Pantami ya lashe zaben fid da gwani na ɗan takarar gwamnan PDP a Gombe
Tsohon Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Zamani na Najeriya Farfesa Isa Ali Pantami, ya sake samun tikitin jam’iyyar PDP na neman kujerar gwamnan Jihar Gombe a zaɓen 2027.
Pantami ya samu nasarar ne bayan mambobin jam’iyyar sun amince da shi a zaɓen fidda gwani da aka gudanar a ranar 29 ga watan Satumban 2026.
Da yake sanar da sakamakon zaɓen, shugaban kwamitin gudanar da zaɓen Hon. Johnbull Tiemlong Shekarau, ya ce jimillar mambobin jam’iyyar 2,555 da aka tantance ne suka halarci zaɓen.
Ya ce Pantami ya samu ƙuri’u 2,054, inda ya doke sauran ’yan takara biyu.
Shekarau ya kuma sanar da cewa tsohon ɗan Majalisar Wakilai, Khamisu Ahmed Mailantarki, ya samu ƙuri’u 389, inda ya zo na biyu, yayin da Hon. Usman Aliyu Garry, wanda ya samu ƙuri’u 112, ya zo na uku.
Yayin sanar da sakamakon zaɓen, ya ce“Ni, Hon. Johnbull Tiemlong Shekarau, a matsayina na shugaban kwamitin zaɓen fidda gwani na ɗan takarar gwamnan Gombe a PDP, ina ayyana Isa Ali Pantami a matsayin wanda ya lashe wannan zaɓen fidda gwani, tare da ayyana shi a matsayin halastaccen ɗan takarar Jam’iyyar PDP a babban zaɓen 2027.”
A jawabinsa na karɓar nasarar, Pantami ya yaba wa mambobin jam’iyyar bisa yadda suka kada ƙuri’unsu cikin lumana.
Ya yi kira ga abokan takararsa, Mailantarki da Garry da su haɗa kai da shi, tare da yin aiki tare domin ganin dukkan ’yan takarar jam’iyyar sun yi nasara a zaɓen gama-gari.
Ya ce idan aka zaɓe shi, zai samar da shugabanci na gari, tare da ceto jihar daga rashin kyakkyawan shugabancin da ta shafe shekaru tana fama da shi.