"Yadda kayan gyaran fata suka ɓata mini fata"

    • Marubuci, Martha Saranga
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 6

Bayan ta yi wani gyaran fuska, kamannin Nice Aston sun sauya matuka cikin yanayi mai tayar da hankali.

"Na firgita lokacin da na tashi da safe. Kowa yana kallo na cikin mamaki domin fuskata ta kumbura kuma tana ƙaiƙayi," in ji Nice Aston, wata mazauniyar Dar es Salaam a Tanzaniya.

Nice, mai shekara 32, ta bayyana cewa ta faɗa cikin wannan tarko ne bayan ta tambayi wasu da ta sani, waɗanda fatar fuskokinsu ke da santsi da haske, irin kayayyakin da suke amfani da su.

Wannan ya sa ta fara neman kayan kwalliya a kasuwa domin kawar da kurajen fuska da ke sa ta rasa kwarin gwiwa.

Ta ce a lokacin ba ta da wata cikakkiyar fahimta game da kula da fata lokacin da ta fara neman mafita ga ƙurajen fuskarta.

Sai dai bayan ta balaga, Nice ta yi imanin cewa tabon da ke bayyana a fuskarta da bayanta da kuma ƙirjinta zai ɓace gaba daya, kamar yadda wasu mutane a kusa da ita suka dinga fada mata.

Ta bayyana cewa ba ta ga wani sauyi ba yayin da lokaci ya wuce.

Da ta samu ƴancin dogaro da kanta kuma tana samun kuɗinta, sai ta yanke shawarar neman mafita ga matsalarta.

Nice ta ce saboda shaguɓe da izgilin da ake yi mata kan yadda abi ya ɓata mata fata ya sanya ta kasance cikin baƙin ciki akai-akai.

"Na tsani kaina. Mutane kan ce mini, 'Kina da tabo masu girman koren wake.' Wasu kuma su ce, 'Kina amfani da kayan sauya launin fata, shi ya sa fatarki ke lalacewa.'"

A cewar ta, waɗannan kalamai masu zafi ne suka sa ta so ta canja kamanninta tare da gwada kayan kwalliya daban-daban, wadanda a lokacin ba su kawo wani gyara ga halin da take ciki ba.

Me ya sa ta fara amfani da kayan shafa da ake samu sayar wa a bakin titi?

A kokarinta na neman mafita ga matsalolin fatarta da kuma kamanninta, Nice ta ce an ba ta shawarar yin gyaran fuska, tare da tabbatar mata cewa hakan zai taimaka wajen magance kurajen fuskarta.

Ta bayyana cewa wata rana, bayan ta yi wannan gyaran fuskar, ta farka ta tarar cewa halin da take ciki ya kara tsananta sosai.

Fuskarta ta kumbura kamar an kona ta, tana kaikayi, kuma fatarta ta fara ɓarewa.

"Na firgita sosai. Na kira mutanen da suka yi min wannan gyaran fuskar kuma suka ce watakila ban bi umarnin yadda ya kamata ba," in ji ta.

Nice ta ce ba za ta taba manta yadda ta ji muni ba da kuma irin nadamar da ta yi saboda yin wannan gyaran fuskar.

Ta yi imanin cewa kurajen da take da su a baya sun fi sauki matuka idan aka kwatanta da kamannin ban tsoro da suka biyo baya.

Ta ce a lokacin ba ta san cewa kayayyakin da aka yi amfani da su sun kunshi sinadarai masu guba ba, wadanda suka kara lalata fatarta maimakon inganta ta.

"Fuskata da ta lalace ta sanya na rasa aiki a wata tashar talabijin."

A wani yanayi da ba kasafai ake gani ba, Nice ta ce ta je ɗaukar jarabawa domin neman aikin mai gabatar da shirye-shirye, amma aka gaya mata cewa fuskarta ta lalace sosai kuma ba za ta iya aiki a talabijin ba.

Ta bayyana cewa bayan haka ta zabi ta killace kanta a gida, ba tare da zuwa ko'ina ba, tana bata lokacinta wajen kallon fina-finai da amfani da wayarta.

"Wani lokaci ba na iya barci. Ina fama da matsanancin ciwon kai kuma na fara shan magungunan barci domin taimaka min jure halin da nake ciki, duk da cewa ba su da saukin samu," in ji ta.

Tun daga wannan lokaci, ta fara amfani da magungunan barci da ta samu a boye domin rage damuwa da fargabarta.

Ta kuma yi ikirarin cewa yawan amfani da su ya kawo matsala ga al'adarta ta wata-wata.

"A wajen saurayina kaɗai nake samun natsuwa da kwanciyar hankali."

Nice ta kasa yarda da abin da ya same ta.

Daga nan sai ta zaɓi katse alaƙa da iyalinta, saboda tsoron cewa ba za su fahimce ta ba saboda yanayin fuskarta.

