Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Jana’izar Khamenei da sauran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 09/07/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku rahotanni game da jana’izar Khamenei da wasu abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 09/07/2026.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Daga Isiyaku Muhammed, Abdullahi Bello da Muslim Muhammad Yusuf

  1. Mutum 28 sun mutu a gobarar da ta tashi a masana'antar takalma a China

    Aƙalla mutum 28 ne suka mutu sakamakon gobarar da ta tashi a wata masana'antar takalma da ke birnin Jinjiang, a kudu maso gabashin China.

    Bidiyon da aka wallafa ya nuna yadda jami'an kashe gobara ke ƙoƙarin shawo kan wutar da ta kama ginin masana'antar, yayin da aka hangi wasu mutane sun maƙale a saman ginin.

    Rahotannin farko sun nuna cewa gobarar ta samo asali ne daga wani sinadarin da ake amfani da shi wajen haɗa takalma, wanda ke da saurin kamawa da wuta.

  2. An kama wani ɗan Ghana kan zargin damfarar matan Amurka $8m da sunan soyayya

    An tasa keyar wani fitaccen mai amfani da shafukan sada zumunta ɗan ƙasar Ghana zuwa Amurka domin fuskantar shari'a bisa zarginsa da aikata laifin zamba ta hanyar soyayyah ga dattawan mata yan Amurka.

    Sai dai mutumin mai suna Frederick Kumi wanda aka fi sani da Abu Trica ya musanta zarge-zargen.

    Masu shigar da ƙara sun ce Abu Trica na amfani da fashar AI wajen ƙirƙirar shafukan sada zumunta na bogi da shafukan ƙulla soyayyah na bogi, inda ya damfari waɗanda lamarin ya shafa sama da dala miliyan takwas.

    Mista Kumi na wallafa motoci da gidajen alfarma a shafinsa na Instagram, lamarin da ya fara sanya kokwanto a kan inda yake samun ƙuɗaɗe.

    Idan dai kotu ta same shi da laifi zai iya fuskantar hukuncin ɗaurin shekara 20 a gidan yari.

  3. Babu sojan Najeriya da ke karɓar ƙasa da albashin naira 100,000 - CG Musa

    Ministan Tsaron Najeriya, Christopher Musa, ya ce babu wani soja a ƙasar da ke karɓar ƙasa da naira 100,000 a matsayin albashin wata bayan sake duba tsarin albashin jami’an tsaro.

    Janar Musa ya bayyana hakan ne cikin wani ɓangare na wata hira da gidan talabijin na News Central zai saki a ranar Juma’a, 10 ga Yulin 2026.

    Ya ce an ƙara mafi ƙarancin albashin sojoji daga naira 49,000 da suke karɓa a baya zuwa naira 100,000.

    “Da can sojoji suna karɓar naira 49,000 a wata ne. Mun yi ƙoƙari sosai, yanzu suna karɓar naira 100,000,” in ji shi.

    Tsohon Shugaban Hafsoshin Tsaron ya ƙara da cewa, duk da cewa yanayin ya inganta, har yanzu rundunar sojin ƙasar ba ta samun isassun kuɗaɗen walwalar jami'ai.

  4. A shirye muke mu ci gaba da gwabza yaƙi da Iran - Isra'ila

    Ministan Tsaron Isra'ila, Israel Katz, ya ce rundunar sojin ƙasar na cikin cikakken shiri, kuma a shirye take ta ci gaba da kai hare-haren kan Iran idan buƙatar hakan ta taso.

    Kafafen yaɗa labarai na cikin gida sun ruwaito cewa Katz ya bayyana hakan ne yayin bikin yaye matuƙan jiragen yaƙin sama, inda ya ce idan ya zama dole, Isra'ila za ta iya ƙaddamar da hari na uku kan Iran.

    Kalaman nasa na zuwa ne a daidai lokacin da ake jin ƙarar fashewar wasu abubuwa a sassan Iran, a lokacin da kuma ake gudanar da jana'izar tsohon jagoran addinin ƙasar Ayatollah Ali Khamenei.

  5. Sojojin Najeriya sun ce sun daƙile harin Boko Haram a Borno

    Rundunar Sojin Najeriya ta ce dakarunta sun daƙile wani harin da mayaƙan ƙungiyar ISWAP/Boko Haram suka kai kan sansanin sojoji da ke Logomani a ƙaramar hukumar Ngala ta Jihar Borno.

