Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Awara ko kaza: Wanne ne ya fi muhimmanci a jiki?
- Marubuci, Muslim Muhammad Yusuf
- Aiko rahoto daga, BBC Hausa
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 5
Idan aka haɗa mutane a wuri guda a tambaye su tsakanin awara da kaza wanne ya fi amfani ga jiki, akwai yiwuwar a samu ra'ayoyi mabambanta.
Wasu za su ce kaza ce, saboda yawan sinadaran gina da take ɗauke da shi, yayin da wasu kuma za su dage cewa awara ce, saboda yadda take da sinadarai masu amfani kuma mutum zai iya ci da kuɗi ƙalilan.
Muhawara ce da aka daɗe ana yi a wuraren cin abinci har ma da tsakanin masana harkar abinci.
Mutane da dama musamman madu ƙaramin ƙarfi sun fi karkata zuwa ga awara saboda ana kallonta a matsayin madadin nama da ita ma take ɗauke da sinadarai masu amfani. Sai dai wasu na ganin babu abin da zai maye gurbin kaza wajen samar wa jiki furotin mai inganci.
Duk da cewa duka biyun na da nasu alfanun wajen gina jiki, tambayar da ake yawan yi ita ce: idan za a zaɓi ɗaya, wanne ne ya fi amfani?
Domin samun amsar wannan tambaya da kuma warware wannan muhawara da ta daɗe tana jan hankali, mun gudanar da nazari kan binciken masana harkar abinci mai gina jiki domin sanin abin da bincike da ilimin kimiyya ke cewa kan awara da kaza.
Me ake nufi da abinci mai gina jiki?
Abinci mai gina jiki shi ne abincin da ke samar wa jiki sinadarai masu muhimmanci da yake buƙata domin girma, gyara ƙwayoyin halitta da suka lalace, samar da kuzari da kuma ƙarfafa garkuwar jiki.
Waɗannan sinadarai sun haɗa da furotin, carbohydrates, kitse masu amfani, bitamin, da ruwan jiki.
Wani bincike da masana a jami'ar Harvard suka yi ya ce ingancin abinci ba ya taƙaita kan yawan sinadaran ɗaya da yake ɗauke da shi ba ne, har ma da kariya daga haɗarin kamuwa da cututtukan zuciya idan aka kwatanta da waɗanda ba sa cin abinci mai gina jiki.
Masana sun ce jiki na buƙatar samun isasshen furotin a kullum domin gina tsoka, gyaran ƙwayoyin halitta da kuma ƙarfafa garkuwar jiki.
A cewar National Academy of Medicine, ya kamata manya su riƙa samun aƙalla gram 0.8 na furotin a kowace rana, ko da yake buƙatar kowane mutum na iya bambanta gwargwadon shekarunsa.
Me bincike ya ce game da sinadaran da ke cikin awara?
Awara na ɗaya daga cikin abincin da ake samarwa daga waken soya, kuma tana ɗauke da sinadaran gina jiki da dama. Binciken masana abinci na Jami'ar Harvard sun nuna cewa awara na da sinadarin furotin. Haka kuma, tana ɗauke da wasu sinadarai da suka haɗa da sinadarin calcium, wanda ke taimakawa wajen ƙarfafa ƙashi da haƙora.
Awara abinci ne da ake sarrafawa daga waken soya. Ana jika waken, a niƙa shi da ruwa, sannan a tace shi domin a samu ruwan waken soya. Daga nan sai a saka sinadarin da zai sa ruwan ya dunkule, kafin a matse shi ya zama awara.
Ana iya soya awara a mai, ko a dafa ta, ta wasu hanyoyi. A Najeriya, ana yawan haɗa ta da kayan ƙamshi da yaji, sannan a ci da miya ko yaji ko wasu abinci.
A cewar bayanan Harvard, awara na ɗauke da furotin mai sinadarin amino acid guda tara da jiki ba ya iya samarwa da kansa, don haka dole ne a samo su daga abinci irin waɗannan
Furotin ɗin da ke cikin awara na taimakawa wajen gina jiki da tsoka, musamman ga masu motsa jiki ko waɗanda ke buƙatar ƙarin abin mai ginda jiki a abincinsu.
