Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Nawa ne farashin man fetur a sassan Najeriya?
Iƙirarin da kamfanin man fetur na Najeriya (NNPC) ya yi na cewa ya rage farashin litar man fetur da naira 66 a gidajen mansa ya sha bamban da abin da ake gani a zahiri.
Binciken BBC a sassa daban-daban na ƙasar ya nuna cewa farashin man fetur a gidajen NNPC ya ɗan yi ƙasa da na yadda wasu sauran ƴan kasuwa ke sayarwa, amma dai bambancin bai kai naira 66 ba.
Duk da rangwamen da gwamnati ta ce za a riƙa samu a gidajen man gwamnati, farashin gidajen man ƴan kasuwa a wasu wuraren ya fi sauƙi fiye da na NNPC.
A ranar 8 ga watan Oktoban 2026, Ministan Kuɗi da Tattalin Arziƙi, Taiwo Oyedele, ya sanar da abin da gwamnati ta kira "rangwamen farashin man fetur" a dukkan gidajen man NNPC.
Washegari, Andy Odeh, babban jami'in hulɗa da jama'a na kamfanin, ya ce rangwamen da aka yi shi ne na naira 66 kan kowace litar mai.
Odeh ya ce sun fahimci matsin da al'ummar Najeriya da marasa ƙarfi ke fuskanta, don haka ne ya sa aka yi rangwamen domin rage musu raɗaɗin mawuyacin halin da ake ciki.
Mece ce gaskiyar rangwamen farashin da gwamnati ta yi alkawari?
A cewar NNPC da masu magana da yawun gwamnatin Najeriya, rangwamen farashin man fetur ɗin zai fara ne daga ranar 1 ga Oktoban 2026, domin bikin cika shekaru 66 da samun ƴancin kai.
Sai dai har zuwa ranar Litinin ɗinnan, 12 ga watan Oktoba, binciken BBC ya nuna cewa farashin man fetur a wasu gidajen NNPC a sassa daban-daban na ƙasar bai nuna ana samun wannan rangwamen ba.
Wakilin BBC a Abuja ya duba gidajen man NNPC guda uku, ciki har da babban gidan mai na kamfanin. Gidajen biyu na sayar da litar mai kan naira 1,370, yayin da babban gidan mai da ke kusa da Cibiyar Kasuwanci ta Duniya ta Abuja (World Trade Centre) ke sayar da ita kan naira 1,405.
A halin da ake ciki, sauran gidajen man ƴan kasuwa masu zaman kansu na sayar da litar mai kan farashi tsakanin naira 1,395 da 1,430.
Wannan na nufin cewa bambancin da ke tsakanin gidajen NNPC da ke sayar da mai kan naira 1,370, da na sauran gidajen mai bai wuce tsakanin naira 25 zuwa 60 ba. Amma a gidan da ke sayar da litar kan naira 1,405, bambancin bai wuce naira 5 zuwa 25 ba, kuma farashin ya fi na wasu gidajen mai masu zaman kansu tsada.
Wani direban tasi mai suna Chukwukere Obieche, ya shaida wa BBC cewa bai ga wani sauyi a farashin mai ba tun bayan sanarwar gwamnati kan rangwamen.
"Farashin duk iri ɗaya ne, wasu wuraren ma ya fi tsada, duk da cewa wani lokaci ba mu san ko mitar da ake amfani da shi wajen zuba man yana aiki daidai ba," in ji shi.
Obieche ya ƙara da cewa bai ga yadda wannan rangwamen da ake magana a kai zai rage kuɗin sufuri ko tsadar rayuwa a ƙasar ba, kamar yadda gwamnati ta yi iƙirari.
Yadda farashin yake a Anambra, Kano da Lagos...
A birnin Onitsha na jihar Anambra, wasu mazauna yankin sun shaida wa wakilinmu cewa NNPC na sayar da litar fetur kan farashi tsakanin naira 1,350 da 1,380, yayin da wasu gidajen man ke sayar da ita kan naira 1,400.