"Ba zan iya magana da iyalina ba domin mahaifiyata tana da tsauri sosai. Da yadda ta raine mu, ba zan taba kuskura in gaya mata abin da na yi amfani da shi da yadda ya lalata fatata ba," in ji ta.

Ta bayyana cewa ta samu kwanciyar hankali ne kawai daga saurayinta, wanda bai daina karfafa mata gwiwa ta amince da kanta yadda take ba.

"Daga baya, na amince in ga likitan fata. Kafin ma ya rubuta min wani magani, ya fara ne da bayyana matsalata ta kurajen fuska da muhimmancin amincewa da kaina yadda nake," ta kara da cewa.

Yanzu ya fi shekara guda kenan da ta samu damar amincewa da kanta tare da daina amfani da magungunan barci ba bisa ka'ida ba.

Ta samu magani kuma ta bi tsarin jinyar da kyau kuma cikin aminci.

"Mutane sun yi mamaki lokacin da na fara warkewa kuma na amince da kaina yadda nake."

Wasu mutane sun lura da sauyin da aka samu a kamanninta kuma suka tambaye ta abin da ya faru.

"Na fara cudanya da mutane sosai, har ma na buɗe shafuka a kafofin sada zumunta domin ba da labari na, ta yadda wasu za su iya koyo daga gare shi," in ji ta.

Ta kara da cewa wasu mutane idan suka gan ta a yau suna tunanin tana sauya launin fatarta ne.

Nice ta ce ta samu mabiya da yawa a shafukanta na Instagram da TikTok.

Sai dai wasu mutanen da ba su fahimci labarinta ba suna ci gaba da sukar ta tare da zarginta da karya.

A cewar ta, har yanzu mafi yawan mutane ba su bayar da muhimmanci da ya kamata ga lafiyar fata ko kuma hadurran da ke tattare da amfani da kayan kwalliya na bogi ko wadanda ba a tsara yadda ya kamata ba.

"Yana da sauki wani ya tambaye ni irin kayan da nake amfani da su sannan ya yi amfani da su domin ya sa fatarsa ta yi haske cikin gaggawa, kawai saboda bai amince da launin fatarsa na asali ba," ta bayyana.

"Kurajen fuska sun ba ni wata dama."

Nice ta bayyana cewa matsalarta ta kurajen fuska daga karshe ta ba ta wata dama a rayuwa.

Bayan an yi mata magani, ta fara nuna karin sha'awa ga batutuwan lafiyar fata da kuma taimaka wa mutanen da ke kewaye da ita.

"Mutane da yawa suna bibiyata kuma suna tambayata game da kurajen fuska da yadda na iya shawo kan su. Wannan ya sa na fara amfani da kafafen sada zumunta wajen wayar da kan jama'a da kuma ba da shawara ga matasa da yawa, wadanda su ne suka fi yawan neman shawarata," in ji ta.

"Wani lokaci wasu masu sayar da kayan kwalliya suna kai rahoton sakonnin wayar da kai da nake yi kan kayan kwalliya na bogi domin a dakatar da shafinta na kafafen sada zumunta".

Shawara ga al'umma

Bayan duk abin da na koya ta hanyar abubuwan da na fuskanta da kaina, ina son karfafa wa iyaye gwiwa su rika bata lokaci tare da 'ya'yansu, musamman a lokacin samartaka, domin su bayyana musu sauye-sauyen da suke ciki.

Hakan zai taimaka wajen hana su kin amincewa da kansu ko kuma shiga dabi'u masu illa.

Kuruciyata da yadda aka raina ni na sanya ni cikin bakin ciki saboda iyayena sun kasance masu tsauri sosai.

Ban taba iya yin magana da su ba lokacin da fuskata ta cika da kurajen fuska kuma kowa yana yi min ba'a.

Ina fata iyayena sun saurare ni kuma sun fahimci matsalolin da nake fuskanta, amma hakan bai yiwu ba saboda tsananin tsaurinsu.

Bayani daga likitan fata

Likitan fata dan Tanzaniya Eli Minja ya bayyana cewa aikin kayan kwalliya shi ne inganta kamannin mutum, ba canza asalin yanayin fatarsa ba.

Sai dai wasu kayayyaki suna dauke da sinadarai da za su iya canza yanayin launin fata tare da haifar da illa.

A cewar kwararren, illolin da ke tattare da amfani da wasu kayan kwalliya sun danganta musamman da irin sinadaran da aka yi amfani da su, tsawon lokacin amfani da su da kuma wurin jikin da aka shafa su.

Ya kara da cewa wadannan kayayyaki na iya sa fata ta yi siriri, wanda ke kara saurin lalacewa da kaikayi.

Haka kuma suna iya haifar da miyagu, mikewar fata da kuma tsufar fata da wuri.

Likitan ya kuma nuna cewa wasu illolin na iya zama mafi tsanani, ciki har da rage kariyar halittar fata, wanda ke kara hadarin kamuwa da wasu yanayi kamar cututtukan fungal ko ma cutar sankarar fata.