Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ta yaya AI zai taimaka wajen yaƙi da matsalar tsaro a Najeriya?
Gwamnatin Najeriya ta ce a shirye take ta fara amfani da fasahar ƙirƙirarriyar basira ta AI da kuma sauran sabbin fasahohin zamani wajen yaki da matsalar tsaron ƙasar.
Mataimakin shugaban ƙasar, Kashim Shettima ne ya bayyana haka lokacin da yake jawabi a madadin Shugaba Bola Tinubu a taron ranar tunawa da rundunar sojin ƙasa ta ƙasar.
Kashim Shettima ya ce gwamnati na shirin cimma hakan ta hanyar girke sabbin fasahohin a yankunan da ake fama da matsalolin tsaron domin taimaka wa yaƙi da matsalar.
Fasahar AI ta shiga kowane lungu da saƙo na harkokin yau da kullum.
Ta yaya AI zai taimaka?
Dangane da yadda fasahar AI za ta taimaka wajen magance matsalar tsaron Najeriya, BBC ta tuntuɓi Mallam Umar Saleh Gwani ƙwararren masanin fasahar AI a Najeriya, wanda kuma ya ce akwai hanyoyi da dama da fasahar AI za ta taimaka wajen yaƙi da matsalar tsaron ƙasar.
Ya kuma zayyano wasu hanyoyin da ya ce fasahar AI za ta taimaka wajen inganta yaƙi da matsalar tsaron ƙasar, kamar haka:
Hanyoyin tattara bayanan sirri
Ya ce hanya ta farko da fasahar za ta taimaka ita ce ta tattara bayanan sirri da tantance su.
''Shi dama yaƙi irin wanda sojojin Najeriya ke yi da ƴanbindiga a ƙasar na buƙatar ɗaukar mataki domin daƙile faruwar hari, tun kafin ƙaddamar da shi,'' kamar yadda ya yi ƙarin haske.
Ya ce idan ana son inganta hanyoyin tattara bayanan sirri to ana buƙatar fasahar AI, wadda ya ce tana aiki da sauri fiye da yadda ɗan'adam zai ɗauki lokaci kafin tattarawa.
''Ita fasahar AI tana amfani da hanyoyin tattarawa da sarrafa bayanan sirri cikin sauri fiye da yadda ɗan'adam zai yi'', in ji shi.
A nasa ɓangare shi ma Dokta Kabiru Adamu shugaban kamfanin Beacon Security mai nazarin ala'muran tsaro a yankin Sahel ya ce fasahar AI za ta taimaka matuƙa wajen tattara bayanai da tantance su.
''Ita wannan fasaha tana iya tsefe ɗimbin bayanai cikin ƙanƙanin lokaci, ciki har da shiga yanar gizo da sauraron hirarrakin jama'a, wanda kuma hakan zai taimaka'', in ji shi.
Bibiyar masu laifi domin gano su
Fasahar AI za ta taimaka wajen bibiyar ayyukan masu laifi da gano inda suke ta hanyar bibiyar kiran wayoyinsu.
Wasu daga cikin masu aikata laifukan nan kan kira waya domin neman kuɗin fansa bayan sun yi garkuwa da wasu.
To a nan ma Musa Saleh Gwani ya ce ta hanyar amfani da fasahar AI za a iya bibiyar kiran domin gano wurin da masu kiran suke.
Tantance bidiyo da hotuna
Masanin fahasar sadarwar ya ce fasahar AI na iya tantance hotuna ko bidiyoyin da aka ɗauka, domin gano muhimman bayanai a cikin hotunan.
''A yanzu akwai sabuwar fasahar da za iya amfani da ita domin gano wurin da aka ɗauki hoto ko naɗar bidiyo ta hanyar amfani da AI'', in ji shi.
Ya ƙara da cewa ta wannan hanya za a iya bibiyar masu aikata laifuka waɗanda ke fitar da bidiyoyi da hotuna, domin gano wuraren da suke.
