Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Aston Villa na nazarin Estupinan, Inter Milan na son Chalobah
Ɗan wasan AC Milan da Ecuador Pervis Estupinan, na daga cikin yan wasan da Aston Villa ke nazarta don siyo shi. (Mail)
Ana yi wa Bruno Guimaraes kallon wanda ba za a siyarwa Newcastle ba, duk da jita-jitar da ake ta yaɗawa na cewar Arsenal za su iya ɗaukar dan wasan Brazil ɗin fam miliyan 50. (Newcastle Chronicle)
Inter Milan sun haƙura da ɗauko ɗan wasan Ingila Trevoh Chalobah, sakamakon gazawarsu wajen siyen dan wasan Chelsea saboda farashin da suka sanya masa na fam miliyan 30, sai dai Como har yanzu na son ɗan wasan. (Corriere dello Sport - in Italian)
Chelsea sun shirya taya ɗan wasan Rayo Vellecano Pep Chavarria, kan fam miliyan 21. (Marca - in Spanish)
Atlentico Madrid ta yi watsi da tayin da Roma ta yi mata na fam miliyan 40 kan ɗan wasa Manu Kone. Manchester United da Liverpool sum ana son ɗaukar dan wasan ɗan ƙasar Faransar. (Corriere dello Sport - in Italian)
Aston Villa, da Leeds United, da Sunderland, da Fulham da Brighton na zawarcin ɗan wasan Sweden da Barcelona Roony Bardghji. (Sport via Sport Witness)
Hull City da Southhampton na harin ɗan wasan Werder Bremen Justin Nijnmah, 25. (Bild - in German)
Ƙwazon da dan wasan Norwary Thomas Schjelderup yayi a gasar cin kofin duniya, ya sa Benfica ƙara farshin dan wasan zuwa fam miliyan 43. Chelsea da Liverpool da Tottenham suma suna son ɗaukar ɗan wasan. (A Bola - in Portuguese)
Sporting da Wolves da Shouthampton sun fuskanci turjiya a yunƙurinsu na siyen ɗan wasan Tottenham Will Lankshear. Yana wakiltar Ingila a ajin Matasa, sannan kuma ya kasance ɗan wasan aro a kakar da ta gabata, a Oxford United . (Football.London)
Barcelona sun shirya siyar da dan wasan tsakiyar ta Ferran Torres, domin kaucewa biyan tsohuwr ƙungiyarsa Manchester City kusan fam miliyan 7, inda suka tsawita masa kwantaragi. (Athletic - subscription required)