    Muƙaddashin Jami'in Yaɗa Labarai na Rundunar Operation Hadin Kai, Kyaftin Muhammed Goni, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a shafin rundunar na X.

    Ya ce mayaƙan sun kai harin ne a kan sansaninsu da ke Logomani, amma sojojin sun yi artabu da maharan, sannan suka fatattake su tare da yi musu mummunar illa.

    Ya ce, wasu daga cikin maharan sun tsere da raunukan harbin bindiga.

    Sai dai ya ce soja ɗaya ya rasu a yayin musayar wutar, yayin da aka lalata wasu motoci biyu masu ɗauke da manyan bindigogi da wasu kayan aiki.

    Sanarwar ta ƙara da cewa dakarun Operation Hadin Kai na ci gaba da kai hare-hare da ayyukan ceto a Arewa maso Gabas, inda a wani samame da dakarun Bataliya ta 115 suka kai ranar 7 ga Yulin 2026 a ƙaramar hukumar Askira/Uba ta Jihar Borno, ta ceto wasu mutum biyu da aka yi garkuwa da su

    Rundunar ta ce ta kuma ƙwato naira miliyan 1.2 da ake zargin kuɗin da aka karɓa ne daga ayyukan ta'addanci ne, tare da kayan abinci da sauran kayayyakin da ake zargin ana amfani da su wajen tallafa wa ayyukan ƙungiyar.

    Sanarwar ta ce, an kai mutanen da aka ceto zuwa wani wuri mai tsaro, inda ake ba su kulawa likitoci da kuma tallafin ƙwararru kan lafiyar ƙwaƙwalwa.

  6. Ƙabarin da za a binne Ayatollah Ali Khamenei

    Kafofin yaɗa labarai na Iran sun wallafa hotunan ƙabarin da za a binne tsohon Jagoran ƙasar, Ayatollah Ali Khamenei, a cikin harabar hubbaren Imam Reza, Imam na takwas a wajen mabiya Shi'a, da ke birnin Mashhad.

    Daga cikin manyan jami'an gwamnatin Iran da suka halarci jana'izar akwai Kakakin Majalisar Dokoki, Mohammad Baqer Qalibaf, shugaban bangaren shari'a, Gholamhossein Mohseni-Ejei, da kuma Mohammad Mokhbar, wanda ya kasance mataimakin tsohon shugaban ƙasar, Ebrahim Raisi.

  7. Gawar Ayatollah Ali Khamenei ta isa wajen da za a binne shi

    Gawar tsohon Jagoran Iran, marigayi Ayatollah Ali Khamenei, ta isa hubbaren Imam Reza da ke birnin Mashhad, inda za a binne shi bayan kammala jana'izarsa.

    Hotunan da gidan talabijin na gwamnatin Iran ya wallafa sun nuna cewa babban ɗan marigayin, Mustafa Khamenei, ne ya jagoranci sallar jana'izar mahaifinsa.

    Tun da farko, kafar talabijin ta gwamnatin Iran ta sanar da cewa Ayatollah Hossein Nouri Hamedani ne zai jagoranci sallar jana'izar Khamenei a Mashhad, sai dai ba a bayyana dalilin da ya sa bai halarta ba.

    Jagorancin sallar jana'izar da Mustafa Khamenei ya yi ya sake jan hankali kan rashin ganin sabon jagoran Iran ɗin Mojtaba Khamenei, a bainar jama'a.

    Tun bayan harin da Amurka da Isra'ila suka kai kan gidan Khamenei a Tehran, wanda ya yi sanadin mutuwarsa da ta wasu daga cikin iyalansa, ba a sake ganin Mojtaba Khamenei a fili ba tun da aka naɗa shi muƙamin.

    Duk da yake yana fitar da saƙonni a rubuce amma tun daga lokacin ba a fitar da wani saƙon murya daga gare shi ba.

  8. Gwamnatin Sokoto ta bai wa sojojin Najeriya gudummuwar motocin sulke 62

    Gwamnatin Jihar Sokoto ta miƙa motocin sulke 62 da sauran kayan aikin tsaro ga hukumomin tsaro domin ƙarfafa ayyukan yaƙi da matsalar tsaro a faɗin jihar.

    Gwamnati ta ce ta kashe sama da naira biliyan 27 wajen sayen motocin, waɗanda suka haɗa da motocin ɗaukar sojoji masu sulke (APC) da babura 320 da za a rarraba wa hukumomin tsaro domin inganta zirga-zirga da kuma saurin mayar da martani ga duk wata barazanar tsaro.

