Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
United da Arsenal na harin Costa, da wuya City ta siyar da Haaland da arha
Manchester United da Arsenal na sa ido kan dan wasan Porto Alberto Cost, sai dai sun fuskantar gagayya daga Paris St-Germain. (Caughtoffside)
Manchester City za ta sanya farashi mai yawa kan Erling Haaland, inda suka fita daga gasar Firimiya kan halin da suke ciki na karya ƙa'idodjin kashe kuɗaɗe.(Football Insider)
Chelsea, da Arsenal, da Bayern Munich, da Real Madrid da Barcelona na cikin jerin ƙungiyoyin da ke son ɗaukar Haaland kuma su sa ido sosai kan halin da Manchester City ke ciki na yiwuwar fusknatar wasu matakai da zaa dauka kanta. (Fichajes - in Spanish)
An yi wa tsohon ɗan wasan Chelsea da Manchester City Raheem Sterling na sha'awar ɗa wasu ƙungiyoyin da ke buga gasar Fransa ta Ligue 1, sai dai dukkan ƙungiyoyin basu nuna niyyar ɗaukar dan wasan, da ke zaman kansa a yanzu. (Foot Mercato - in French)
Shugaban Besiktas Serdal Adali ya ci alwashin siyo Joe Willock, daga Newcastle, a watan Janairu, yana mai shada car dan wasan tsakiyar su ya zabi komawa Turkiya. (Talksport)
Tsohon mai horar da ƴan wasan Newcastle Eddie Howe ba zai koma mataikaita ko ƙananan ƙungiyoyi da ke buga gasar Firimiya irinsu Crystal Palace ko Fulham, sai dai ya na son manyan ƙungiyoyin da ba sa taka rawar da ake tsammani ba. (Telegraph - subscription required)
Liverpool har yanzu na sa ido kan dan wasan Real Madrid Aurelien Tchouameni, duk da cewar ɗan wasan bai jima da sanya hannu kan sabon kwantaragi da ƙungiyar na tsawaita zaman sa a Madrid ɗin, a kakar nan. (Teamtalk)