An kai hare-hare a wurare huɗu a birnin Bushehr na Iran
Mataimakin gwamnan lardin Bushehr mai kula da harkokin tsaro ya ce an kai hare-hare a wurare huɗu da ke cikin birnin Bushehr.
Ehsan Jahanian ya ce hare-haren sun faru ne da yammacin ranar Litinin agogon ƙasar Iran.
Ya ce binciken farko da aka gudanar, sun nuna cewa babu rahoton asarar rayuka sakamakon hare-haren.
Tun da farko kuma, gidan talabijin na ƙasar Iran ya ruwaito cewa an ji ƙarar fashewa har sau biyar a yammacin birnin Bandar Abbas.
Hare-haren sun faru ne sa'o'i kaɗan bayan Rundunar Sojin Amurka ta CENTCOM ta sanar da kammala wani sabon jerin hare-haren da ta kai kan Iran.