    Gwamnan Jihar Sokoto, Ahmad Aliyu, ya bayyana hakan ne yayin bikin ƙaddamar da motocin a ƙarƙashin shirin jihar na Operation Fight Terrorism da aka gudanar a jihar.

    Ministan Tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa, wanda ya ƙaddamar da motocin, ya ce yana da yaƙinin cewa ƙalubalen tsaron da ƙasar ke fuskanta zai zo ƙarshe nan ba da jimawa ba.

    Ya ce gudummuwar da gwamnatin ta bayar, za su taimaka wajen ƙara ƙarfin hukumomin tsaro wajen yaƙi da ‘yan bindiga, ta’addanci, da sauran laifuka a jihar.

    Ya buƙaci 'yan Najeriya su ci gaba da bai wa jami’an tsaro goyon baya a yaƙin da suke yi da ta’addanci da ayyukan ‘yan bindiga.

    Jihar Sokoto da ke arewa maso yammacin Najeriya na cikin jihohin da ke fama da matsalar tsaro da garkuwa da mutane.

  9. EFCC ta gurfanar da Bello Bodejo kan zargin badaƙalar kuɗi

    Hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin ƙasa ta'annuti a Najeriya (EFCC), ta gurfanar da shugaban ƙungiyar Fulani ta Miyetti Allah Kautal Hore na ƙasa, Bello Bodejo bisa zargin hada-hadar kuɗi da ta wuce ƙima har dala miliyan 2.63.

    An gurfanar da shi ne a babbar kotun tarayyar Najeriya da ke Abuja ƙarƙashin mai shari'a Inyang Ekwo, bisa wasu tuhume-tuhume 12.

    EFCC na zargin Bodejo da karɓar tsabar kuɗi dala 200,000 daga Sa'idu Abubakar, tsohon Akanta Janar na Jihar Bauchi, a ranar 21 ga Janairun 2022, abin da ta ce ya zarce iyakar kuɗin da doka ta amince a yi cinikayya ta irin wannan hanya.

    Hukumar ta kuma zargi Bodejo da karɓar ƙarin dala 100,000 daga Abubakar a ranar 26 ga Oktoban 2022, da kuma wasu dala 980,000 a wasu mu'amaloli na tsabar kuɗi daban-daban.

    Sai dai kotun ta ba da umarnin a ci gaba da tsare Bodejo, kuma zai ci gaba zama a hannun EFCC har sai kotu ta yanke hukunci kan buƙatar belinsa, inda aka ɗage sauraron buƙatar belinsa har zuwa ranar 20 ga watan Yuli.

    Bayan karanta tuhumar, lauyan EFCC, Wahab Shittu, ya nemi kotun ta sanya ranar fara shari'ar tare da ci gaba da tsare wanda ake ƙarar.

    Sai dai lauyan Bodejo, Ahmed Raji, ya sanar da kotun cewa tuni sun shigar da buƙatar beli, inda ya nemi a saurari buƙatar.

    Bodejo dai ya musanta dukkan tuhume-tuhumen da ake masa.

  10. Zai ɗauki gawar Khamenei a helikwafta saboda dandanzon jama'a

    An kasa kai gawar tsohon jagoran addinin Iran, Ayatollah Ali Khamenei, zuwa wurin da za a binne shi ta mota sakamakon ɗimbin jama'ar da suka taru a kan hanyar da aka shirya wucewa.

    Saboda haka, rahotanni sun ce an yanke shawarar amfani da jirgin helikwafta domin ɗaukar gawar zuwa wajen da za a gudanar da sallar jana'iza da binne shi.

    Kafofin yaɗa labarai na Iran sun ruwaito daga birnin Mashhad cewa an sauya hanyar motar da ke ɗauke da akwatin gawar tsohon jagoran da wasu daga cikin 'yan uwansa, domin kai su zuwa hubbaren Imam na takwas na Shi'a, inda aka shirya gudanar da addu'o'i da jana'iza.

    Kamfanin dillancin labarai na IRNA ya ce, saboda yawan jama'ar da suka cika hanya, motar ta sauya hanya daga mahadar Danesh da ke Mashhad, inda ta nufi yankin Cham Ferdowsi domin daga nan a ɗauki akwatunan gawarwakin zuwa hubbaren ta hanyar helikwafta.

  11. A shirye muke mu kare kanmu daga hare-haren Amurka - Iran

    Ministan Harkokin Wajen Iran, Abbas Araqchi, ya bayyana cewa ƙasarsa a shirye take ta kare kanta idan har Amurka ta ci gaba da kai mata hare-hare.

