinta, Guo Jiakun ta gargaɗin cewa rufe tashoshin ruwan zai ƙara "ta'azzara rikicin ne sannan ya yi zagon ƙasa ga tsagaita wutar da aka yi."

    Jiakun ya kuma ce rahotannin da ke nuna cewa China na shirin kai wa Iran sabbin garkuwar sararin samaniya zuwa Iran "ƙarya ce tsagwaronta".

  14. Jam'iyyar ADC na gudanar da babban taronta a Abuja

    Jam'iyyar ADC ta haɗakar masu hamayya a Najeriya ta ce ta kammala shirinta tsaf, domin gudanar da babban taronta na ƙasa a Abuja, babban birnin ƙasar.

    A ƙarshen mako ne jam'iyyar - tsagin David Mark - ta gudanar da tarukanta na jihohi, inda ta zaɓi shugabanninta na rassa jihohin.

    Tuni dai jam'iyyar ta fitar da jerin kwamitocin babban taron nata.

    Taron jam'iyyar na zuwa ne a daidai lokacin da take tsaka da rikicin shugabanci.

    Sai dai jam'iyyar ta koka kan ƙalubalen da take fuskanta game da samun wurin da za ta gudanar da taron nata, ko da yake daga baya ta ce za ta yi taron a babban ɗakin taro na Rainbow Event Center da ke Abuja.

  15. An bai wa Fulani makiyaya wa'adin tashi daga garuruwan jihar Kwara

    A jihar Kwara da ke cikin yankin kudancin Najeriya, wasu al'ummomin Fulani a yankin Lafiyaje da Patigi da Gugu sun ce suna fuskantar barazanar kora daga muhallinsu na iyaye da kakanni.

    An bai wa al'ummomin Fulanin wa'adin kwana uku da ke ƙarewa a ranar Talatar nan 14 ga watan Afirilu, 2026 da su fice su bar wuraren.

    An yi barazanar cewa idan kuma ba su tashi daga wuraren ba to duk abin da ya same su, su suka nema a cewar shugaban matasan Fulanin yankin, Abdulahi Mohammed a tattaunawar da ya yi da BBC.

    Ya ce a dalilin haka tuni suka shiga yanayi na tashin hankali ganin yadda har aka shiga ƙone muhallinsu.

  16. Me ya sa Fafaroma Leo zai kai ziyara masallaci?

    A ranar Litinin ne Fafaroma Leo XIV ya fara balaguronsa mafi tsawo tun bayan hawa kan muƙamin, inda zai ziyarci ƙasashen Algeria da Kamaru da Angola da kuma Equatorial Guinea.

    Fadar Vatican ta ce maƙasudin balaguron shi ne domin janyo hankalin duniya zuwa nahiyar Afirka.

    Fiye da kashi 20% na mabiya ɗariƙar Katolika na duniya na rayuwa ne a nahiyar. Wasu majiyoyi daga fadar Vatican sun bayyana Cocin Katolika a Afirka a matsayin "mai ƙarfi".

    Yawan mabiya Katolika a nahiyar na ƙaruwa cikin sauri fiye da kowane yanki na duniya, kamar yadda alƙaluman Vatican suka nuna.

  17. Lebanon da Isra'ila za su yi ganawar gaba da gaba a karon farko

    Ana sa ran jakadan Isra'ila da na Lebanon a Amurka su shiga tattaunawa ta gaba da gaba a Washington naN gaba.

    Wannan shi ne karon farko a cikin gomman shekaru, inda jami'ai daga kasashen biyu - wadanda ba su da alaka ta diflomasiyya, z asu yi hakan.

    Hukumomin Lebanon farko na son su ga an dakatar da bude wuta a yakin da Isra'ila ke yi da kungiyar Hezbollah, wadda Iran ke mara wa baya, to amma kuma Isra'ila ta ce ba wannan magana, dole ne sai Hezbollah, ta zubar da makamanta.

    Shi ma sakataren harkokin waje na Amurka Marco Rubio zai halarci tattaunawar. Hezbollah ta kafe lalle cewa Lebanon ta fice daga wannan sha'ani.

    A jiya Litinin shugaban kungiyar Naim Qassim, ya kara jaddada, matsayar kungiyar ta kawar da yuwuwar tattaunawa ta kai tsaye da Isra'ila

  18. Mataimakin shugaban Amurka, JD Vance ya zargi Iran da "ta'addanci na tattalin arziƙi"

    Mataimamin shugaban Amurka JD Vance ya zargi gwamnatin Iran da abin da ya kira ta'addanci na tattalin arziki saboda rufe mashigar Hormuz ta hana jiragen ruwa bi.

    Ya ce Shugaba Trump ya nuna - kamar yadda ya ce - shi ma kwallo ne - a kan wannan harka.

    A jiya Litinin Amurka ta fara aiwatar da abin da ta kira - datse jiragen ruwa ta hana su amfani da tasoshin ruwa na Iran.

    Ya zargi Irn da tsilla-tsilla a lokacin tattaunawar ta karshen mako , inda ya ce yana sa ran Iran ta bude mashigar gaba daya, ita kuma a saka mata da dakatar da bude wuta.

    Hakan dai ya biyo bayan gaza cimma matsaya a tattaunawar zaman lafiya ta Iran da Amurka a Pakistan.

    Amma kuma duk da haka mataimakin shugaban na Amurka ya sheda wa kafar yada labarai ta Amurka Fox News cewa an samu cigaba sosai a tattaunawar.

  19. Buɗewa

    Masu bibiyar shafin Hausa kai tsaye da ke kawo muku labarai da rahotannin al'amuran da ke faruwa a yaƙin da Amurka da Isra'ila ke yi da Iran da kuma sassan duniya musamman Najeriya wadda ita ce ƙasa mafi girma da yawan baƙar fata a faɗin duniya.

    Kamar kullum ma yau za mu kawo muku bayanai dangane da irin wainar da ake toyawa a waɗannan wurare.

    Da fatan za ku kasance da shafin da ma sauran shafukan sada zumunta na BBC Hausa kamar Facebook da Instagram da X da kuma Youtube.