Haka kuma, binciken ya cewa duk wani abinci da akaa sarrafa da waken soya tsarin cin abinci ne mai kyau ga zuciya, musamman idan aka yi amfani da shi a madadin nama. Sai dai ba a tabbatar cewa cin awara kaɗai zai hana cututtukan zuciya ba.
Sai dai kuma wani ƙarin bayanin shi ne, yadda aka sarrafa awara na da muhimmanci. Idan aka soya ta cikin mai mai yawa, hakan na iya ƙara yawan kitsen da kuzarin da mutum ke samu daga gare ta. Saboda haka, cin awara da aka soya da mai kaɗan ko aka dafa ta, ta wata hanya na iya taimakawa wajen rage maiƙon da ke jikinta.
Amfanin naman kaza ga jikin ɗan'adam
Naman kaza na ɗaya daga cikin abincin da ke samar wa jiki da sinadaran gina jiki, musamman furotin. A cewar masana kiwon lafiya na Jami'ar Harvard, naman kaza na ɗauke da ƙarancin kitsen da ba shi da amfani idan aka kwatanta da wasu nau'o'in jan nama.
Sai dai amfaninsa ga lafiya na da alaƙa da irin ɓangaren kazar da aka ci da kuma yadda aka dafa shi.
Furotin ɗin da ke cikin naman kaza na taimakawa wajen ginawa da gyaran tsokoki da sauran ƙwayoyin halittar jiki. Haka kuma, yana samar da muhimman sinadaran amino acid da jiki ke buƙata, waɗanda ke taimakawa wajen gudanar da ayyuka daban-daban a cikin jiki.
Naman kaza yana kuma ɗauke da bitamin na rukunin B, waɗanda ke taimakawa jiki wajen sarrafa abinci da samar da kuzari. Baya ga haka, nama da kaji na daga cikin hanyoyin samun sinadarin iron, wanda ke taimakawa wajen samar da haemoglobin a jini, sinadarin da ke ɗaukar iska zuwa sassan jiki.
Amfanin naman kaza ga jiki na iya raguwa idan aka sarrafa shi ta hanyar da ke ƙara masa kitse ko gishiri da yawa. Misali, soyawa cikin mai mai yawa ko idan aka sarrafa shi sosai na iya ƙara yawan kitse da gishirin da mutum ke ci.
Binciken ya ya ce naman kaza da aka gasa ko aka dafa shi ya bambanta da wanda aka sarrafa ko aka soya
Saboda haka, ana iya cin naman kaza a matsayin wani ɓangare na abinci mai gina jiki, tare da kayan lambu da sauran abinci masu amfani. Haka kuma, yana da muhimmanci a dafa shi sosai kafin a ci domin rage haɗarin kamuwa da cututtukan da ƙwayoyin cuta ke haddasawa.
Wanne ya fi amfani ga jiki?
Binciken masana abinci mai gina jiki na Jami'ar Harvard ya nuna cewa naman kaza da awara duk suna samar wa jiki da sinadarin furotin, wanda ke taimaka wa gina tsoka da gyaran ƙwayoyin halittar jiki.
Sai dai naman kaza na ɗauke da furotin mai yawa idan aka kwatanta da awara a ma'aunin iri ɗaya. Misali, gram 85 na ƙirjin kaza na iya samar da kusan gram 25 na furotin, yayin da irin wannan adadin a awara zai iya samar da kusan gram 9 zuwa 13, gwargwadon yadda aka sarrafa ta
Wannan ya sa naman kaza ya fi dacewa ga masu son samun furotin mai yawa daga abinci kaɗan.
Amma awara ma tana da muhimmanci, a cewar binciken. Ana yin ta ne daga waken soya, kuma tana samar da furotin da sinadarin calcium, gwargwadon yadda aka sarrafa ta.
Naman kaza kuma yana samar da sinadarai kamar bitamin B da iron. Sai dai amfaninsa ga lafiya ya danganta da ɓangaren naman da aka ci da yadda aka dafa shi.
Soyayyen kaza mai yawan mai ko gishiri ba zai kai irin amfanin da dafaffen kaza marar fata zai yi ba. Haka kuma, awara da aka soya cikin mai, mai yawa na iya ƙara yawan kitsen da mutum ke ci.