    A wata tattaunawa ta waya da ya yi da Babban Hafsan Sojojin Pakistan, Field Marshal Asim Munir, Araqchi ya bayyana kalaman baya-bayan nan na wasu jami'an Amurka a matsayin "babbar alama da ke nuna karya yarjejeniya da kuma ci gaba da tayar da hankali."

    Ya kuma yi Allah wadai da hare-haren da Amurka ta kai kan wasu yankuna a Iran, inda ya ce hakan ya saɓa wa kundin tsarin Majalisar Ɗinkin Duniya da kuma yarjejeniyar da aka cimma a Islamabad.

    Araqchi ya gargaɗi Asim Munir kan "duk wani yunƙuri na soji daga Amurka" yayin tattaunawar da suka yi a daren Alhamis.

    Rahotanni sun ce Araqchi ya shaida wa shugaban sojojin Pakistan, wanda ya taka muhimmiyar rawa a tattaunawar sulhu, cewa Iran na da shirin kare kanta idan hare-haren Amurka suka ci gaba.

  12. Kotu ta tura tsohon shugaban kotun ɗa'ar ma'aikata Danladi Umar gidan yari

    Wata babbar kotun birnin tarayya da ke zamanta a Maitama ta bayar da umarnin tsare tsohon shugaban kotun ɗa'ar ma'aikata ta Najeriya, Danladi Umar, a gidan gyaran hali na Kuje da ke Abuja.

    Mai shari'a Peter Kekemeke ne ya bayar da umarnin tsare shi bayan hukumar EFCC ta gurfanar da shi a gabanta kan tuhume-tuhume guda huɗu na zargin amfani da muƙaminsa wajen almundahana naira miliyan 15.5.

    An zarge shi da amfani da asusun bankin matarsa a shekarar 2021 wajen karɓar kuɗi har Naira miliyan 5.5 daga wani kamfanin da aka ba aikin fentin hedikwatar CCT da ke Abuja.

    Haka kuma an zarge shi cewa a ranar 25 ga Janairu, 2024, ya sake amfani da asusun bankin matarsa wajen karɓar Naira miliyan 6 daga wani kamfani da ya gudanar da aikin sauya tsarin aikace-aikacen CCT zuwa na zamani.

    Danladi Umar ya musanta dukkan tuhume-tuhumen da ake yi masa.

    A ƙarshe Mai shari'a Peter Kekemeke ya ɗage shari'ar zuwa ranar 15 ga Yuli domin sauraron buƙatar neman beli.

    Danladi Umar ya yi fice ne a lokacin da yake shugabantar kotun ta CCT, lokacin da yake jagorantar shari'ar tsohon shugaban majalisar dattawar Najeriya Bukola Saraki.

  13. Sojojin Najeriya sun ce mayaƙan ISWAP shida sun miƙa wuya

    Sojojin Najeriya sun ce aƙalla mutum shida da ake zargin mayaƙan Boko Haram tsagin ISWAP ne sun miƙa tare da iyalansu a jihar Borno da ke arewa maso gabashin ƙasar.

    Mai magana da yawun rundunar Operation Hadin Kai Captain Mohammed Goni ne ya sanar da haka, inda ya ƙara da cewa binciken farko-farko ya nuna cewa mutanen sun fito ne daga maɓoyar mayaƙan da ke Guduf Bubayagwa da Chikide a tsaunukan Mandara duk a ƙaramar hukumar Gwoza.

    Sojojin sun kuma ce sun ƙwato kimanin dalar Amurka 1,120, wayoyin salula biyu kirar Tecno, da wasu kayayyaki daban-daban.

    Har ila yau, sojojin sun kama wani da ake zargi mai samar wa ISWAP da Boko Haram kayayyaki ne a shingen bincike na Molai a jihar, inda aka kama shi da magunguna.

    Goni ya kuma ce dakarun da ke sansanin soji na Logomani a ƙaramar hukumar Ngala sun daƙile wani hari da aka kai a daren ranar 6 zuwa 7 ga Yuli, wanda ISWAP ta ɗauki alhaki.

  14. Iran da Amurka sun kwashe dare suna kai wa juna hare-hare

    Amurka da Iran sun yi musayar wuta a dare na biyu a jere, inda ma'aikatar harkokin wajen Iran ta caccaki hare-haren Amurka kan ababen more rayuwar fararen hula.