Wannan na nuna cewa an samu rangwamen farashin naira 20 zuwa 50 ne, wanda bai kai naira 66 da NNPC ta ce ta rage ba.
Wani mazaunin yankin, Obi Francis, ya ce wannan rangwamnen ba zai iya sa mutane su fi son sayen mai a gidajen NNPC ba, domin ko mutum ya sayi lita 50, ba zai samu sauƙin da ya kai naira 2,000 ba.
Haka kuma, a jihar Kano, cibiyar kasuwanci a arewacin Najeriya, wakilinmu ya ziyarci gidajen mai uku a sassa daban-daban na birnin. Biyu na sayar da litar fetur kan naira 1,385, yayin da ɗayan ke sayar da ita kan naira 1,420.
A sauran gidajen man masu zaman kansu, farashin yana tsakanin naira 1,395 da 1,420. Wannan ma ya nuna cewa rangwamen farashin bai kai naira 66 da NNPC ta ce ta rage ba.
Dan Asabe Tamburawa, mazaunin Kano, ya ce rangwamen naira 50 bai isa ba.
Ya ce: "Mun ga cewa rangwamen naira 50 da gwamnatin tarayya ta yi a farashin fetur, gaskiya, ya yi kaɗan sosai. Ya kamata a rage farashin zuwa naira 700 domin kowa ya amfana."
Ya ƙara da cewa sanarwar rangwamen ta jawo saɓani tsakaninsa da fasinjoji, domin suna neman ya rage kuɗin sufuri saboda an ce farashin fetur ya sauka.
A jihohin Legas da Ogun kuwa, binciken wakilinmu ya nuna cewa NNPC na sayar da litar fetur kan naira 1,355, amma masu amfani da manhajar wayar kamfanin ta NNPC Retail ne kawai ke iya biyan naira 1,339.
A sauran gidajen man ƴan kasuwa masu zaman kansu, ana sayar da litar fetur kan farashi tsakanin naira 1,360 da 1,400.
CNG ko man fetur: Wanne ne ya fi sauƙaƙa wa direbobi?
A ɗaya daga cikin gidajen mai na kamfanin NNPC da ke Abuja, inda ake sayar da man fetur da kuma iskar gas ta CNG, wakilinmu ya lura da dogayen layukan motoci da ke jiran a sanya musu gas.
Ɗaya daga cikin direbobin ya ce yana iya shafe sa'o'i huɗu zuwa shida a layi kafin ya samu damar cika tankin gas ɗinsa. Sai dai ya ce duk da lokacin da yake ɓatawa, ribar
"Yanzu da na shafe lokaci mai tsawo a layi, bayan na cika gas zan koma gida in yi wanka in ci abinci, sannan in fara aiki da ƙarfe ɗaya na rana har zuwa kusan ƙarfe goma na dare. Amma zan iya samun aƙalla naira dubu 60 zuwa 70."
Ya ƙara da cewa: "Ina iya sayen gas na naira dubu 10 ko ma dubu bakwai, kuma kullum nake sayensa. Amma direban motar da ke amfani da man fetur, wanda ya fara aiki tun safe, zai iya kashe naira dubu 50 wajen sayen mai, kuma ya samu naira dubu 90 ko 100 idan ya gama aiki da ƙarfe shida ko bakwai na yamma."
Direban ya ce duk da ɓata lokacin da ake yi wajen jiran CNG, farashinsa ya fi sauƙi idan aka kwatanta da man fetur.
Ya kuma bayyana cewa da a ce ma'aikacin gwamnati ne, kuɗin gas na naira dubu 10 zai iya isar masa na tsawon kwanaki huɗu zuwa biyar.
A sanarwar da gwamnatin Najeriya ta fitar a ranar 8 ga Oktoba kan rage farashin man fetur, ta kuma yi alƙawarin sauƙaƙa wa 'yan Najeriya amfani da motocin da ke amfani da CNG, wanda ta ce farashinsa ya fi na man fetur rahusa da kashi 60 zuwa 70 cikin 100.