Najeriya ta soki harin da Houthi ta kai wa Saudiyya

Asalin hoton, Asiwaju/Facebook
Najeriya ta yi Allah-wadau da harin da mayaƙan Houthi suka kai filin jirgin saman King Khalid da ke Riyad babban birnin Saudiyya.
Cikin wata sanarwa da ma'aikatar harkokin wajen Najeriyan ta fitar a yau, ta ce harin da ya yi sanadin mutuwar mutum 12 tare da jikkata sama da 300 abin Allah wadai ne.
Sanarwar ta ce harin tamkar "mayar da hannun agogo baya ne a yunkurin da duniya ta ke yi na samar da zaman lafiya mai ɗorewa a Gabas ta Tsakiya, wanda kuma zai ƙara ingiza zaman ɗar-ɗar din da ake yi a yankin, tare da sake jefa rayuwar fararen hula cikin haɗari, da lalata ababan more rayuwa".
Ƙasar ta yi kira da ɓangarori biyun da ke rikici da juna da su girmama dokokin ƙasa da ƙasa, domin kaiwa ga nasarar samun mafita kan rikicin.
Haka kuma gwamnatin ta mika sakon ta'aziyya ga gwamnatin Saudiyya da iyalan wadanda suka rasa rayukansu sakamakon harin, tare da yi wa wadanda suka jikkata fatan samun sauki cikin gaggawa.
Najeriya ta kuma yaba wa gwamnatin Saudiyya bisa yadda ta gaggauta daukar matakan agaji da tsaro bayan harin, tare da amincewa da kokarin da take yi na kare tsaro da jin dadin al'ummarta.
Har ila yau, Najeriya ta bayyana cikakken goyon bayanta ga duk wani mataki na sasanta rikice-rikice ta hanyar tattaunawa da fahimtar juna, maimakon amfani da karfi da ka iya kara ta’azzara matsaloli.