    Ma'aikatar ta ce ƙaddamar da hare-hare a kan ababen more rayuwar fararen hula laifukan yaƙi ne da suka saɓa da dokokin duniya.

    A nata ɓangaren, Amurka ta ce ta kai hare-hare a wurare aƙalla 90 da ta bayyana da wuraren sojojin Iran.

    Iran ta ruwaito an samu fashewar bama-bamai a wurare da dama a faɗin ƙasar, sannan an dakatar da sufurin jirgin ƙasan Tehran zuwa Mashhad, inda za a binne tsohon jagoran addinin ƙasar Ali Khamenei a yau Alhamis.

    Ma'aikatar lafiyar ƙasar ta ce an kashe mutum 14 a kwana biyu da suka gabata, sannan ta ƙara da cewa ta mayar da martani a kadarorin Amurka a Kuwait da Bahrain da Qatar.

  15. Duk jami'in tsaron da ya yi jinkirin harbin ɗanbindiga za mu ɗauke su ɗaya - CG Musa

    Ministan tsaron Najeriya Janar Christopher Musa mai ritaya, ya gargaɗi jami’an tsaron Najeriya kan jinkiri wajen ɗaukar mataki kan ƴanbindiga, inda ya ce za su ɗauki jami'in tsaron da ya yi haka daidai da ɗanbindigar ko mai haɗa gwiwa da su.

    A ranar Laraba ne ministan ya yi wannan gargaɗin a lokacin rabon motocin sulke da sauran kayan aiki ga hukumomin tsaro a jihar Sakkwato, inda ya sake jaddada aniyar gwamnatin tarayya na ƙarfafa tsarin tsaron ƙasa.

    Tsohon babba hafsan tsaron ƙasar ya ƙara da cewa duk wani jami'in tsaro da aka tura bakin daga, ba y buƙatar jinkirin neman izini kafin ya ɗaukin matakin harbi idan ya ga waɗanda yake faɗa da su.

    “Ina so in sake nanatawa ga dukkan jami’an tsaron Najeriya cewa, da zarar an tura ku aiki, kada ku tsaya jiran umarni kafin ku harbin ɗanbindiga ko ɗanta’adda.

    “Duk wanda ya ƙi harbi ko kashe ɗanbindiga ko ɗanta’adda saboda yana jiran umarni, za mu ɗauke shi tamkar ɗanbindiga ne.”

    Ya ƙara da cewa an saya kayan aikin ne domin a yi amfani da su, sannan ya buƙaci ganin sakamakon gaggawa.

    Sai dai ministan ya bayyana cewa kayan yaƙi kaɗai ba za su tabbatar da zaman lafiya mai ɗorewa ba, inda ya ƙara da cewa amfani da ingantaccen bayanan sirri da haɗin kai tsakanin hukumomin tsaro su ne ginshiƙan da za su taimaka wajen kawo ƙarshen matsalar tsaro.

  16. Kashi 70 na ayyukan da muka kammala waɗanda aka yi watsi da su ne a baya - Wike

    Ministan birnin tarayya (FCT) Abuja, Nyesom Wike ya bayyana cewa kusan kashi 70 cikin 100 na ayyukan da suka kammala a ƙarƙashin jagorancin gwamnatin Bola Ahmed Tinubu, tsoffin ayyuka ne da aka yi watsi da su a gwamnatocin baya, inda ya ƙara da cewa wasu sun yi shekara 16.

    Wike ya ce sun waiwaiyo ayyukan tare da kammala su ne bisa umarnin Shugaba Tinubu, domin a cewarsa shugaban ya ce bai kamata a yi watsi da muhimman aikin gwamnati ya lalace ba.

    Da yake magana a tattaunawarsa da manema labarai a ranar Alhamis a Abuja, ministan ya ce gwamnatin ta ba da fifiko wajen kammala ayyukan da ta gada kafin fara sabbin ayyuka.

    A cewarsa, barin waɗannan ayyuka a cikin halin da aka yi watsi da su zai hana mazauna yankin cin moriyar muhimman ababen more rayuwa tare da asarar maƙudan kuɗaɗe.

    "Ina tabbatar muku cewa kusan kashi 60 cikin 100 na ayyukan da muka aiwatar cikin shekara uku da suka gabata, ayyuka ne da aka ba da kwangilarsu shekara 15 zuwa 16 da suka wuce amma aka yi watsi da su."

