Tottenham na son Pulisic, Everton za ta sake karɓar aron Grealish

Danwawasan Amurka mai shekara 27 Christian Pulisic.

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Tottenham ta tuntuɓi AC Milan kan ɗanwasan Amurka mai shekara 27 Christian Pulisic. (Teamtalk)

Liverpool da Everton na son ɗanwasan Stuttgart Jamie Leweling, mai shekara 25, yayin da ita ma Roma ke son ɗanwasan na Jamus. (Patrick Berger, external/Sky Sport Germany)

Newcastle na son cimma yarjejeniya kan ɗanwasan gaba na Lille Matias Fernandez-Pardo, mai shekara 21, amma babu wani cigaba a tattaunawa kan ɗanwasan na Belgium. (Florian Plettenberg)

Everton na koƙarin sake karɓo aron ɗanwasan Man City da Ingila Jack Grealish. (Athletic)

Crystal Palace ba ta son rabuwa da golanta Dean Henderson, mai shekara 29, bayan Nottingham Forest ta nuna tana so. (Mail - subscription required)

Newcastle United da Aston Villa da Chelsea na hamayya kan ɗanwasan Kamaru mai shekara 20 Christian Kofane daga Bayer Leverkusen. (Football Insider)

Liverpool na sa ido kan golan Genk Lucca Brughmans, mai shekara 18, amma idan har an cimma yarjejeniya ba zai tafi ba nan take. (Ben Jacobs)

Crystal Palace da Fulham na tattaunawa kan ɗanwasan tsakiya na Eintracht Frankfurt Hugo Larsson, mai shekara 22. (Teamtalk)

Crystal Palace ta farfaɗo da tattaunawa da Marseille kan ɗanwasan tsakiya na Netherlands Quinten Timber. (Mail - subscription required)

Juventus har yanzu tana nazarin ɗauko ɗanwasan gaba na Manchester United Joshua Zirkzee, mai shekara 25, amma sai idan Jonathan David ya tafi Atletico Madrid. (Sky Sport Italy)