Kula da kayan aikin soji
Dokta Kabiru Adamu ya ce ta hanyar amfani da AI za a iya kula da kayan aikin sojoji, kamar motocin da makaman da suke amfani da su, domin gano matsala tun kafin ta afku.
''Fasahar AI za ta taimaka wajen gano matsala a kayan aikin sojojin ƙasar tun kafin zuwan matsalar, wanda kuma hakan zai taimaka wajen raguwar lalacewar kayan aikin sojojin kamar motocinsu da jirage marasa matuƙa'', in ji shi.
Kula da iyakokin ƙasa da dazuka
Dokta Kabiru Adamu ya ce fasahar AI za ta taimaka sosai wajen kula da iyakokin Najeriya da kuma dazukan ƙasar da ke zama mafakar galibin ƴanbindigar.
''Za a iya amfani da jirage marasa matuƙa masu aiki da fasahar AI wajen sanya idanu a kan iyakoki da dazukan ƙasar domin lura da zirga-zirga da motsin ƴanbindigar da ke addabar ƙasar,'' kamar yadda ya yi ƙarin haske.
Ya ƙara da cewa dazuka na daga cikin wuraren da ke yi wa jami'an tsaro wahalar shiga, amma ta hanyar amfani da fasahar AI za a iya gano abin da ke ƙunshe cikin dajin.
Daƙile hanyar sadarwar ƴanbindiga
Masanin fasahar ya ce AI za ta taimaka wajen daƙile sadarwar masu aikata laifukan domin hana su yin waya da juna.
''Ka ga hakan zai taimaka wajen hana su samun muhimman abubuwan da suke buƙata kamar makamai da sauran kayan aikinsu'', in ji shi.
Dokta Kabiru Adamu ya ce za a iya amfani da fasahar AI wajen fahimta da fassara saƙonnin da ƴanbindiga ke fitarwa da harsunan da suke ji.
''Ita fasahar AI za a iya amfani da ita wajen fassara kowane harshe da aka magana da shi zuwa harshen da ake son a fahimci saƙon'', in ji shi.
Nau'ikan fasahar AI da ake bukata
Ƙwararren masanin fasahar ta AI ya ce abubuwan da ake buƙata domin inganta fasahar sun haɗa da na'urorin kwamfutoci na zamani, waɗanda ya ce za su taimaka wajen tattarawa da kuma sarrafa bayanan sirri.
''Su waɗannan na'urorin da su ne za yi amfani da su wajen tantance bayanan sirrin da aka tattara'', in ji shi.
Masanin fasahar ya kuma ce ana buƙatar na'urorin ɗaukar hoto domin ɗaukar hoton wuraren da ake zargin akwai mayaƙa domin tantance su.
Haka ma masanin tsaron ya ce za a iya amfani da fasahar AI a kayan da ake amfani da su wajen leƙen asiri.
'Ƙalubalen aiki da AI don magance matsalar tsaron Najeriya'
Umar Saleh Gwani ya ce amfani da sabuwar fasahar ka iya gamuwa da cikas masu yawa a ƙasar.
''Na farko shi ne rashin ƙwararrun mutane da za su iya aiki da fasahar, galibi jami'an tsaron ƙasar suna da ƙarancin ilimi kan fasahar, don haka akwai buƙatar horas da su, ko kuma yin aiki da masana'', in ji shi.
Sannan wasu shafukan sada zumunta kan goge adireshin bidiyo ko hoto.
''Alal misali shafukan Instagram da TikTok sukan goge adireshin bidiyo da zarar an ɗora shi, to yana da kyau gwamnati ta samu haɗin kan waɗanann kamfanoni domin samun damar bibiyar bidiyoyin idan an ɗora su'', in ji Umar Saleh Gwani.
Dokta Kabiru Adamu ma ya ce wani ƙalubalen da za a iya fuskanta shi ne hatsarin fallasa bayanan hukumomi, idan ba a iya taskace su yadda ya kamata ba.
Ya kuma jaddada samun kasadar amfani da fasahar a wajen yaƙi da matsalar tsaro, musamman la'akari da gasar da manyan ƙasashen duniya ke yi wajen sayar da fasahar ta AI.