    Sai dai ministan ya ce a daidai lokacin da suke kammala ayyukan da suka gada, tuni hukumar FCT ta ƙaddamar da sabbin ayyukan tituna da sauran ababen more rayuwa a faɗin Abuja.

    Ya danganta nasarar da ake samu a babban birnin ƙasar da goyon bayan Shugaba Tinubu, musamman a cewarsa matakin cire hukumar FCT daga tsarin asusun bai-ɗaya wato TSA, inda ya ce hakan ya sa kuɗaɗe suka fi samuwa cikin sauƙi domin gudanar da ayyukan.

  17. Bowen: Trump ba shi da wani zaɓi da ya wuce tattaunawa da Iran

    Sabbin kalaman Donald Trump game da Iran da yiwuwar cimma yarjejeniyar sulhu ta hanyar tattaunawa ya kamata a ɗauke su da muhimmanci, domin shi ne shugaban ƙasar Amurka.

    Ga abin da ya faɗa a taron ƙasashen Nato da aka gudanar a Turkiyya:

    "Ba na son mu ci gaba da mu'amala da su. Su miyagu ne. Kun san abin da ake nufi da miyagu? Miyagu ne. Mutane ne marasa hankali. Mutane marasa hankali ne ke jagorantarsu. Kuma mutane ne masu mugunta da tashin hankali.

  18. An aikata laifukan cin zarafin bil’adama a Darfur - ICC

    Mataimakiyar mai gabatar da ƙara a Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya (ICC) ta ce kotun ta samu ‘ƙwararan hujjoji’ da suka nuna an aikata laifukan cin zarafin bil’adama a yankin Darfur yayin yaƙin basasar Sudan.

    A hirarta ta farko tun bayan da ICC ta ƙaddamar da binciken, Nazhat Shameem Khan ta ce dakarun (RSF) sun aikata munanan laifuka a biranen El-Geneina da El Fasher.

    Ta ce mun samu ƙwararan hujjoji da ke nuna alaƙa tsakanin abubuwan da ke faruwa a fili da wasu jagorori,

    Ana zargin dakarun RSF da kashe dubban fararen hula tun bayan barkewar fada tsakaninsu da sojojin kasar a shekarar 2023.

    Sai dai ƙungiyar RSF ta musanta zargin.

  19. Brazil za ta mayar da ɗan Rasha da take zargi da leƙen asiri

    Gwamnatin Brazil ta yanke shawarar mayar da wani mutum da ake zargi ɗan leƙen asirin Rasha ne zuwa gida Rasha bayan ya kammala zaman hukuncin ɗaurin shekara biyar a gidan yari.

    Rahotanni sun ce Sergey Vladimirovich Cherkasovya yi amfani da fasfo na bogi na kasar Brazil da kuma sunan ƙarya a wani yunƙuri na kutsawa cikin kotun hukunta manyan laifuka ta duniya (ICC) da ke birnin Hague na kasar Netherlands.

    Wakiliyar BBC ta ce an kama shi ne a Netherlands bayan ya isa ƙasar domin fara wani shirin samun horo a kotun ta ICC.

    Ana zarginsa da ƙoƙarin tattara bayanai kan shari'o'in laifukan yaƙi domin ya aikawa Moscow

  20. Dole mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin yaƙi da matsalar tsaro a arewa - Sarkin Musulmi

    Mai alfarma Sarkin Musulmin Najeriya Alhaji Sa’ad Abubakar II ya ce akwai buƙatar jihohin arewacin Najeriya da su haɗa ƙarfi da ƙarfe domin yaƙi da matsalolin tsaron da ke addabarsu.

    Sarkin ya bayyana haka ne a ranar Laraba a wajen taron gwamnoni da sarakunan yankin a jihar Kaduna, inda ya ambaci garkuwa da mutane da ƴanbindiga da Boko Haram a matsayin matsalolin da suka yi wa yanki dabaibayi.

    “Kowa na da rawar da zai taka wajen tabbatar da tsaro. Dole ne mu haɗa kai domin yaƙi da wannan matsalar ta tsaro musamman ta ta'addanci, garkuwa da mutane da duk wani nau'in rashin tsaro."

    A game da kafa kwamitin amintattu kan tsaron yankin a matsayin wani mataki na musamman domin nemo mafita mai ɗorewa ga matsalolin tsaro da yankin ke fuskanta.

    Ya ce kwamitin, wanda ya ƙunshi fitattun mutane daga jihohin Arewa 19, zai zo da sabbin dabaru da hanyoyin aiki wajen magance rashin tsaro.