Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Su wane ne ƴanƙasashen waje 3 da sojojin Najeriya suka zarga da aiki da ISWAP
Rundunar sojin Najeriya ta ce ta gano wasu ƴan ƙasashen waje uku cikin mayaƙan ISWAP da suke taimaka wa ƙungiyar kitsa hare-harenta a Najeriya.
Cikin wata sanarwa da Captain Mohammed Goni kakakin rundunar Operation haɗin kai mai yaƙi da Boko Haram da ISWAP a arewa maso gabashin Najeriya ya fitar, ya ce ta gano mutanen uku ne cikin kyamarar da mayaƙan ƙungiyar suka jefar bayan gumurzu da sojojin a yankin Cross Kauwa na jihar Borno.
Sojojin sun ce sun yi nasarar daƙile wani hari da mayaƙan na ISWAP suka yi niyyar kai wa wani sansanonin soji da ke Kauwa.
Bayanai sun ce mayaƙan sun kitsa kai harin ne cikin dare yayin da sojojin suka ankare tare da ɗaukar matakin daƙile harin.
Mutanen uku da ƴan ƙasasashen waje da sojoji ke zargi da aiki da ISWAP a Najeriya sun haɗa da:
Abu Ishaq
Mutum na farko da sojojin suka gano a hoto cikin tsakiyar mayaƙan na ISWAP shi ne Abu Ishaq.
Sanarwar da Captain Mohammed Goni ya fitar ya ce ɗan asalin ƙasar Falasɗinu ne da ke aiki da ƙungiyar.
Sojojin Najeriyar sun ce aikin Abu Ishaq a ISWAP shi ne bayar da horo ga mayaƙan ƙungiyar.
Abu Thaiba
Mutum na biyu da sojojin suka ce sun gano shi ne Abu Thaiba, wanda shi ma aka ganshi a cikin hoto tare da mayaƙan ƙungiyar.
Abu Thaiba ya kasance ɗan asalin ƙasara Moroco da ke arewacin Afirka.
Sojojin sun ce Abu Thaiba ya kasance likitan da ke aiki da ƙungiyar, wand ake taimakawa wajen yi wa mayaƙan ƙungiyar - suka ji raunuka - magani.
Mutum na uku
Mutum na uku ɗan ƙasar waje da ke aiki da ISWAP da sojojin suka gano cikin kyamarar sun ce babu cikakkun bayanai game da shi.
''Kawo yanzu dai muna cikin bincike domin ƙoƙarin gano cikakken sunansa da ƙasarsa da ma aikin da yake yi wa ƙungiyar'', in ji shi sanarwar.
Da ma dai an jima ana zargin hannun ƴankasashen waje a ayyukan ƙungiyoyin ISWAP da Boko Haram.
Sanarwar ta ce a lokacin fafatawa da mayaƙan ƙungiyar ɗaya daga cikin amsu ɗaukar wa ƙungiyar hotuna ne ya jefar da kyamarar wadda ta ƙunshi hotuna da bayanan yadda mayaƙan suka kitsa shirya hari kan sansanonin soji.
''A cikin kyamarar mun gano muhimman bayanan da aka naɗa na ayyukan ƙungiyar, ciki har da bidiyoyin hare-haren da suka kai d kuma abubuwansu na farfaganda'', in ji shi.
Sojojin sun ce daga cikin bayanan da suka gano, har da batun kitsa wannan hari na Kauwa, wanda suka ce wasu manyan ƙusoshin ƙungiyar huɗu suka kitsa da taimakon ƴanƙasashen wajen uku.