Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Me zai faru bayan gaza cimma yarjejeniya tsakanin Amurka da Iran?
- Marubuci, Lyse Doucet
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Chief international correspondent, in Islamabad
- Lokacin karatu: Minti 5
Zaman kwana ɗaya ya yi kaɗan ya warware rikicin da aka shafe shekara 47 ana yi tsakanin Iran da Amurka.
Tarihin irin tataunawar da aka yi a birnin Isalamabad a yayin yarjejeniyar tsagaita wutar ta makonni da aka ƙulla a baya, abu ne da aka riga aka yi hasashen cewa zai ƙare ba tare da samun mafita ba.
Tattaunawar da aka shafe sa'oi ana yi ta zamo wani abu da ke tabbatar da yadda aka gaza amincewa da girman ƙalubalen da ke ƙasa masu sarƙaƙiyar gaske, kama dga batun zargin mallaka makamin nukiliya da aka daɗe ana yiwa Iran, da sabbin abubuwan da yaƙin ya ɓullo da su, musamman yadda Iran ta ƙanƙame ƙarfin iko da mashigar Hormuz, lamarin da ya ke ci gaba da girgiza tattalin arzikin duniya.
Kafin ƙulla yarjejeniy a cikin irin wannan yanayi, akwai buƙatar shawo kan matsalar rashin yarda da ta yi ƙamari a tsakani.
Kwana ɗaya baya, ba a yi zaton ɓangarorin biyu za su zauna domin tataunawa da juna, kuma a ɗaki guda ba.
Da wannan zama, an karya wani tarihi na rashin jituwar siyasa.
Babbar tambayar a nan ita ce: M ya rage a yi yanzu?
Me zai faru da yarjejeniyar tsagaita wuta ta makonni biyu, wadda ta kawo sauƙi a fargabar da duniya ta shiga bayan barazanar da shugaba Trump ya yi, ta yin balbalin bala'i kan duk wasu kayayyakin ci gaban rayuwa a Iran?
Ko shugaban Amurkan zai sake tura wakilansa domin komawa teburin tattaunawar?
Muna samun rahotanni daga Islamabad masu cewa an ci gaba da wasu matakan tattaunawar bayan mataimakin shugaban Amurka, JD Vance ya kama hana komawa gida, inda ya ayyana cewa tawagar Amurkan ta yi ''bakin ƙoƙarin ta'' kan batun.
Me Amurka za ta yi yanzu: ruruta wutar yaƙin ko sake shiga tattaunawa?
Har yanzu akwai abubua da dama da ba mu sani ba kan yadda tattaunawar ta tsawon sa'oi da ta gudana cikin sirri a birnin Islamabad.
Babu cikakken bayani kan irin jayayyar da aka yi tsakanin ɓangarorin biyu, da kuma Pakistan a matsayin mai shiga tsakani.... kama daga kiraye-kirayen waya tsakanin wakilan ɓangarorin da shugabannin su da kuma ƙwararru, kamar yadda MrVance ya sanar cewa shi ma ya yi waya da shugaba Trump fiye da sau 12 a lokacin tattaunawar.
Mataimakin shugaban ƙasan ya jaddada ''manyan muradun'' game da yaƙin, a yayin wani taron manema labarai bayan tattaunawar.
Ya ce "Muna buƙatar gani ƙarara cewa Iran da gaske take kan cewa ba zata mallaki makaman nukiliya ba, kuma ba za su sake aiwatar da duk wani shiri da zai kai ƙasar ga komawa shirin nata ba,''
A yayin tattaunawar da aka yi a watan Faburairu, kafin sake ƙaddamar da hari kan Iran, ƙasar ta gabatar da tayin da ya ƙunshi sadaukar da sinadarin ta na Uranium da yawan shi ya kai kilogiram 440 wanda ake zargin tana haɗa munanan makamai da shi.
Amma ƙasar ta tsaya kai da fata cewa tana da ƴancin mallakar sinadarin, ta kuma ƙi yarda ta sadaukar da shi. Asali ma a yanzu ana cewa ta binne shi a wani waje can ƙarƙashin ƙasa byan hare-haren da Amurka ta ƙaddamar kanta a shekarar da ta gabata.
Haka nan kuma, Ian ta ƙi buɗe mashigar Homuz domin bari a cigaba da jigilar mai da sauran kayayyaki zuwa ƙasashen duniya.
Wakilan Amurka da na Iran da suka halarci tattaunawar, sun isa birnin Islamabad ne, kowanne na iƙirarin nasara a yaƙin.
Sun shiga tattaunawar da tunanin cewa ko da ba a cimma matsaya ba, to za su koma a ci gaba da fafatawa a fagen daga, duk da nakasun da hakan ke janyowa ga tttlin arzikin duniya.
Akwai kuma abin da Dr Sanam Vakil ta Chatham House ta bayyana a matsayin ''ƙarancin basirar da za ta sanya ɓangarorin biyu masu yaƙi da juna su fahimci muradun da za su ci gaba da karewa da kuma waɗanda za su sassauta domin a fahimci juna''.
Mr Vance ya sanar da cewa abin farin cikin shi ne – "muna da ƙwararru masu shiga tsakani da yawa'' amma abin damuwar shi ne "ba mu cimma matsaya ba."
Ya kuma ce wannan a bayyane take cewa "Iran ta Amurka matsala a kan batun".
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Iran, Esmail Baghaei ya wallafa wani saƙo a shafin x, inda ya soki Amurka da nemin ''buƙatun da suka yi tsauri kuma waɗanda ba su da madogara''
Shugaban majalisar dokokin Iran wanda ke jagorantar tawagar ƙasar a tattaunawar, Mohammad Bagher Ghalibaf, ya ce Amurka ta gaza gamsar da tawagar Iran cewa da gaske suke, kuma za a iya yarda da su a yanzu.
Iran ta nuna cewa a shirye take ta ci gaba a tattauwa.
Ministan harkokin wajen Pakistan Ishaq Dar ya buƙaci dukkan ɓangarorin su ci gaba da mutumta yarjejeniyar tsagaita wutar, duk da cewa tana tangal-tangal. Ya kuma ya ce za su ci gaba da yin duk ain da ya dace domin sasanta ɓangarorin.
Idan har tarihi za a bi, za a fahimci cewa ko a 2015 da aka ƙulla yarjejeniyar makamin nukiliya tsakaninta da Amurka da kuma wasu ƙasashen turai, sai da aka shafe watanni 18 ana tattaunawa kafin cimma matsaya.
Trump ya bayyana cewa ba ya son a yaudare shi, yayin da ake cikin ataunawa. Vance kuma a nasa ɓangaren ya yi gargaɗin cewa Amurka za ta lamunta b, idan har Tehran ta yaudare su.
Do you have any views, comments or questions about this story?