'Sojoji 8 sun mutu bayan motarsu ta taka nakiya a Borno'

Asalin hoton, Getty Images
Wasu majiyoyin tsaro sun shaida wa AFP cewa sojojin Najeriya takwas sun mutu bayan wata motar sintirin soji ta taka nakiya da mayaƙan ƙungiyar ISWAP suka dasa a kusa da iyakar Najeriya da Kamaru.
Lamarin ya faru ne a ranar Asabar a jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya, a daidai lokacin da Babban Hafsan Sojin Ƙasa, Laftanar Janar Waidi Shaibu, ke ziyartar Maiduguri bayan wani hari da aka kai wa sansanin soji kwanaki kaɗan da suka gabata, wanda ya kashe sojoji 15 da kuma mambobin ƙungiyar sa-kai masu yaƙi da masu tayar da ƙayar baya biyar.
Ko da yake tashe-tashen hankulan ƴan jihadi da suka fara a Najeriya a shekarar 2009 sun ragu idan aka kwatanta da yadda suka yi ƙamari kusan shekara goma da ta gabata, ana ganin hare-haren sun fara ƙaruwa a cikin shekaru biyu da suka gabata.
A sabon harin, sojojin na duba ayyukan wasu mambobin ƙungiyoyin sa-kai da ke share dazuzzuka da ciyayi a gefen babban titin da ke wajen garin Gamboru, lokacin da motarsu ta taka nakin, wanda ya tarwatse tare da kashe dukkan sojojin takwas da ke cikinta.
Majiyoyin sun zargi ƙungiyar Islamic State West Africa Province (ISWAP) da kai harin, kasancewar tana da ƙarfi a yankin.
Mayaƙan jihadi kan yi amfani da dazuzzuka da ciyayi da ke gefen manyan tituna domin ɓuya su kai wa sojoji da matafiya hari ba-zata.
Wani jami'in soji a yankin ya ce harin ya faru ne a ƙauyen Kinuba, mai tazarar kilomita 25 daga Gamboru, inda ya tabbatar da cewa dukkan sojojin takwas sun mutu nan take a fashewar.
Ibrahim Liman, wanda ke cikin ƙungiyar sa-kai da ke taimakawa sojoji wajen yaƙi da 'yan ta'adda, shi ma ya tabbatar da adadin waɗanda suka mutu.
Ya ce an binne abin fashewar ne a kan titin ƙasa kuma an tayar da shi daga nesa ta hanyar wata igiyar fashewa.
Liman ya kuma ce wani ɗan ƙungiyar sa-kai da ke kula da aikin share ciyayin ya samu raunuka sakamakon gutsattsarin ƙarfen da fashewar ta watsa.



